Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza.

Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu.

Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane.

Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey ba kwararren dan jarida ba ne, mutum ne wanda ya shahara da watsa labarun karya ba tare da dogaro da wata hujja ba.

Bugu da kari bayanin ya sake jaddada matsayar Libya akan batun Falasdinu da kare hakkokinsu na su yi rayuwa a cikin mutunci a cikin kasarsu.

Tun a ranar 25 ga watan Janairu ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump yake magana akan  fitar da Falasdinawa daga Gaza zuwa kasashen makwabta kamar Masar da Jordan,lamarin da kasashen biyu su ka yi watsi da shi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya

Kalli yadda aka karɓi ’yan Najeriya guda 203 da aka dawo da su daga ƙasar Libya.

(Hoto: Onyekachukwu Obi).

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NEMA Ta Karɓi ‘Yan Nijeriya 203 Da Suka Maƙale A Libya
  •  Bom Da Ya Tashi A Arewa Maso Gabashin Najeriya Ya Kashe Mutane 6
  •  Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani
  • Jaridar The Guardian Mafi Yawan ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Ne A Gidan Yarin Kasar Girka
  • HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya
  • Gwamnatin Tarayya Ta Umurci WAEC, NECO Su Koma Amfani Da CBT Nan Da 2026
  • Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi
  • Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano
  • Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba