Ayukkan Sojoji Na Taimakawa Wajen Samar da Tsaro a Taraba
Published: 6th, March 2025 GMT
Kwamandan runduna ta 6 ta sojan Nijeriya a jihar Taraba, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya karbi bakuncin mahalarta kwas din Cibiyar Bayar da Agaji ta Sojojin Najeriya (NARC) karo na 7/2025 a wani rangadin karatu a jihar Taraba a hedkwatar rundunar dake Jalingo.
A yayin ziyarar, Janar Uwa ya yi wa mahalarta taron karin haske kan ayyukan gudanar da aiki, nasarori, kalubale, da hasashen da za a yi a nan gaba, inda ya bayyana muhimman nasarorin da aka samu wajen yaki da rashin tsaro a cikin shekarar da ta gabata.
Ya yi nuni da cewa al’amuran satar mutane don neman kudin fansa, fashi da makami, da kuma rikicin kabilanci ya ragu matuka saboda jajircewar sojojin.
A wani bangare na bayanin, Janar Uwa ya baje kolin makamai da alburusai da aka kwato daga ayyuka daban-daban da aka samu nasara.
Ya yaba da kwazo da jajircewar sojojin, wanda jajircewarsu ya taimaka matuka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
A nasa jawabin, shugaban tawagar, Manjo Janar Dahiru Sanusi, wanda ya wakilci Darakta Janar na NARC, Manjo Janar Garba Ayodeji Wahab murabus, ya bayyana godiya ga kwamandan da jami’ansa bisa kyakkyawar tarba da karimcin da suka yi.
Ya yi nuni da cewa, an shirya rangadin binciken ne domin fahimtar aiki da kuma aikace-aikace na zahiri, tare da mayar da hankali musamman kan tantance tasirin ayyukan tsaro na rundunar ga kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs) a cikin jihar.
Za a ci gaba da rangadin ne tare da ziyartan wasu muhimman wurare a fadin jihar ta Taraba, domin baiwa mahalarta damar fahimtar yanayin tsaro da kuma rawar da sojojin Najeriya ke takawa wajen samar da kwanciyar hankali da tsaro.
PR/ Sani Sulaiman
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato
Shi ma dayan, bayan ya bayyana cewa, sun kasance barayin mota ne a jihar Katsina amma wani abokinsu ya gayyace su zuwa jihar Filato domin ci gaba da sana’ar.
Yayin da ya amince zai jagoranci Tawagar Soji zuwa maboyarsu, jami’an sun gano bindiga kirar fistul daya da mukullai da suke amfani da su wajen bude motoci da gidajen jama’a, inda daga bisani shi ma ya yi kokarin arcewa kamar yadda abokin shi ya yi. Hakan ta sa shi ma aka harbe shi har lahira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp