HausaTv:
2025-03-15@23:24:02 GMT

Kalibaf: Maganar Donald Trump Akan Tattaunawa Da Iran Yaudara Ce

Published: 9th, March 2025 GMT

Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana.

Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da karfinta.

A yau Lahadi ne shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Kasarsa ba ta jiran wani sako  daga Amurka, kuma za ta dakile dukkanin takunkuman da ta kakaba mata ta hanyar dogaro da karfin tattalin arzikinta da kuma alakarta ta kasa da kasa.

Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Yadda Donald Trump ya yi mu’amala da sauran kasashe, yana tabbatar da cewa managarsa akan tattaunawa yaudara ce, da kuma son raba Iran da karfin da take da shi, ta hanyar sanya ta ja da baya akan wasu tsare-tsarenta na tsaro.

 A cikin kwanakin nan ne dai Donald Trump ya yi batun aikewa da Iran sako yana kiranta zuwa tattaunawa, lamarin da Tehran ta kore.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Karkush: Ganawata Da Arakci A Tehran Ta Yi Kyau

Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau.

Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa:  Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma  aiki tare.”

Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu,  da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Iran a shirye take ta shiga tattaunawa da Turawa bisa mutunta juna
  • Karkush: Ganawata Da Arakci A Tehran Ta Yi Kyau
  • Dangote Da NNPCL Sun Koma Teburin Tattaunawa Kan Cinikin Danyen Mai A Kan Naira
  • Kasar Sin Ta Gabatar Da Shawarwarin Warware Batun Nukiliyar Iran
  •  An Yi Gargadi Akan Rushewar Kungiyar  Agajin Falasdianwa Ta UNRWA
  • Taron Kasashen Iran, Rasha Da China A Birnin Beijing Ya Bukaci A Kawo Karshen Takunkumai Akan Tehran
  • Araqchi: Iran ta karbi Wasikar Trump kuma tana yin nazari a kanta
  • Sojojin Iran Sun Ce A Shirye Suke Su Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana Ga Tsaron Kasar
  • Duniyarmu A Yau: Martani Jagora Ga Trump kan Shirin Nukliyar Kasar Iran
  • Jagora : kiran Trump, na tattaunawa Da Iran yaudarar duniya ne