HausaTv:
2025-07-26@17:32:29 GMT

An kori ma’aikatan Microsoft saboda adawa da yahudawan sahyoniya

Published: 28th, February 2025 GMT

Kamfanin Microsoft ya kori ma’aikata biyar bayan da suka nuna rashin amincewa da kwangilar da kamfanin ya kulla da sojojin Isra’ila.

A rahoton cibiyar yada labarai ta Falasdinu, ma’aikatan sun gudanar da zanga-zangar ne a hedkwatar Microsoft da ke Redmond a birnin Washington, sanye da riguna masu dauke da taken nuna adawa da amfani da fasahar kamfanin wajen kai wa Falasdinawa hari.

Matakin ya zo ne bayan da aka buga wani rahoto da ke nuna cewa an yi amfani da bayanan sirri na wucin gadi da na’urar tantance gajimare na Microsoft wajen ayyukan sojojin Isra’ila.

Bayan wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya yi a baya-bayan nan, ya bayyana cewa kamfanonin fasahar kere-kere na Amurka sun taimaka wa Isra’ila wajen kara yawan laifuka da kashe-kashe a Gaza da Lebanon ta hanyar samar da kayayyakin leken asiri ga gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Jaridar The Guardian ta Burtaniya ta bayar da wani rahoto da ke cewa,  Microsoft ya karfafa alakarsa da sojojin Isra’ila tare da ba su tallafin fasaha a yakin Gaza.

Jaridar Guardian ta kara da cewa dogaron da sojojin Isra’ila suka yi kan fasahar Microsoft ya karu matuka a lokacin yakin Gaza, kuma sun yi amfani da hakan wajen aiwatar da kashe-kashe kan Falastinawan Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: sojojin Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!

“Mun kasance muna jiran a ba mu garin alkama, saboda muna jin yunwa sosai, muna neman abin sha da abinci, kwatsam tankokin sojan Isra’ila suka zo suka kewaye mu, suka fara harba bindiga a kanmu, ba mu iya motsawa ba. Ba mu samu gari ba, an kuma kewaye mu na tsawon sa’a daya da rabi zuwa biyu, wasu sun gudu, wasu an kashe su, wasu kuma sun ji raunuka.” In ji wani dan Gaza game da abin da ya faru gare shi a ranar 21 ga wata.

Tsawon kwanaki 140 ke nan da Isra’ila ta rufe hanyoyin shiga Gaza. A halin yanzu, kashi 93% na iyalai a Gaza ba su da ruwan sha, kuma fiye da kashi 87% na yankunan Gaza sun zama yankunan soja ko kuma sassan da mazauna wurin suka bar muhallansu, kusan mutane miliyan 2.1 aka tilasta musu shiga wani karamin yanki, ba su da abubuwan da ake bukata na yau da kullum. Isra’ila ta hana shigar da kayayyakin agaji, da garin madarar jarirai da man fetur, wanda ya sa abinci da magunguna suka kusan kare a Gaza. Fararen hula na Gaza da dama da suka je wuraren rarraba kayayyakin agaji na Isra’ila da ake kira “Gaza Humanitarian Foundation” (GHF) sojojin Isra’ila ne suka harbe su. Firaministan Falasdinu Muhammad Mustafa ya ce adadin wadanda aka kashe ya wuce 995. A Gaza, Isra’ila tana amfani da yunwa a matsayin makami, har ma wuraren rarraba abinci sun zama “tarkon mutuwa”, mutanen Gaza ba su samu gari ba, a maimakon haka ana kashe su da harbin bindiga.

A ranar 21, kakakin harkokin wajen kasar Sin ya jaddada cewa bai kamata a rika kai wa fararen hula hari ba, kuma bai kamata masu ba da agaji na kasa da kasa su fuskanci barazanar tsaro ba. Bugu da kari, kwanan nan kasashe 25 sun fitar da sanarwar hadin gwiwa suna bukatar a kawo karshen yakin yankin Gaza nan take, tare da bukatar Isra’ila ta bi dokokin kasa da kasa na jin kai, da kuma soke takunkumin da aka sanya na shigar da kayayyakin agaji.

Da fatan gwamnatin Isra’ila za ta saurari kiran kasa da kasa na kada ta yi amfani da “yunwa a matsayin makami”. Da kuma gaggauta dakatar da yakin nan take a yankin Gaza, don ba da damar shigar da kayayyakin agaji cikin sauki, tare da tabbatar da hakkin fararen hula.(Mai zane da rubutu: MINA)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jagora: Za’a Gaggauta Ci Gaba A Ilmi Da Fasahar Tsaron Sojojin Kasar
  •  Gaza: Ana Ci Gaba Da Samun Shahidai Da Yunwa Take Kashewa A Gaza
  • Miliyoyin Al’ummar Yemen Sun Fito Taron Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Falasdinawa
  • Mutanen A Netherlands Suna Zaman Dirshen Saboda Gaza
  • Hukumar Ba Da Agajin Jin Kai Ta ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa Ta “UNRWA” Ta Sanar Da Kashe Ma’aikatan 330 A Gaza
  • Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza
  • Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
  • Iran: Sojojin Ruwan Iran Sun Kori Jirigin Yakin Amurka Daga Tekun Oman
  • A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
  • Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!