Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Amurka Da Jakadan Sin A Burtaniya Sun Nuna Adawa Da Matakin Harajin Fito Na Ramuwar Gayya Da Amurka Ta Dauka
Published: 5th, April 2025 GMT
A ranar Alhamis ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka da jakadan Sin a Burtaniya Zheng Zeguang, suka bayyana matukar kin amincewa da harajin fito “na ramuwar gayya” da Amurka ta kakaba.
Suna masu nuni da cewa, Amurka ta sanar da karin harajin fito kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe da dama ciki har da kasar Sin, ta hanyar fakewa da abin da take kira ramuwar gayya, ofishin jakadancin Sin da ke Amurka ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, matakin ya saba wa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kuma ya saba wa ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban.
Kazalika, jakadan kasar Sin a Burtaniya, Zheng Zeguang ya ce, yin amfani da harajin fito a matsayin makami ya sabawa ka’idojin WTO, yana kuma yin illa sosai ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kana yana haifar da babbar illa ga moriyar dukkan bangarori, jakadan ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar bikin kaddamar ba da lamunin RMB na kasar Sin na farko kan ayyukan da ke maida hankali kan kiyaye muhalli wato green bond a birnin London.
Har ila yau, Zheng ya ce, kasar Sin tana adawa da karin harajin fito da Amurka ke shirin kakaba wa kan kasar Sin, kuma za ta dauki kwararan matakai don kare muradunta. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: harajin fito
এছাড়াও পড়ুন:
‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka.
Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.
Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.
BBC