Ƴansanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan Bijilanti A Tawagar Sarki Sunusi II
Published: 31st, March 2025 GMT
Hukumar Ƴansandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 20, Usman Sagiru, bisa zargin kashe wani ɗan Bijilanti a tawagar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II bayan Sallar Eid. Iftila’in ya faru ne da ƙarfe 12:40 na rana a Lahadi, lokacin da ayarin Sarkin Kano ke watsewa daga filin Sallar Idin.
A cewar kakakin Ƴansanda SP Haruna Kiyawa, ana zargi Sagiru da wasu da suka tsere da soka makami ga wani ɗan sa kai mai suna Surajo Rabiu daga unguwar Sabon Titi Jaba, wanda ya mutu sakamakon raunin.
Wani ɗan Bijilanti, Aminu Suleman daga Kofar Mata, shi ma ya jikkata a harin wanda yana yanzu yake jinya a Asibitin Murtala Muhammad na Jihar Kano. Waɗannan ‘yan sa kai sun kasance cikin tawagar da ke kare Sarkin Kano a lokacin harin. ‘Yansandan sun bayyana cewa sun fara cikakken bincike kan lamarin, inda suka kuma gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin yi masa tambayoyi dangane da lamarin.
Hukumar ta sake nanata haramcin duk wani irin hawan Sallah a jihar, tare da gargadin cewa za a kai duk wanda aka tarar yana shiga irin waɗannan ayyuka gaban doka. A cewar sanarwar, ‘yan sandan sun dage kan yaƙi da daba da duk wani aiki da zai haifar da tarzoma a jihar, musamman ma a yayin da ake shirye-shiryen bikin Sallah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kwara Ta Kwashe Mabarata Daga Titunan Jihar Su 94
Gwamnatin jihar Kwara ta kori mabarata 94 daga titunan Ilorin, domin tantancewa, gurfanar da su da kuma mayar da su gida.
Da take magana da ‘yan jarida yayin aikin, kwamishiniyar jin dadin jama’a da ci gaban jihar Dr Mariam Nnafatima Imam ta ce wadanda aka kama domin dawo da su sun hada da mata 43 da maza 51.
Ta ce ma’aikatar ta yi aikin dawo da mabaratan domin an haramta barace-barace a jihar Kwara.
Imam ya godewa gwamnan jihar bisa kokarin da yake yi na ganin jihar ta kawar da barace-barace a kan tituna da sauran matsalolin zamantakewa .
Kwamishinan ta ce a ko da yaushe gwamnatin jihar tana tuntubar gwamnatocin jihohin masu bara a tituna kafin a mayar da su jihohinsu.
A nasa jawabin, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kwara kan sha da fataucin miyagun kwayoyi, Haliru Mikail ya ce galibin mutanen da ke bayyana kansu a matsayin mabarata suna safarar kwayoyi.
Ya ce aikin dakile barace-barace a kan tituna zai ci gaba da kasancewa domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
A nasa bangaren, shugaban sashin da ba na kariya ba, rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kwara Mista Adebayo Okunola ya bayyana cewa, an gudanar da aikin ne domin tsaftace jihar daga matsalolin zamantakewa yayin da wadanda aka kama tare da gurfanar da su a gaban kotun da ta dace za a hukunta su daidai da dokar jihar ta 2019.
Ya yi nuni da cewa hukumar da ke aikin za ta tabbatar da hukunta wadanda aka kama.
An gudanar da aikin ne a wasu yankuna da aka zaba a cikin birnin Ilorin da suka hada da Geri Alimi, Junction Tanke, Garage Offa, Garage Tipper da Zango, da dai sauransu.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU