Kwamatin Majalisar Jigawa Ya Yi Rangadi A Cibiyoyin Ciyar Da Abincin Azumi
Published: 12th, March 2025 GMT
Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba.
Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram.
Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari.
Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun bukaci mai aikin dafa abincin da ya kara yawan shinkafa da ake baiwa kowanne mutum daya, tare da kayan miya domin samun dandano mai gamsarwa.
A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Gwaram Farfesa Abdulrahman Saleem Lawan ya ce akwai cibiyoyin rabon abincin azumi guda 22 a mazabu 11, yayin da ya Samar da cibiya ta 23 a gidansa domin mara baya ga kokarin gwamnatin jihar na ciyar da jama’a a watan Ramadan.
Kwamatin ya kuma duba rabon abincin azumi a cibiyar da ke Babban Masallacin Juma’a na Gwaram da ke fadar Hakimin Gwaram.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: rabon abincin azumi
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Gwamna Namadi Ya Nada Sarkin Kazaure Amirul Hajj
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai.
Gwamnan ya kuma amince da nadin mambobin tawagar Amirul Hajjin.
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, mambobin sun hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure.
Sauran su ne Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia.
Sanarwar ta bayyana cewa an yi wadannan nade-nade ne bisa la’akari da irin kwazon da suka nuna a ayyukansu, sadaukarwa, kishin kasa, amana da kuma tsoron Allah.
A cikin sakon taya murna ga wadanda aka nada, Sakataren Gwamnati ya bukace su da su ci gaba da nuna wadannan dabi’u yayin da za su gudanar da wannan muhimmin aiki da aka dora musu, don kara tabbatar da amanar da gwamnatin da al’ummar Jihar Jigawa suka dora a kansu.
Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran tawagar Amirul Hajjin za ta yi aiki kafada da kafada da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa da kuma sauran hukumomin da suka dace a matakin Jiha, Tarayya da na kasa da kasa domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da inganci.
Sanarwar ta bayyana cewa nade-naden sun fara aiki nan take.
Usman Muhammad Zaria