2025-08-12@10:24:22 GMT
إجمالي نتائج البحث: 416

«cibiyoyin rubuta jarabawa»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Masu zanga-zanga sun kai hari kan ofisoshin jakadancin kasashen waje da dama hari a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC). An bayar da rahoton cewa, fusatattun masu zanga-zangar sun kai wa ofisoshin jakadancin Amurka, Faransa, Belgium, Rwanda, Uganda, Kenya da Afirka ta Kudu hari. Masu zanga-zangar dai na neman hadin kan kasashen waje da yunkurin kasa da kasa na shiga tsakani na soji da kuma dakatar da ‘yan tawayen M23 da ke ci gaba da mamaye wasu sassan yankin gabashi. ‘Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa amma masu zanga-zangar sun samu damar shiga sassan harabar, inda suka yi banka wuta. Rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana yi da kungiyar ta M23 ya yi Kamari a baya bayan...
    Da yake jawabi a taron manema labarai ranar Talata a Yola a madadin Masarautar Fufore, Alkasum Abba, ya ce kafa sabbin Masarautu abu ne wanda sam bai da ce ba kuma an aiwatar da tsarin ba bisa ka’ida ba.   Ya yi ikirarin cewa, sun yi iyakacin kokarinsu na neman tattaunawa da sulhu a kan lamarin da gwamnan jihar amma abin ya ci tura.
    Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da Amurka cikin halin fargaba da dardar. Shafin watsa labaran Al-Quds Al-Arabi, ta yi nuni da cewa Trump ya gabatar da tunaninsa domin hanyar gabatar da shawarwari da tunani tana da dama tare da sabani da siyasa a aikace. Ta ce Trump na fuskantar daukan matakin yin kasadar da zai lalata kyawawan ra’ayinsa da bayyana munanan tunaninsa. Jaridar ta kara da cewa: shugaban na Amurka zai...
    Kwalejin Sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta hada kai da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya SNB domin gudanar da wani taron tattaunawa kan kalubalen aikin jarida na bincike da bayanai a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.   Taron wanda ya gudana a BUK, ya tattaro ‘yan jarida, malamai, da kwararru kan harkokin yada labarai, inda suka tattauna kan yanayin aikin jarida na bincike a yankin.   Taron dai na da nufin gano kalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin bunkasa aikin jarida na bincike a yankin Arewa maso yammacin Najeriya.   A jawabin sa na farko, shugaban SNB wanda kuma shine Shugaban jami’ar tarayya Kashere Gombe Farfesa Umaru Pate ya jaddada muhimmancin bayar da bayanai ta...
    Hamas ta bayyana komawar Falasɗinawa a matsayin nasara, tana mai cewa hakan ya karya yunƙurin da aka yi na tilasta wa mutanen barin gidajensu.
    A ranar 25 ga wata, agogon Najeriya, ofishin karamar jakadiya kasar Sin dake Legas, da tawagar Sinawa wadanda ke kasar, sun gudanar da jerin ayyuka don yin maraba da murnar bikin Bazara na shekarar maciji bisa kalandar gargajiyar Sinawa. An gudanar da bikin nune-nunen abinci, da nune-nunen kayayyaki, da liyafar maraba bi da bi, wanda ya samu halartar mutane sama da 2,000 da suka hada da Sinawa dake kasar da abokai ‘yan Najeriya. Kafin an fara liyafar a maraice, an watsa bidiyon dandanon shagalin murnar bikin Bazara na shekarar maciji na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, Kyan hoton bidiyon mai kayatarwa kuma mai cike da ma’anar kimiyya da fasaha ya matukar burge bakin da ke...
    A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da katin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a matsayin martani ga abokai a jihar Iowa ta kasar Amurka, inda ya ce, Sin da Amurka na da manyan muradun bai daya, da damar yin hadin gwiwa, kuma suna iya zama abokan hulda da aminai. Ya yi fatan jama’ar kasashen biyu za su kara cudanya da juna, da kara yin mu’amala da juna, da yin aiki tare wajen rubuta labarin abokantaka a tsakanin jama’ar kasashen biyu, da ba da sabbin gudummawa ga ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Mohammed Yahaya)  
    Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
    Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya
    Isra’ila ta sako Falasɗinawa 200 daga cikin waɗanda take riƙe da su a kurkuku kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas ta tanada. Wannan dai na zuwa ne bayan da Hamas ta saki rukuni na biyu na ’yan Isra’ilar da ta yi garkuwa da su — wasu sojojin Isra’ila mata da Hamas take riƙe da su tsawon watanni. Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania An ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda A wata sanarwa da hukumomin gidan yari na Isra’ila suka fitar sun ce: “Bayan kammala dukkanin abubuwan da suka wajaba a gidajen yarin da kuma amincewar hukumomi an saki dukkanin ’yan ta’addan daga gidajen yari na Ofer da Ktziot,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na...
    Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya
    “Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni. “Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara da walwalarsu. A matsayinsu na ginshiƙin makomarmu, dole ne mu tabbatar da cewa yara suna cikin aminci da kulawa don cimma burinsu. “Dokar nakasassu ta jihar Zamfara ta nuna ƙudurinmu na kare haƙƙin nakasassu. Wannan na neman kawar da wariya da haɓaka damar shigarsu cikin al’umma. Mun haɗa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da nakasassu, don tabbatar da jin muryoyinsu. “Saboda haka,...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a rundunar arewaci ta rundunar sojin ’yantar da al’ummar Sinawa wato PLA, gabanin Bikin Bazara. Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban hukumar koli mai kula da ayyukan soji (CMC), a madadin kwamitin kolin da hukumar CMC, ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga dukkan jami’an rundunar soji ta PLA, da sojoji ’yan sanda, da fararen hula dake aiki a rundunar soja, da mambobin kungiyoyin sa kai da ma jam’an tsaro da aka kebe domin bukatar gaggawa. A bana, Bikin Bazara na sabuwar shekarar al’ummar Sinawa ya fado ne a ranar 29 ga watan nan na Janairu. (Fa’iza Mustapha)
    Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...