Sheikh Qassem: Tsaron Isra’ila zai ruguje cikin sa’a 1 idan ta shelanta yaki a kan Lebanon
Published: 6th, August 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheik Naim Qassem ya jaddada cewa, ba a samu wani abu na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba daga bangarenmu ba, amma Isra’ila ta keta wannan yarjejeniya sau dubbai.
Da yake jawabi a wajen taron cika kwanaki 40 da shahadar Birgediya Janar Mohammad Saeed Izadi (Hajji Ramadan), Sheikh Qasem ya bayyana cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana fatan ganin an kwace makaman Hizbullah, ta yadda hakan zai bata damar cin karenta babu babbaka a kan kasar Lebanon.                
      
				
Ya ci gaba da cewa, “Abin da ya faru a Siriya ya yi tasiri matuka kan matakan da Isra’ila ta dauka, wanda hakan ya sanya ta yi nadama wajen tsara yarjejeniyar.
Shugaban na Hizbullah ya jaddada cewa, Amurka ce ta tsara dukkanin bukatu da aka gabatar da nufin raunana kasar Labanon da kungiyar Hizbulah, da al’ummar Lebanon baki daya, domin hakan ne kawai zai amfanar da muradun Isra’ila a kan kasar ebanon.
Ya kuma tattauna abubuwan da wakilin Amurka Tom Barrack ya rubuta, wanda ya bayyana a matsayin “mafi muni” fiye da nau’i biyu na baya. Sheikh Naim Qassem ya yi nuni da cewa, daya daga cikin muhimman bukatun nasa shi ne kungiyar Hizbullah ta ruguza rabin kayayyakin aikinta na soji a cikin wata guda, sannan Isra’ila ta fice daga wurare masu muhimmanci guda uku kawai daga cikin biyar din da ta mamaye a kudancin Lebanon.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin Sulhu na MDD ya yi zaman gaggawa kan batun Gaza August 6, 2025 Kamaru: An haramta wa babban dan hamayya tsayawa takara a zaben Oktoba August 6, 2025 Yunkurin Netanyahu na mamaye Gaza ya tayar da balli a Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 6, 2025 Araqch: Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi Na Tabbatar Da Karfi Da Ci Gaba August 5, 2025 Wilayati: Iran Ba Za Ta Amince Da Yin Amfani Da Hanyar Zangezur Ta Hanyar Da Bata Dace Ba August 5, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Yankin Jaffa Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 5, 2025 Dr Muhammad Tahir Da Aka Yi Wa Barazanar Kisa Ya Bayyana Abin Da Ya Gani Na Masifa A Gaza August 5, 2025 An Samu Bullar Sabani Da Rikici Tsakanin ‘Yan Sahayoniyya Game Da Batun Mamaye Zirin Gaza August 5, 2025 Jiniyoyin Gargadi Sun Tashi A HKI Bayan Da Yemen Ta Cilla Sabbin Makamai August 5, 2025 Iran Ta Kafa Kwamitin Tsaron Kasa Wanda Zai Kula Da Sabbin Matsalolin Tsaro August 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Tanzaniya: An rantsar da shugaba Samia a wa’adi na biyu na shugabanci
A Tanzaniyaan rantsar da Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan a wa’adinta na biyu bayan ta lashe zaben da ya haifar da mummunar zanga-zanga a fadin kasar.
An ayyana Samia, wacce ta hau mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar magabacinta, a matsayin wacce ta lashe zaben da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi kusan 98.% na kuri’un da aka kada.
Tayi rantsuwar kama aikin ne a sansanin sojoji da ke Dodoma, babban birnin kasar.
Samia Hassan mai shekaru 65 ta fafata da ‘yan takara daga kananan jam’iyyu, yayin da manyan abokan hamayyarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu aka haramta musu tsayawa takara.
Babbar jam’iyyar adawa a kasar ta ce an kashe daruruwan mutane a zanga-zangar.
Gwamnati ta yi watsi da mace-macen, tana mai cewa “an zuzuta alkalumman.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iraniyawa na bikin tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a Tehran a 1979 November 4, 2025 ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam November 4, 2025 Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda Dalilan Tsaro November 4, 2025 Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa November 4, 2025 Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya November 4, 2025 Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar November 4, 2025 Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha November 3, 2025 An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci