OIC Ta Yi Maraba Da Shirin Gwamnatocin Larabawa Na Sake Gina Zirin Gaza
Published: 8th, March 2025 GMT
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, Hussein Ibrahim Taha, ya bayyana goyon bayan kungiyar ga shirin Larabawa na sake gina zirin Gaza.
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta gudanar da wani zama na musamman na majalisar ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kungiyar, taron da ya gudana a birnin Jeddah na kasar Saudiyya a wannan Juma’a, inda suka tattauna halin da ake ciki dangane da ayyukan wuce gonad a iri na Isra’ila a Falastinu.
A cikin jawabinsa, Sakatare-Janar na Kungiyar Hadin Kan Musulunci ya tabbatar da goyon bayansa ga shirin sake gina zirin Gaza, wanda taron kolin kasashen Larabawa ya amince da shi, tare da jaddada hakkin al’ummar Palasdinu na ci gaba da zama a cikin kasarsu.
Baya ga haka kuma ya yi gargadi dangane da hadarin da ke tattare da matakan da Isra’ila take shirin dauka na korar Falastinawa daga yankunansu a Gaza, da kuam ammaye wasu yankuna a gabar yammacin kogin Jordan, yana mai cewa kungiyar OIC ba za ta taba amincewa da hakan ba.
Babban magatakardar ya jaddada cewa, ba za a iya raba ko kuma maye gurbin hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Falasdinu wato (UNRWA) da kuma muhimmiyar rawar da take takawa wajen yi wa miliyoyin ‘yan gudun hijirar Falasdinawa hidima ba, yayin da ya jaddada bukatar a rubanya tallafin siyasa da kudade ga wannan hukumar.
Babban magatakardar ya yi kira da a kara kaimi wajen aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da janyewar sojojin mamaya gaba daya daga Gaza, da kuma isar da kayayyakin jin kai ga al’ummar yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido.
An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje.
Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar da ingantaccen kulawa.
A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta dauki nauyin kula da lafiyar ido ga mutum sama da 500 daga Birnin Kano da sauran kananan hukumomi.
Shugaban kula da lafiya am matakin farko na ƙaramar hukumar, Alhaji Lawan Jafar, ya ce wadanda lalurar su ba ta tsananta ba za a ba su shawarwarin kula da lafiyar su, da magunguna, wa su ma har da tabarau, yayin da wadanda ta su ta tsananta kuma za a musu tiyata.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna godiya tare da yi wa gwamnati addu’a don samun nasara.
Shugaban tawagar likitocin, Dr. Kamal Saleh, ya tabbatar da cewa shirin ya samu nasara sosai.
Daga Khadijah Aliyu