Jihar Jigawa Ta Yi Garambawul Ga Dokar Bada Tallafi Ga Masu Bukata Ta Musamman
Published: 6th, March 2025 GMT
Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi garambawul ga dokar bada kudaden tallafi ga masu bukata ta musamman domin kara yawan kudaden tallafin daga naira dubu bakwai zuwa naira dubu goma.
Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin kula da al’amuran mata da cigaban al’umma na majalisar.
Da yake gabatar da rahotonsa, shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim, yace kwamatin ya tattauna da masu ruwa da tsaki domin duba bukatar kara yawan kudaden da ake tallafawa masu bukata ta musamman daidai da halin da rayuwa ta ke ciki a yau.
Ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar ya hada da kara yawan makafi da kurame da kutare da sauran masu bukata ta musamman da ke amfana da wannan tallafi daga mutane 150 zuwa 200 a dukkan kananan hukumomin jihar 27.
Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim ya yi nuni da cewar, karin yawan tallafin da kuma wadanda su ke amfana na daga cikin kudurin gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta rayuwar masu rauni a cikin al’umma.
Ya bukaci dukkan masu bukata ta musamman a fadin jihar, su ci gaba da gudanar da addu’oi ga gwamnatin jihar da sauran shugabanni domin samun sukunin sauke nauyin da ke kan su tare da wanzuwar zaman lafiya da cigaban tattalin arziki da zamantakewa a Jigawa da Najeriya ba ki daya.
Bayan Akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar ya gudanar da karatu na 3 akan kudurin, sai shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya sanar da amincewa da kudurin ya zamo doka.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa Majalisar Dokoki
এছাড়াও পড়ুন:
Hajj 2025: Kaduna Ta Gaddamar Da Ayarin Likitoci Da Za Su Kula Da Alhazan Jihar
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar da ayarin likitoci su tara domin kula da lafiyar maniyata aikin hajjin na wannan shekaran.
Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan ganawar farko da ayarin da kuma shugabannin hukumar.
Ayarin likitocin ƙarƙashin jagorancin Dr. Bello Jamoh, za su gudanar da cikakken binciken lafiyar maniyata kafin tafiyar su zuwa kasa mai tsarki da zai gudana a sansanin alhazai da ke Mando, Kaduna.
Sannan kuma za su bayar da taimakon gaggawa a kasar Saudiyya tare da haɗin gwiwar Ayarin likitocin daga Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON).
Shugaban hukumar ya ce mambobin ayarin za su kasance cikin tsari na duba lafiyar mahajjata a tsawon lokacin aikin hajjin.
“Lafiya maniyata aikin hajjin tana da matuƙar muhimmanci, mun zaɓi ayarin ne bisa ƙwarewarsu, kuma muna da tabbacin za su bayar da ingantaccen kulawa ta lafiya a lokacin aikin hajjin,” In ji shi.
Shugaban ya ƙara da cewa za a gudanar da cikakken gwajin lafiya ga dukkan masu niyyar zuwa aikin Hajj, musamman don gano mata masu juna biyu.
“Babu sassauci ko kaɗan wajen barin mata masu juna biyu su tafi Hajj.” in ji Malam Salihu, yana mai jaddada cewa gudunmuwar da ayarin likitocin za su bada wajen tabbatar da wannan doka, na da muhimmanci don bin ƙa’idodin aikin Hajjin.
Ya ja hankalin ayarin likitocin su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da sadaukarwa, domin tabbatar da cewa mahajjata sun samu aikin hajji mai sauƙi cikin koshin lafiya.
Adamu Yusuf