Gaza: Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sanadiyar Hare-Haren HKI Ya Dara 400
Published: 18th, March 2025 GMT
HKI ta keta yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a jiya inda ta kai hare-hare masu yawa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300 ya zuwa safiyar yau.
Tashar talanijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a kan yankunan zirin Gaza da dama, kuma yawan mutanen da suka yi shahada ya zuwa yanzu ya kai 342 kumamafi yawansu mata da yara ne.
Labarin ya kara da cewa a garin Khan Yunus na kudancin Gaza jiragen yakin HKI sun kashe falasdinawa 77 sannan falasdinawa akalla 20 suka kashe a birnin Gaza. SAMA kamfanin dillancin labaran Falasdinawa ya bayyana cewa daruruwan Falasdinawa sun rasa rayukansu, kuma har yanzun ana neman wasu a wuraren da yahudawan suak kai hare hare.
Tashar talabijin ta Aljazeera ta bada labarin cewa hare-haren yahudawan sun game dukkan zirin gaza kuma sai da suka girgiza yanking aba daya.
Wasu masana suna ganin sojojin yahudawan sun yi amfani da sabbin makamai masu tun 20 wadanda gwamnatin Trump ta bawa HKI bayan ya dare kan kujerar shugabancin kasar ta Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zargin yin katsalandan a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya musanta zargin katsalandan din Iran a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza.
A yayin da yake amsa tambaya game da ikirarin da shugaban kasar Amurka ya yi na cewa Iran na tsoma baki a shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da dukkan kasashen duniya tana yin kakkausar suka kan kisan gillar da ake yi a Gaza tare da goyon bayan duk wani tsari da zai kai ga dakatar da aikata laifuka da kuma rage radadin wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki.
Baqa’i ya jaddada cewa; Masu yin shawarwarin Hamas sun fahimci bukatar neman cimma muradun al’ummar Gaza da ake zalunta ta hanyar da ta dace, kuma ba sa bukatar shiga tsakani na bangarori na uku dangane da hakan.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya yi la’akari da katsalandan din Iran a cikin shawarwarin da suka dace da cewa ba shi da tushe balle makama, yana mai jaddada cewa irin wadannan zarge-zarge wani nau’i ne na neman tauyaye hakki da gujewa hakkin da ya rataya a wuyar mutum da kokarin Amurka na gujewa duk wani mugun aiki da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aikita kan al’ummar Falasdinu, da suka hada da kisan fararen hula 60,000 da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da kananan yara da kuma killace Zirin Gaza tsawon watanni. Da hana shigar agajin jin kai da kuma kashe fararen hula da ke fama da yunwa da kishirwa a tarkon kisa a wuraren da ake kira cibiyoyin rarraba kayan agaji da wata cibiyar Amurka ta kafa.