Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Matakin Isra’ila Na Hana Shigar Da Kayan Agaji A Gaza
Published: 3rd, March 2025 GMT
Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa.
Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar ta yi Allah-wadai da kuma yin tir da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin jin kai ga Gaza, tare da yin amfani da shi a matsayin wani makami na cin zarafi da azabtarwa.
Masar ta kuma yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da duk wani agajin jin kai a zirin Gaza a matsayin “ketare iyaka” na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
Ma’aikatar harkokin wajen Masar a cikin wata sanarwa da ta fitar “ta yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin jin kai da mashigin da ake amfani da shi wajen kai agaji.”
Ma’aikatar ta ce “wadannan ayyukan sun saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta, dokar jin kai ta kasa da kasa, Yarjejeniyar Geneva ta Hudu, da dukkan ka’idojin addini.”
Yarjejeniyar Geneva ta hudu da aka amince da ita a shekarar 1949 bayan yakin duniya na biyu, ta ta’allaka ne kan ba da kariya ga fararen hula, ciki har da yankunan da aka mamaye.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta dauka na
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24.
Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 da su ka gabata.
A cikin sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” mutane 3 sun yi shahada da su ka hada da karamar yarinya sanadiyyar harin da sojojin na HKI su ka kai wa yankin.
A gabashin birnin Khan-Yunus ma dai wasu Falasdinawa sun yi shahada.
Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun wuce 52,000,wadanda su ka jikkata kuma sun haura 100,000.