Sharhin Bayan Labarai: Zanga-Zanga A Kasashen Larabawa Ta Goyon Bayan Falasdinaw A Gaza
Published: 7th, April 2025 GMT
Assalamu alaikujml/m masu sauraro, sharhin bayan labarummu zai yi magana danagne da zanga-zanga masu yawa wadanda ake yi a kasashen larabawa a dai dai lokacinda HKI take kara tsananta kisan kiyashi a yankin Zirin gaza, wanda ni tahir amin zan karanta.
////.. Madalla, a dai-dai lokacin da sojojin HKI suke kara yawan hare-haren da suke kaiwa Falasdinawa a Gaza, da kuma yadda suke kara kissan kiyashi a yankin, an gudanar da zanga-zanga a kasashen larabawa da dama a ranar litinin, inda mutane a birnin Damaskus na kasar Siriya suka fito kan tituna a birane da dama a kasar suke allawadai da HKI da kuma karin dauke rayukan falasdinawa da take yi a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto masu zanga zanga a birnin Damaskus suna allawadai da HKI, kan hare-hare da kuma kisan kiyashin da take yi a gaza da kuma hare haren da suke kaiwa a cikin kasar ta Siriya na lalata cibiyoyin tsaron kasar da kuma wadanda take kaiwa kan lardin Dra’a dake kudancin kasar sannan sun roki All..rahama ga wadanda suka yi shahada a lardin.
A birnin Halab kuma daliban Jami’ar birnin ne suka fito zanga-zanga suna allawadai da HKI da kuma kissan da take yi a Gaza, sun kuma rera shi’ar, mai cewa (gaba dayammu shahidai ne). Muna kuma goyon bayan gwagwarmayan Falasdinawa a Gaza da sauran yankuna a yankin yamma da kogin Jordan.
A birnin Hama kuma daliban jami’ar birnin ne suka fito zanga-zanga suna allawadai da HKI, da kuma goyon baya ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi da HKI.
Sai kuma kasar Morocco inda daliban kanan makarantu da kuma daliban jami’o’iin kasar suka fito gangami a cikin birane da garuruwan kasar inda suke allawadai da kisan kiyashin da sojojin HKI take yi a Gaza, suna kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi don samun yencin kasarsu wacce aka mamaye.
Sai kuma kasar Jordan inda daliban Jami’a a birnin Amman suka gudanar da gangami a cikin Jami’ar Amman babban birnin kasar suke kuma allawadai da kissan kiyashin da sojojin HKI suke yi a Gaza, sannan sun nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu. Kafafen yada labarai a kasar Jordan sun bada labarin cewa daliban jami’ar Amman sun yi tir da kissan Falasdinawa a Gaza, suna kuma kira ga kasashen larabawa , da kasashen musulmi da kuma duk wani mai yenci a duniya ya tashi ya taimaka don kubutar da Falasdinawa daga halin da suke ciki.
Sai kuma birnin Ramallah na kasar Falasdinu da aka mamaye, masu zanga –zanga suka rera taken girmama shahid Muhammad Dhaif babban kwamnadan dakarun izzuddeen Qassam wanda sojojin yahudawan suka kai ga shahada a cikin yan watannin da suka gabata.
Sannan a areawacin kasar Lebanon kuma, mutanen birnin Tarabulos sun fiti zanga-zangar yan allawadai da yahudawan da kuma kissan kiyashin da suke yi a gaza.
A birnin Tunis na kasar Tunisiya daliban jami’o’ii a kasar sun fito kan tituna a birnin suna allawadai da HKI da kima laifukan yakin da suke aikatawa a kasar Falasdinu. Labaran sun bayyana cewa a garin Susah da kuma Safaqs na kasar mutanen da dama sun fito kan tityuna inda suke allawadai da yahudawan sahyoniya.
Masana da dama suna ganin mafi yawan mutanen kasar Larabawa basa kaunar yahudawan sahyoniyya, amma wasu daga cikin shuwagabanninsu ne suke tare da yahudawan, harma wasu daga cikinsu na kokarin samar da huldar jakadanci da su.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: suna allawadai da HKI Falasdinawa a kiyashin da
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra
A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gwamnatocin kasashen biyu na fadar haka, sun kuma jaddada muhimmancin layin dogon da kuma samar da kasuwar babu kudaden fito a kan iyakokin kasashen biyu.
Labarin ya kara da cewa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya zuwa yanzu ya kai dalar Amurka biliyon $11a ko wace shekara kuma anan saran nan gaba zai iyakaruwa zuwa dalar Amurka biliyon $25.
Rahmatollah Akrami, ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI, da kuma Hazem Majid Naji Al-Khalidi mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara sun jaddada muhimmancin kammala layin dogo tsakanin kasashen biyu, da kuma kasuwar ba kudaden fito tsakanin kasashen biyu. Da kuma fatan zasu yi kokarin amfanar juna gwagwadon abinda zasu iya.