Masarautar Bauchi Ta Sauya Shawara: Za A Yi Hawan Daushe
Published: 22nd, March 2025 GMT
“Bayan nazari da tattaunawa da gwamnati, Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya amince da gudanar da wannan gagarumin biki,” in ji shi.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a fitar da cikakken jadawalin shirye-shiryen hawan nan gaba kaɗan, tare da fatan Allah Ya sanya ayi bikin lafiya.
A tarihi, Hawan Daushe yana da muhimmanci sosai a al’adun Bauchi, inda sarakuna da masu riƙe da mukamai ke hawa dawakai cikin shiga ta alfarma, tare da nuni da al’adun gargajiya.
Hakan yana jan hankalin jama’a da yawon buɗe ido daga sassa daban-daban.
Masarautar Bauchi ta jaddada cewa ba a bayyana haƙiƙanin labari ba, kuma kwamitin da ke kula da hawan ne ya nemi a soke bikin da farko.
Sai dai bayan shawarwari, yanzu an tabbatar da cewa za a yi Hawan Daushe kamar yadda aka saba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Hawan Daushe Masarauta
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta samu nasarar kama mutane 15 da ake zargi da laifuka daban-daban, ciki har da wani kasurgumin dan fashi da makami mai suna Mu’azu Barga, a wani samame da aka lakaba wa suna “Operation Kukan Kura”.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.
Ya ce samamen, wanda dakaru na musamman suka gudanar a unguwannin Sheka, Ja’oji, da Kurna a ranar 26 ga Yulin 2025, na da nufin gano da kuma hana aikata laifuka, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun.
Kiyawa ya bayyana cewa, wadanda aka kama ‘yan tsakanin shekaru 14 ne zuwa 28, kuma an same su da wayoyin salula guda hudu da suka sace daga hannun mutane daban-daban.
“Wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata sata da fashi, musamman satar wayoyin salula,” In ji shi.
“Mu’azu Barga, wanda ake zargi da kasancewa barawo a lokuta da dama, yana daga cikin wadanda aka kama. Ana danganta shi da laifukan fashi da makami, da kuma. jagorantar hare-hare masu tayar da hankali da fada tsakanin kungiyoyin daba a cikin birnin Kano.”
Kiyawa ya kara da cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ayyana yaki da duk wani nau’in laifi na daba, tare da jaddada kudurin rundunar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya bayyana godiyar rundunar bisa goyon bayan jama’a, tare da yin kira da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani motsi ko mutum da suke zargi da aikata laifi, a ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Abdullahi Jalaluddeen