Aminiya:
2025-06-15@06:44:42 GMT

Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace

Published: 4th, March 2025 GMT

Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke.

Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa?

An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki

Bayan haka, akwai turaren humra wadda za a iya shafa shi a gashin kai.

Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai, wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga.

Lallai duk macen da ta kasance cikin ƙamshi, za ta sami girmamamwa a cikin al’umma da kuma mai gidanta.

Kuma akwai turaren kanti kamar su ‘Dior’ da cool water da sauransu.

Yadda za ai amfani da turaren gargajiya

A sami kabbasa (za a iya saminsa a kasuwa) da kasko, a zuba garwashin wuta sannan a dora kabbasar a kai.

A kuma zuba turaren wuta a cikin garwashin sannan sai a rufe kabbasa da kayan da za a saka a ranar ko kuma wanda za a je unguwa da su, hayakin ya shiga kayan sosai.

Bayan haka, sai a shafa kulaccam (kamar man shafawa yake amma da turaruka aka hada shi).

Bayan an yi wanka sai a shafa a matsayin man shafawa. Sannan sai a saka riga a shafa humra fari ko baki a jikin kayan.

Idan kayan mai duhu ne sai a saka humra baƙa. Idan kuma kayan masu haske ne sai a saka farar humra.

Idan kuwa ana son amfani da turaren kanti, fesawa kawai ake yi.

Amma na gargajiya ya fi daɗewa a jiki don kuwa ko kaya sun yi datti da ƙyar a ji warin kayan don ƙamshin turaren.

Irin waɗannan turaruka na taimaka wa masu jego wajen rage ƙarnin nono a jikinsu da kuma jikin jariri.

Sai a ga wasu matan daga sun haihu, suna ƙarni, ɗan da suka haifa ma idan an ɗauka sai a ji cewa yana ƙarni.

Wani ƙarnin jinjirin ma har ya shafi wanda ya ɗauki jinjirin.

Don haka, sai a kula wajen amfani da turare domin magance waɗannan matsalolin.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Turare

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato 

Aƙalla mutum 41 aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da aka kai wa jama’a daban-daban a Jihar Filato cikin mako guda da ya gabata.

Yankunan da aka kai wa hari sun haɗa da Bassa, Riyom, Bokkos da Ƙaramar Hukumar Mangu.

Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya

Hakazalika, an ruwaito cewa ɗaruruwan mutane sun rasa matsugunansu, an kuma ƙone gidaje da ba a san adadinsu ba.

Ɗaya daga cikin mafi munin hare-haren ya auku ne a ranar 8 ga watan Yuni, a ƙauyen Bauda da ke yankin Langai a Ƙaramar Hukumar Mangu.

’Yan bindiga sun shiga garin da sassafe, inda suka kashe mutum bakwai tare da ƙond gidaje 61, ciki har da cocin COCIN LCC.

A daren ranar, wasu ’yan bindiga sun sake kai hari garin Chinchim da ke yankin Mangu, inda suka kashe mutum takwas.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Mangu, Emmanuel Bala, ya tabbatar da aukuwar hare-haren.

“Mutane na cikin gidajensu lokacin da aka kai musu hari. An fi amfani da wuƙa wajen kashe su. Mutane takwas aka kashe a Chinchim. Kafin nan, mutane bakwai aka kashe a Bwai, kuma mun yi musu jana’iza a ranar Talata.”

Washegari, 9 ga watan Yuni, an sake kai hari a Gyenbwas da ke Langai, inda aka kashe mutum uku, an kuma ƙone gidaje sama da 90 ciki har da ginin JNI.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun sace abinci, shanu, katifu da sauran kayayyaki.

Sakataren Ƙungiyar Gan Allah Fulani Development Association of Nigeria (GAFDAN), Abubakar Garba, ya musanta zargin cewa Fulani ne suka kai hare-haren.

“Ba ma goyon bayan tashin hankali. Mambobinmu masu bin doka ne. Muna kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike don gano masu laifi,” in ji shi.

Wannan rikici ya daɗe yana faruwa tsakanin manoma da makiyaya a yankin, inda suke yawan kai wa juna hare-hare, lamarin da ke ƙara haifar da rashin yarda a tsakaninsu.

Wasu na ɗora laifi kan wasu ƙabilu, wanda hakan ke ƙara dagula lamarin.

A ranar 7 ga watan Yuni, an kashe mutum huɗu a ƙauyen Uwok-Ishe da ke Kekkek a Bassa.

Har ila yau, an sake kai hari Riyom, inda aka kashe wani yaro guda ɗaya, wani kuma ya jikkata.

Rahotanni sun ce an kashe wasu makiyaya biyu a Ancher, yayin da a Kwall aka kashe mutum uku, bayab kai wani hari cikin dare.

Duk da waɗannan hare-haren da suka faru a cikin ƙanƙanin lokaci, Gwamnatin Jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa ba.

Har ila yau, babu wani martani daga kakakin rundunar ’yan sandan jihar ko rundunar Operation Safe Haven (OPSH), duk da ƙoƙarin da manema labarai suka yi na jin ta bakinsu.

Masana tsaro sun bayar da shawara kan yadda za a magance matsalar.

Tsohon jami’in ’yan sanda, SP Bulus Ajiji, ya ce: “Rashin haɗin kan al’umma da kuma rashin bayar da bayanai ga jami’an tsaro na daga cikin matsalolin. Wasu jama’a na kare miyagu kai-tsaye ko ba tare da sani ba.”

Masanin zaman lafiya kuma malami a jami’a, Joel Baba Alfa, ya bayar da shawarar matakan da za a ɗauka.

“Ya kamata gwamnati ta kai farmaki wajen da maharan ke ɓuya maimakon jiran suka kawo hari. Kuma a ƙirƙiro rundunar zaman lafiya ta al’umma wacce za ta ƙunshi dukkanin ɓangarorin da ke rikici da juna.”

Ya kuma ƙara da cewa: “Dole a riƙa bayyana gaskiya. Idan shanu sun mutu ko gonaki sun lalace, sai a sanar da jama’a. Haka kuma, kafofin watsa labarai su guji ɗaukar ɓangaranci kan addini ko ƙabila domin kaucewa tayar da rikici.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Isra’ila da Iran su daidaita rikicin da ke tsakaninsu — Gwamnatin Tarayya
  • Muhimmanci, Tasiri Da Kuma Amfanin Jigida Ga Mata
  • Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu — Gwamnatin Tarayya
  • Ya kamata Isra’ila da Iran su kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu
  • Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya
  • Gwamnatin Tarayya Ta Dukufa Wajen Karya Farashin Kayan Abinci – Minista
  • IRGC : Iran a shirye take na tunkarar duk wani yanayi
  •   Bokoharam Ta Kashe Sojojin Kamaru Ta Hanyar Amfani Da Jirgin Sama Maras Matuki
  • Zamfara: APC Za Ta Maka PDP A Kotu Kan Zargin Matawalle Da Hannu A Satar Mutane
  • An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato