Har Kullum Jama’ar Kasar Sin Suna Adawa Da Nuna Fin Karfi
Published: 5th, March 2025 GMT
A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda a yayin taron, wani dan jarida ya gabatar da tambaya game da matakin Amurka, na sake kakabawa Sin karin harajin kashi 10 cikin dari, bisa fakewa da batun sinadarin kashe radadi na Fentanyl.
Ya ce, har kullum jama’ar kasar Sin suna adawa da nuna fin karfi, da yin matsin lamba, da tilastawa, da kuma barazana, saboda hakan ba hanya ce da ta dace a bi yayin mu’ammala da kasar Sin ba.
Ya kara da cewa, idan bangaren Amurka yana son warware batun Fentanly, ya kamata ya tattauna tare da bangaren Sin bisa daidaito, da mutunta juna, da samun moriyar juna, har a kai ga warware matsalolin dake tsakani. To amma idan har Amurka na da wasu manufofi, kuma ta nace a kan kaddamar da yakin haraji, da yakin kasuwanci ko wani yaki na daban, kasar Sin za ta tunkari yakin har zuwa karshe.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin.
Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar neman ’yancin kan Taiwan, matakin da ya yi hannun riga da ra’ayoyin al’ummun Taiwan, kuma zai fuskanci turjiya daga akasarin al’ummun yankin na Taiwan. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp