Iran Tace:Tattaunawa Tare Da Barazana Ba Tattaunawa Ba Ce, Sai Dai Tursasawa
Published: 10th, March 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa tattaunawa tare da barazana ba tattaunawa ake kiransa ba, sai dai tursasawa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmael Baghaie ya na fadar haka a yau litinin a jawabin mako-makon da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin.
Baghaei ya kara da cewa JMI ba zata taba tattaunawa da Amurka tare da barazana da kuma takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Zabin tattaunawa ko kuma yaki, ba tattaunawa sai dai tursasawa.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa JMI ba ta da zabi, ko ta shiga tattaunawa da Ita Amurka ko kuma ta shiyawa yaki. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya kara da cewa takunkuman tattalin arziki mafi muni wanda Amurka ta dorawa kasar tun shekara ta 2018, sun yi illa da kuma tasiri kan rayuwar mutanen kasar Iran, amma wannan bai sa ta mika kai ga bukatun Amurka ba. Ya kuma kara da cewa ko yakin ma, ba zai tilsatawa kasar Iran mika kai ga bukatunta ba.
Abinda Trump yake kira tattaunawa shi ne wakilan kasar Iran su zauna kan wani teburi, sannan Amurka ta ce, ga abinda zaki yi, ga abinda zaki bari, idan kunki yin haka, to ga makamai.
Ya ce, tattaunawa kam, Iran ta yi hakan a yarjeniyar JCPOA kuma an dauki shekaru biyu cur ina tattaunawa tsakanin kasashe 5 +1 da Iran, daga ciki har da ita Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azamar Gina Kasa A Gabar Da Ake Bikin Cika Shekaru 120 Da Haihuwar Dan Mazan Jiya Chen Yun
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a yi koyi daga akidun dan mazan jiya, kuma jagora na gari Chen Yun, tare da kara azamar dorar da kyawawan dabi’unsa cikin himma da kwazo, don gina kasar Sin mai matukar karfi.
Shugaba Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar koli ta rundunar sojojin kasar, ya yi kiran ne a yau Juma’a, cikin jawabin da ya gabatar, yayin taron bikin murnar cika shekaru 120 da haihuwar Chen Yun, taron da ya gudana a babban dakin taruwar jama’a dake tsakiyar birnin Beijing
Shugaban na Sin ya ce, an haifi Chen a shekarar 1905, ya kuma shiga JKS a shekarar 1925. Ya kuma kasance shahararren dan gwagwarmaya a rundunar ‘yantar da al’umma kuma dattijon arziki, kana daya daga cikin kusoshin da suka kafa tsarin tattalin arziki na gurguzu na kasar Sin. Kazalika, ya kasance muhimmin memba cikin jerin shugabannin JKS zangon farko mai Mao Zedong a matsayin babban jigo, kana da shugabannin JKS zango na biyu mai Deng Xiaoping a matsayin babban jigo. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp