Gwamna Zamfara Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikata.
Published: 6th, March 2025 GMT
Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Yakubu Sani Haidar a matsayin babban shugaban ma’aikatan jihar Zamfara.
Nadin wanda ke fara aiki nan take, ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ta bakin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Sulaiman Ahmad Tudu.
A cewar sanarwar, Haidar ya gaji Ahmad Liman, wanda ya yi ritaya a ranar 28 ga Fabrairu, 2025.
Haidar, wanda ya kammala karatunsa na kimiyyar siyasa a shekarar 1989 a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, an nada shi Babban Sakatare a shekarar 2012, kuma ya yi aiki a ma’aikatu da hukumomi gwamnati da dai sauransu.
Gwamna Lawal ya bayyana godiya ga shugaban ma’aikata mai barin gado bisa sadaukarwar da ya yi wa jihar.
Ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan da aka nada da ya kiyaye mutunci tare da bin ka’idojin aikin gwamnati wajen gudanar da ayyukansa.
REL/AMINU DALHATU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.