Trump ya janye harajin da ya kara wa duniya, amma ya laftawa China 125%
Published: 10th, April 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da haraje-harajen da ya lafta kan kayayyakin da ke shiga kasar daga kasashen duniya, sai dai ya kara harajin da kashi 125 ga kasar China.
A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaba Trump ya ce za a rage haraje-harajen zuwa kashi 10%, sai dai za a kara wanda aka lafta kan kayan China zuwa kashi 125%.
Donald Trump ya kuma zargi China da nuna rashin girmamawa da kuma zaluntar Amurka.
Kafin haka, China ta sanar da kara haraji kan kayan Amurka da ake shiga da su kasarta zuwa kashi 84% – inda Chinar ta zargi Amurka da barazana kan kasashen duniya.
Matakin na zuwa ne jim kadan bayan da Beijing ta mayar da martani ga karin harajin da Washington ta yi a baya
Trump ya kuma yi nuni da cewa, ba kamar China ba, “wadannan kasashen, bisa ga kwakkwarar shawarata, ba su mayar da martani ta kowace hanya, ko siffa, a kan Amurka ba.”
Kazalika, jami’an Amurka sun bayyana a wannan rana cewa, yanzu kasashe ko kungiyoyin kasa da kasa fiye da 50 sun riga sun tuntubi Amurka kan matakin nata na harajin kwastam.
Wannan lamarin ya shafi kasashe 70 na duniya, wani abu da ya haddasa barkewar rikicin kasuwanci tsakanin Amurkar da kasashe da dama, musamman manyan kasashen da take huldar kasuwanci da su, kamar China da kuma kasashen Tarayyar Turai.
Su ma kasashen Tarayyar Turai sun lafta harajin kashi 25 cikin dari kan kayan da Amurka da ake shiga da su yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya
Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya.
Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki.
Dasuki: Kotu ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kammala shari’ar kuɗin makamai Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ilaYa bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda sauran abokan hulɗa suka riga suka gudanar, ciki har da Shirin Farfado da Yankunan Da Rikici Ya Shafa (MCRP).
Haka kuma, bankin ya jaddada cewa rikice-rikicen tsaro da rashin kwanciyar hankali da ke gudana a yankin sun raba mutane fiye da miliyan 3.5 da muhallansu, lamarin da ya shafi ababen more rayuwa, wanda a cewar bankin hakan ya sa ababen more rayuwan suka yi ƙaranci a garuruwan da suke zama.
Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Mathew Verghis, ya ce: “Muna farin cikin ƙaddamar da wannan shiri mai matuƙar tasiri da zai taimaka wa Nijeriya magance ƙalubalen da take fuskanta wadanda suka shafi ’yan gudun hijira”
“Daga cikin ɓangarorin da za mu mayar da hankali akwai rage illolin sauyin yanayi, samar da haɗin kai ta hanyar sasanci, tallafa wa iyalai da inganta ababen more rayuwa.
“Muhimman fannoni sun haɗa da gina ababen more rayuwa masu jure wa sauyin yanayi, ƙarfafa zaman lafiya, tallafa wa hanyoyin samun abin yi, da kuma ƙarfafa cibiyoyi domin su iya magance matsalolin da tsugunar da ’yan gudun hijirar ya haifar.”
Bayanai sun ce shirin SOLID na iya amfanar da mutane kusan miliyan 7.4, wadanda daga cikinsu miliyan 1.3 ’yan gudun hijira ne.
Za a aiwatar da shirin ne ta hanyar tsari na haɗin gwiwar al’umma, tare da shigar dukkan bangarorin gwamnati da kuma haɗin kai da ƙwararrun abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.