Falasdinawa 40 Ne suka Yi Shahada A Zirin Gaza Sakamakon Ta’addancin Sojojin Mamayar Isra’ila A Jiya Juma’a
Published: 3rd, May 2025 GMT
Falasdinawa 40 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Juma’a
Rahotonni sun bayyana cewa: A yammacin jiya Juma’a, Falasdinawa fararen hula 8 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon wani hare-haren da jiragen saman sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin Jabaliya da al-Balad da ke arewacin zirin Gaza.
Haka zalika hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 6 sannan wasu 8 suka jikkata a wani harin da jiragen saman yakin mamayar Isra’ila suka kai kan taron fararen hula da ke kusa da mahadar Abd al-Aal da ke kan titin al-Jala’a da ke arewacin birnin Gaza.
A cewar majiyoyin cikin gida, jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai hari kan wani asibiti da ke titin al-Jala’a, inda suka janyo shahadan Mahmoud Abdullah al-Muqayyad, Ahmed Qaza’ar, Tamer Hamdan, Samer al-Nuwairi, Hatem al-Sa’ati, da Rizq al-Madhoun.
A kudancin zirin Gaza kuwa, Falasdinawa uku ne suka yi shahada, kuma wasu suka jikkata, lokacin da wani jirgin saman yakin mamayar Isra’ila ya kai hari kan wata tanti da ke dauke da ‘yan gudun hijira a yankin Mawasi na Khan Yunis.
Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza a rana ta 46 a jere, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, da jikkatan wasu na daban
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya , da kuma halin da yankin ke ciki da yi yuwar sake komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka.
Wannan bayani yazo ne adaidai lokacin da lamura ke kara zafi a yankin bayan yakin da aka yi tsakanin iran da kuma Israila, don haka bayanan na Araqchi wata sanarwa ce dake nuna shirin iran na mayar da martani amma kuma tabar kofar tattaunawar diplomasiya a bude.
Har ila yau ministan ya bayyana cewa iran a shirye take ta tunkari duk wani kalu-bale, kuma za ta mayar da martani mai karfi game da duk wani wuce gona da irin Isra’ila, don mun shirye fiye da kowanne lokaci a baya, kuma yayi gargadin cewa isra’ila za ta sake shan wani kayen idan ta kara shelanta yaki akan iran a nan gaba,
Yace isra’ila tana kokarin kara fadada rikicin yanki ne ta hanyar kai hari kan abubuwan manfetur din kasar iran, yace isra’ila ba za ta iya shiga wani yaki ba ba tare da samu amincewar Amurka ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci