Gwamnatin Bahrain Ta Kara Kaimi Wajen Kama Yan Adawa Daga Ciki Har Da Yara Kanana
Published: 12th, March 2025 GMT
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana tsaresu.
Shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama ta ADHRB Hussain Abdullah yayi allawadai da kama yan adawa musamman yara kanana kimani 11 da mahukuntan kasar ta Bahrain suka tsare, ba tare da gabatar da su a gaban kotu ba. Har’ila yau tare da hana iyayensu ziyartarsu, ko kuma sanin inda suke.
Sannan akwai rahoton azabtar da wasu daga cikinsu, da hanasu abinci mai gina jiki da kuma rashin kula da lafiyarsu ko basu magani.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da kama aƙalla ’yan daba 100 da ake zargi da tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano.
Kwamishinan INEC na Jihar Kano, Abdu Zango, ya shaida wa manema labarai a Bagwai cewa jami’an tsaro suna aikin tabbatar da zaman lafiya domin a gudanar da zaɓen cikin lafiya.
HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya An kama shi da N25m na sayen kuri’u a zaɓen Kaduna“Dukkanin mutanen da muka gani suna kawo matsala an kama su, kuma zaɓen yana tafiya lafiya.
“Na gamsu sosai da yadda komai ke tafiya. Kayan zaɓe sun isa a kan lokaci, kuma yawancin rumfunan zaɓe sun fara aiki tun ƙarfe 8:30 na safe,” in ji shi.
Zango, ya ƙara da cewa an ɗan samu jinkiri a wasu wurare saboda matsalar sufuri da kuma yunƙurin wasu ƙungiyoyi na kawo cikas.
Amma ya ce jami’an tsaro sun shiga tsakani tare da tabbatar da doka da oda.
Ya ce ko da yake ba zai iya gane mutanen da aka kama ba, rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar masa cewa ta kama aƙalla ’yan daba 100 kuma za a gurfanar da su a gaban kuliya.