An kama masu garkuwa da mutane 3 da kuɓutar da wasu
Published: 3rd, May 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sashen tawagarta masu tattara bayanan sirri (IRT), ta kuɓutar da wasu ’yan ƙasar Ghana biyu da aka yi garkuwa da su tare da damƙe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke aiki a kan iyakokin ƙasashen duniya.
Rundunar ’yan sandan a ranar Juma’ar ta ce hakan ya biyo bayan rahoton da aka shigar gaban babban ofishin hukumar a Abuja a ranar 27 ga Afrilu, 2025, game da yin garkuwa da wani Anastasia Arthur da aka fi sani da Baidoo, ɗan ƙasar Ghana mai shekara 48.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar, ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa sace Baidoo ya samo asali ne daga wata zamba ta soyayya ta Facebook.
Adejobi ya ce ci gaba da bincike na fasaha ya nuna wani muhimmin wuri da ke da alaƙa da waɗanda suka aikata laifin, kuma an tura jami’ai domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Ya ce, tare da haɗin gwiwa da hukumar ’yan sandan Ghana, jami’an IRT sun gano wata ƙungiyar masu aikata laifuka da masu garkuwan da ke aiki a ƙasashen Ghana da Najeriya.
Ya ce, “Babban nasarar da aka samu a binciken sun haɗa da kama wani Emeka Christian, ɗan Najeriya mai shekara 27 da ke zaune a Bolgatanga, Upper Eastern Ghana, wanda ya amsa laifin karɓar kuɗi cedis GH10,000 a matsayin kuɗin fansa ga wanda aka yi garkuwa da shi ta hanyar asusun wayarsa na Ghana.
“Ya kuma amince da tura Naira kwatankwacin kuɗin zuwa wani asusun bankin Najeriya mallakar wani Peter Okoye.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Masu Garkuwa da mutane
এছাড়াও পড়ুন:
Za a dawo da dukkan Alhazai gida ranar 28 ga Yuni – NAHCON
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar da aniyarta na dawo da dukkan Alhazan Najeriya da ke Saudiyya zuwa ranar 28 ga watan Yunin, 2025.
Rahotanni daga Hukumar NAHCON da ke birnin Makkah na cewa, alhazan Najeriya 6,528 ne suka dawo Najeriya, yayin da Kamfanin Max Air ya kammala jigilar Alhazai jirgi na 16 a ranar Talata.
Kotu ta ba da belin Natasha kan N50m kan zargin bata sunan Akpabio Ba Atiku kaɗai ba ne matsalar PDP — Gwamna LawalWata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan yaɗa labarai Fatima Sanda Usara ta fitar ta ce NAHCON tare da hukumar jin daɗin alhazai ta jiha, da kuma masu jigilar jiragen sama na shekarar 2025 suna yin duk abin da za su iya don ƙara saurin jigilar.
“Hukumar ta shirya dawo da dukkan alhazan nan da ranar 28 ga watan Yuni 2025 kuma ta ci gaba da zage damtse don jigilar.
“A cikin wannan lokaci, dukkan ƙasashen suna ƙoƙarin dawo da alhazansu a lokaci guda, kuma hakan ya haifar da tsananin buƙatar filayen jiragen sama.
“Waɗannan gurbi na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (GACA) da ke Saudi Arabiya ne ke kula da su, kuma a halin yanzu, ba a ware wa Nijeriya gurabe masu yawa kamar yadda ake buƙata domin tafiyar da alhazai masu yawa cikin gaggawa.
“Saboda haka, manyan masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama guda uku sun tsara dabarun ƙara yawan wuraren da za a samu a ƙasar.
“Ana fatan tattaunawa mai ƙarfi da mahukuntan Saudiyya za ta taimaka wajen ƙara yawan filayen jiragen.