Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri
Published: 5th, August 2025 GMT
Tsohon Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Adamu Maina Waziri, ya caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cewa gwamnatinsa ta kere ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta fuskar muni, wanda a yanzu ƙasar tana cikin mummunan bala’i.
Waziri, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC (African Democratic Congress), ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust TV.
“Babu ta inda gwamnatin Tinubu ba ta gaza ba. Ta gaza a dukkan fannoni, kama daga kan tsaro, tattalin arziki, yaƙi da cin hanci saboda komai ya tabarbare. Nijeriya ta koma baya sosai a ƙarƙashin mulkinsa,” in ji shi.
Duk da ya amince an tafka kura-kurai a gwamnatin Buhari, Waziri ya ce a ganinsa Tinubu ya yi wa tsohon shugaban ƙasar fintinkau ta fuskar gazawa.
Tsohon Ministan ya bayyana cewa mulkin shugaba Tinubu ya jefa ’yan Nijeriya cikin ƙuncin rayuwa, musamman tun bayan janye tallafin mai da sauye-sauyen tattalin arziki, wanda ya janyo hauhawar farashin kaya da ƙarancin abinci.
Ya kuma soki yadda wasu ’yan siyasa ke nuna goyon baya ga gwamnatin Tinubu saboda saboda son zuciya da wani ra’ayi na ƙashin kai, yana mai cewa “wadannan mutanen su kansu suna cikin tsaka mai wuya, amma sai su riƙa yabon gwamnati saboda siyasa.”
Ya ce yana mamakin irin waɗannan mutane musamman waɗanda yankunansu ke fama da hare-haren ’yan bindiga da rashin tsaro za su riƙa fitowa a kafafen watsa labarai suna goyon bayan gwamnati, lamarin da ya bayyana a matsayin mai ɗaure kai.
“Ina mamakin yadda wasu mutane waɗanda ƙananan hukumominsu ke ƙarƙashin ikon ’yan bindiga za su iya fitowa a talabijin na ƙasa su na yabon wannan gwamnati,” in ji shi.
Waziri ya ƙara da cewa, a yanzu Nijeriya na buƙatar shugabanci nagari, wanda babu makirci da ruɗu a cikinsa, saboda haka babu wata gwamnati da ta rasa ƙima irin wannan da za ta nemi wa’adi na biyu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adamu Maina Waziri Muhammadu Buhari
এছাড়াও পড়ুন:
Shugabar Ma’aikata Ta Jihar Kaduna Ta Yi Kiran Amfani Da Fasahar AI.
Shugabar ma’aikata ta jihar Kaduna, Madam Jummai Bako ta yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su yi amfani da fasahar Artificial Intelligence, A.I yadda ya kamata domin bunkasa ayyukan yi da gudanar da ayyukan.
Misis Bako ta yi wannan kiran ne a wani taron bita na yini guda da ofishin shugaban ma’aikata tare da hadin gwiwar cibiyar samar da ayyukan yi ta kasa tsakanin rukunin ma’aikata dake matakin goma zuwa goma sha uku da kuma wasu daraktoci a jihar.
Da take bude taron, shugabar ma’aikatar, Madam Jummai Bako ta bayyana cewa, Artificial Intelligence, A.I na iya taimaka wa gwamnati wajen yanke shawara mai kyau, magance matsalolin da suka dade suna tabarbarewar gwamnati da kuma cin hanci da rashawa, don haka akwai bukatar dukkan ma’aikatan gwamnati a jihar Kaduna su shiga cikinsa.
Ta bayyana cewa, muhimmancin AI a fannin hidimar jama’a ba zai iya misaltuwa ba, domin zai yi tafiya yadda ya kamata, da inganta gaskiya da kuma kara gamsar da ma’aikata ta hanyar sarrafa ayyuka, da inganta rabon albarkatun kasa da kuma samar da bayanan da suka dace.
Ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna a karkashin jagorancin Malam Uba Sani na taka muhimmiyar rawa wajen samar da manufofin da za su tallafa wa ma’aikatan gwamnati wajen bunkasa karfinsu na haduwa su yi koyi da su don gabatar da gaskiyar kimiyyar fasahar Sadarwa.
“Makullin samun bunƙasa a cikin wannan makomar AI na gaba shine daidaitawa. Muna buƙatar haɓaka al’adun rayuwa na dogon lokaci, inda ma’aikata ke ci gaba da sabunta basirarsu don kasancewa masu dacewa,” in ji ta.
A jawabin da ya gabatar, mai gudanarwa a shirin kuma shugaban cibiyar samar da ayyukan yi ta kasa, Malgwi Gideon ya jaddada bukatar ma’aikatan gwamnati su mai da hankali wajen bunkasa kansu domin bayar da gudunmawa a wuraren ayyukansu.
A nasa bangaren, Farfesa Ayuba Peter dake sashin kimiyyar lissafi na Jami’ar Jihar Kaduna wanda ya yi magana a kan batun: inganta fasahar kere-kere don inganta ayyukan jama’a a Jihar Kaduna ya bayyana cewa zai taimaka gaya wajen ganin ayyukansu sun gudana cikin sauki.
Farfesa Ayuba ya ba da shawarar cewa a kafa wata kungiya mai aiki da za ta tsara bayanin manufofin da za su jagoranci amfani da AI a cikin ma’aikata don kauce wa yin amfani da shi ba daidai ba.
A wata hira da wasu daga cikin mahalarta taron, Mista Alexander Garba dake ofishin shugabar ma’aikata da Misis Victoria Williams dake hukumar KASACA da Mista Nuhu Yakusa dake hukumar Kastlea, sun ce horon ya taimaka wajen wayar da kan su yadda za su yi aikinsu cikin sauki.
Sun ce samar da sabis da aiki shine mabuɗin kuma sun yi alkawarin yin amfani da ilimin da suka samu yadda ya kamata
Taken taron bitar shine dabaru da amfani da fasahar AI don inganta aiki da aiki.
COV. Naomi Anzaku