Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Wani Dan Siyasa Ya Shirya Addu’o’i Na Musamman Domin Samun Zaman Lafiya A Zamfara

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa.

 

Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

 

A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin tsaro da zamantakewar al’umma da ke addabar Zamfara da sauran sassan kasar nan.

 

Ya kara da cewa, idan aka ajiye siyasa a gefe, kowane dan majalisa daga jihar Zamfara yana yin kokari na gaske don ganin an magance rikicin.

 

Manyan Malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na jihar ne suka jagoranci addu’o’i na musamman, da karatuttukan Alkur’ani mai girma, tare da gabatar da addu’o’in neman zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban Zamfara da Najeriya baki daya.

 

Sun kuma yi addu’ar Allah ya baiwa shugabanni a dukkan matakai da hikima da jagoranci.

 

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Tudun Wada, wanda ya jagoranci zaman addu’ar, ya bayyana muhimmancin Ikhlasi, Adalci, da kokarin hadin gwiwa wajen ganin an samu dawwamammen zaman lafiya.

 

Sauran sun bukaci al’umma da su rungumi afuwa, hakuri, da hadin kai, tare da jaddada cewa zaman lafiya da tsaro yana farawa ne daga jama’a da kansu.

 

Mahalarta taron sun nuna jin dadinsu ga Alhaji Kabiru Amadu bisa kaddamar da taron addu’ar, inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya dace kuma a yaba masa.

 

Shima da yake jawabi a wajen taron, mai martaba Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad ya yi kira ga sauran ‘yan majalisar tarayya da su yi koyi da irin wannan kokari da Mai Palace ya yi, yana mai cewa sa hannun Allah shi ne ginshikin magance matsalar tsaro a jihar.

 

An kammala taron addu’o’in ne da yin kira ga al’umma baki daya da su bayar da gudunmawarsu wajen ganin an dawo da zaman lafiya da zaman lafiya da adalci a jihar Zamfara da Najeriya baki daya.

 

 

AMINU DALHATU

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ruftawar Gini Ya Kashe Uwa Da ‘Ya’yanta Biyar A Katsina
  • Xizang Ya Cimma Nasarorin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Suka Kafa Tarihi Cikin Shekaru Fiye Da 60
  • Sashen Lafiya Zai Fara Amfani Da Sabuwar Fasahar AI Don Inganta Lafiya
  • Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15
  • Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa ya Samu Gagarumar Nasara a Karamar Hukumar Gwarzo
  • Gwamna Yusuf Ya Kaddamar da Shirin Dashe Itatuwa Don Yaki da Matsalolin Muhalli
  • Wani Dan Siyasa Ya Shirya Addu’o’i Na Musamman Domin Samun Zaman Lafiya A Zamfara
  • Gwamnan Kano Ya Kaddamar da Shirin Dashen Bishiyoyi
  • Son Zai Bar Tottenham Zuwa Amurka Bayan Shafe Shekaru 10 A Ingila