Jagoran Juyin Musulunci Ya Bayar Da Tallafin Kudi Domin Sakin Fursunoni
Published: 5th, March 2025 GMT
Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayar da tallafin kudin da sun kai Riyal biliyan 40 ga kungiyoyin agaji da suke aiki domin ganin an saki frusunonin da su ka aikata laifuka ba cikin ganganci ba.
A kowace shekara a cikin watan Ramadan mai alfarma kungiyoyin na agaji suna kaddamar da neman taimako saboda sakin fursunonin da su ka aikata laifuka ba a cikin ganganci ba.
Ana amfani da kudaden ne wajen biyar fansa da diyya ga wadanda fursunonin su ka yi wa illa. Biyan fansa din dai ana yinsa ne maimakon zartar da hukunci na Kisasi.
Watan azumin Ramadana da shi ne na 9 a cikin kalandar musulunci yana da matsayin na musamman da ake son aikata alheri fiye da kowane lokaci a cikinsa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri
Ruwan sama mai ƙarfi da ya sauka da safiyar ranar Laraba a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, ya haddasa ambaliya.
Ruwan wanda ya fara sauka tun da misalin ƙarfe 5 na Asuba, ya cika tituna da gidaje musamman a unguwannin Dala, Bulunkutu, titin Damboa, filin Polo, da Federal Low Cost.
Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasuAmbaliyar ta haifar da cikas a rayuwar jama’a, inda ruwa ya lalata dukiyoyi mutane masu tarin yawa.
Mutane da dama dun fice daga gidajensu domin neman mafaka, musamman waɗanda gidajensu ruwa ya mamaye.
Hakazalika, wasu tituna sun shafe sakamakon mamakon ruwan, lamarin da ya hana mutane fita ko komawa gidajensu da kuma yin ayyukansu na yau da kullum.
Wasu daga cikin mazauna garin sun ce ambaliyar ta tsananta ne saboda magudanan ruwa sun cika da shara irin su robobi, datti da tarkacen kayan gini.
Hakan ya hana ruwa tafiya yadda ya kamata.
Wani da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce mafi yawan magudanan ruwan Maiduguri ba sa aiki yadda ya kamata saboda sun toshe da shara.
Ya ƙara da cewa rashin kula da tsaftar muhalli ne ya haddasa irin wannan matsala.
A halin yanzu, akwai buƙatar gwamnati ta ƙara sanya ido, ta tsaurara dokokin muhalli, da kuma wayar da kan jama’a kan muhimmancin tsaftar gari.
Har ila yau, akwai buƙatar a gyara magudanan ruwa domin gujewa irin wannan ambaliya a nan gaba.
Masana sun gargaɗi jama’a cewa ana sa ran samum mamakon ruwan sama a makonni masu zuwa.
Amma an buƙaci jama’a su ɗauki matakan kariya da kuma haɗa kai da hukumomi domin shawo kan lamarin.