Aminiya:
2025-09-18@00:43:34 GMT

Fasinjoji 16 sun ƙone ƙurmus a Ogun

Published: 5th, March 2025 GMT

Aƙalla fasinjoji 16 suka ƙone ƙurmus, yayin da wasu uku suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku ranar Talata a Jihar Ogun.

Aminiya ta ruwaito cewa hadarin wanda ya rutsa da mota ɗaya kacal ya afku ne a gidan Buhari da ke kan titin Abeokuta zuwa Shagamu.

DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana ‘A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice’

An bayyana cewa, hatsarin dai ya rutsa da wata farar motar bas kirar Mazda mai lamba KJA 949 YJ, da misalin ƙarfe 1:00 na rana.

Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar.

Ta ce ba za a iya tantance jinsin waɗanda abin ya shafa ba saboda “sun ƙone ƙurmus ta yadda ba a iya fahimtar halittar jikinsu ba.”

Okpe ta ɗora alhakin faruwar hatsarin a kan gobarar da ta tashi a cikin motar, tana mai cewa bas ɗin tana ɗauke da fasinjoji 21 da kuma wata tukunyar gas wadda ta yi bindiga a cikin motar.

“Hatsarin ya rutsa ne da mutane 21. Ba a iya tantance waɗanda abin ya shafa ba saboda sun ƙone ba a iya gane su ba.

“Mutane 16 ne suka mutu a hatsarin, yayin da uku suka samu raunuka daban-daban, sai kuma wasu biyu suka tsallake rijiya da baya.

“Abinda ake zargin ya haddasa hadarin shi ne gobarar da ta tashi a cikin motar, wadda kuma tana ɗauke da wata tukunyar gas, wanda ya kai ga fashewar,” in ji ta.

Okpe ta ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Idi Aba a birnin Abeokuta.

Kwamandan Hukumar FRSC na yankin, Akinwumi Fasakin, yayin da yake jajantawa iyalan mamatan, ya yi gargaɗin cewa, ya kamata a riƙa safarar kayan da ka iya jawo tashin wuta cikin kulawa da kuma motocin da aka keɓe waɗanda ƙwararru direbobi ke tuƙawa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hatsari Jihar Ogun

এছাড়াও পড়ুন:

Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo

An garzaya da ita asibiti, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

’Yansanda sun kama Bosede kuma suna bincike a kan lamarin.

Kakakin rundunar, DSP Olusola Ayanlade, ya ce za su tabbatar da adalci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara