Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-30@19:16:42 GMT

Gwamnatin Jigawa Ta Yi Sabbin Nade-nade A Fannin Ilimi

Published: 3rd, April 2025 GMT

Gwamnatin Jigawa Ta Yi Sabbin Nade-nade A Fannin Ilimi

Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar.

A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr.

Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu.

“Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta ‘yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce mai  kishin jasa da son cigaban ilimi da hidima ga al’umma,” in ji Sakataren Gwamnati.

Haka kuma, Gwamna Namadi ya amince da naɗa Hassan Nayaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Raya Ilimi ta Jihar Jigawa (JERA).

“Kafin wannan mukami, Nayaya ya kasance mukaddashin Shugaban Hukumar. Ya samu digiri a fannin Lissafi daga Jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 2000. Ya fara aiki a ma’aikatar ilimi ta Jihar Jigawa ne tun daga shekarar 1992, har ya kai matsayin Darakta a shekarar 2020,” in ji sanarwar.

Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen suna daga cikin kokarin Gwamna na inganta shugabanci a fannin ilimi da ci gaban al’ummar Jihar Jigawa.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an yi naɗin ne bisa cancanta, kwarewa da nagarta.

“Yayin da ake taya sabbin shugabannin murna, ana fatan za su yi aiki tukuru domin ba da gudunmawa ga ci gaban Jihar Jigawa.”

Sanarwar ta ƙara da cewa dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.

 

Usman Muhammad Zaria 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Sabbin Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci: Nan Ba Da Jimawa Ba, ‘Yan Ta’adda Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu – COAS

Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sabbin Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci: Nan Ba Da Jimawa Ba, ‘Yan Ta’adda Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu – COAS
  • Talauci Da Rashin Ilimi Ne Ya Sa Ayyukan Boko Haram Ke Dawowa – Gwamnan Yobe
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
  • Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
  • Hajjin 2025: An Fara Yi Wa Maniyyata Allurar Rigakafi A Jigawa
  • Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
  • Makafi 37 Sun Zana Jarabawar JAMB A Bauchi
  • Gwamnatin Tarayya Ta Umurci WAEC, NECO Su Koma Amfani Da CBT Nan Da 2026
  • Iran Da Rasha Sun Jaddada Yin Aiki Tare A Fagen Kiwon Lafiya