HausaTv:
2025-08-13@10:00:01 GMT

Tawagar ECOWAS Ta Fice Daga Guinea-Bissau Bayan Barazana Daga Shugaban Kasar

Published: 3rd, March 2025 GMT

Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar.

A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.”

Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa.

ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci.

Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata.

 Amma daga bisanio ya zarge su da wuce gona da iri ta hanyar tattaunawa da wasu shugabannin ‘yan adawa.

Ita dai tawagar ta ECOWAS, an dora mata alhakin samar da mafita ta samar da zaman lafiya a kasar Guinea-Bissau, ta hanyar mai da hankali kan cimma matsaya ta siyasa kafin zaben da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Umaro Sissoco Embalo ke shiga takun tsaka da tawagar ECOWAS a kasar sa ba. A lokacin da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa tare da goyon bayan jami’an tsaro, ya kori mambobin ECOWAS da ke kasar tare da tare da cewa bai maraba da wakilin kungiyar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm

Biyo bayan sanarwar hadin gwiwa bayan taro kan tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin Sin da Amurka a birnin Geneva a ranar 12 ga watan Mayun 2025 wato sanarwar Geneva, da tarukan da aka yi a birnin London a ranekun 9 da 10 ga watan Yunin 2025, da wanda aka yi a Stockholm a ranekun 28 da 29 ga watan Yulin 2025, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin da gwamnatin Amurka, sun waiwayi alkawuran da suka dauka karkashin sanarwar hadin gwiwa ta Geneva, kuma sun amince cewa daga ranar 12 ga watan nan na Agusta, za su fara aiwatar da matakai kamar haka:

Amurka za ta ci gaba da gyara matakan karin haraji kan kayayyakin kasar Sin, ciki har da na yankin musammam na Hong Kong da na Macau, wanda tana cikin umarni shugaban kasar mai lamba 14257 na ranar 2 ga watan Afrilun 2025, ta hanyar dakatar da maki kaso 24 na karin har na tsawon kwanaki 90, daga ranar 12 ga watan Agustan bana, yayin da za a ci gaba da aiwatar da karin harajin kaso 10 kan wadannan kayayyaki bisa tanade tanaden wannan umarni.

Ita kuma a nata bangare, kasar Sin za ta ci gaba da gyara matakan karin haraji kan kayayyakin Amurka da aka tanada cikin umarni mai lamba 4 ta 2025, na babbar hukumar kwastam ta majalisar gudanarwar kasar, ta hanyar dakatar da maki kaso 24 na karin har tsawon kwanaki 90, daga ranar 12 ga watan Agustan bana, yayin da za a ci gaba da aiwatar da karin harajin kaso 10 kan wadannan kayayyaki. Haka kuma, Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakan dakatarwa ko cire matakan ramuwa da ba na haraji ba da ta dauka kan Amurka, kamar yadda bangarorin biyu suka amince cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar a Geneva. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Bago Ya Yabawa Tinubu Kan Kama Shugaban Kungiyar Ta’addanci A Neja
  • Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka
  • Ronaldo Zai Daura Aurensa Na Farko A Rayuwa Tare Da Budurwarsa Georgina
  • Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm
  • Majalisar Kano Ta Karbi Kudirin Karamin Kasafin Kudi Na Shekarar 2025
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Kungiyar Asiri Ne A Jihar Kwara
  • Tinubu Ya Sake Nada Dankaka A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Ta Kasa
  • Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Gobe Talata
  • Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Don Yi Wa Iyalan Ogbeh Ta’aziyya
  • ‘Yan Ta’addar ISWAP Sun Kashe Shugaban Mafarauta A Borno