2025-10-13@22:00:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4223

«Zamora»:

    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya ƙaddamar da shirin tallafa wa mata 1,400 da kayan sana’ar ɗinkin hula domin bunƙasa harkokin kasuwancinsu. A wajen bikin raba kayan, Gwamna Namadi ya ce ɗinkin hula tsohuwar sana’a ce da mata suka gad tun daga iyaye da kakanni, wadda ke taimaka musu wajen dogaro da kai da...
    Ana ta rade-radin an baki sarauta, shin mene ne gaskiyar maganar? Alhamdulillah, maganar an bawa Zahra’u sarauta ba karya ba ne, hakkun haka ne an ba ni sarauta.   Mutane za su so su ji, shin daman Haj. Zahra’u ‘yar Ghana ce, tana da sarauta a Ghana? A’a! Ni ba ‘yar Ghana ba ce, ba...
    ’Yan sanda sun harbe wasu mayaƙan Lakurawa har lahira a yayin da ragowar suka tsere a yankin Gorun Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Dandi da ke Jihar Kebbi. Kakakin rundunar, SP Nafi’u Abubakar , a cikin wata sanarwa a ranar Asabar ya ce bayan samun rahoton harin ’yan ta’addan a yankin ne ’yan sanda suka...
    Kanunfari kamar guda bakwai 7, daidai lokacin da za a kwanta barci a rika taunawa ana hadiye ruwan. Ko kuma a nemi man kanumfarin a rika shan karamin cokali kafin kwanciya barci. In sha Allah za a rabu da wannan matsalar. A samu zuma tatacciya mai kyau mara hadi a dinga wanke baki da ita...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Bai kamata dokar kasa da kasa ta zama abin wasa a hannun Amurka ba A wata wasika da ya aikewa takwarorinsa na kasashen Sri Lanka da Maldives, ministan harkokin wajen Iran ya yi gargadin cewa: Kada dokokin kasa da kasa su zama abin wasa a hannun Amurka, ya...
    Shugaban Amurka ya ce: Dole ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta daina kai hare-hare kan Gaza nan take domin samun damar sakin fursunoninta Shugaban Amurka Donald Donald Trump, bayan da kungiyar Hamas ta fitar da martanin kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza, ya yi kira ga gwamnatin mamayar Isra’ila da ta gaggauta dakatar da kai hare-hare...
    Babban jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Mika fursunoni da gawarwaki cikin sa’o’i 72 ba gaskiya ba ne a halin da ake ciki yanzu. Babban jami’in kungiyar Hamas Musa Abu Marzouk ya tabbatar a ranar Juma’a cewa, batun mika fursunoni da gawarwakin yahudawan sahayoniyya cikin sa’o’i 72 lamari ne na nazari, ba tabbas ba, a...
    Hukumar kashe gobara ta yankin Gaza ta ce a ranar Asabar, sojojin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a birnin Gaza duk da kiran da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na a dakatar da luguden wuta bayan ƙungiyar Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta. A ranar Asabar din nan da karfe 6 na...
    ’Yan bindigar da ke addabar yankunan karkara sun kaƙaba sun ƙaƙaba musu haraji da ke kaiwa Naira miliyan 10 a Ƙaramar Hukumar Mashegu Jihar Neja. Rahotanni sun nuna cewa an umarci al’ummomin yankunan Babban Rami da Kaboji su su biya Naira miliyan biyu-biyu. Yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami an umarce su da su Naira...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa.   Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta...
    Bincike ya kuma kai ga cafke wani bangare na kungiyar karkashin jagorancin Babangida, wadanda aka gano sun hada da Isah Musa da Usman Abdullahi, wadanda suka amsa laifin karya shaguna da kuma yin fashi a yankin Rigasa. Lokacin bincike, wadanda ake zargin sun ambaci masu karbar kayan sata da suka taimaka musu wajen sayar da...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadin cewa amincewa da takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Iran ba bisa ka’ida ba ya sabawa dokokin kasa da kasa, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su bijirewa haramtattun takunkuman. Jakadan Iran a Colombo Alireza Delkhosh ya bayyana cewa, gargadin na ministan harkokin...
    Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da farmakin da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan jiragen ruwan ‘yan fafatuka dake dauke da kayan agaji ga al’ummar Gaza. Hamas ma ta yi Allah wadai da farmakin kan Global Sumud Flotilla a iyaka da Gaza wanda ta danganta a matsayin “laifi na...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Jihar Legas zuwa Jos, babban birnin Jihar Filato, a ranar Asabar, 4 ga watan Oktoba, domin halartar jana’izar Nana Lydia Yilwatda Goshwe, mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nantewe Yilwatda Goshwe. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Shugaban Ƙasa zai kuma gana...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi daga Legas zuwa Jos, Babban Birnin Jihar Filato, a ranar Asabar domin halartar jana’izar mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nantewe Yilwatda Goshwe. Zai halarci jana’izar Nana Lydia Yilwatda Goshwe, mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa. Ana fargabar mutuwar mutane a gobarar tankar mai Boko Haram ta...
    A kan zaben 2027, Abdullahi ya ce ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar sun yarda za su goyi bayan duk wanda ya lashe zaben fid da gwani. “Dukkan ‘yan takarar shugaban kasarmu sun yarda za su goyi bayan wanda ya ci zaben fid da gwani da jam’iyyar za ta gudanar,” in ji shi. Ya kara...
    A yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Grand Duke Guillaume na Luxembourg bisa hawa karagar mulki. Xi ya yi nuni da cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Luxembourg a cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata, a ko da yaushe suna mutunta juna...
    Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da...
    Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance. “Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00...
    Sakatarin majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya soki kasashen yamma da kokarin tursasawa Iran kan shirinta na makamashin Nukliya da kuma makamanta masu linzami. Ya maimakon su dauki hanyar tattaunawa da diblomasiyya sai sukazami hanyar tursasawan da kuma nuna karfi. Larijani ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da...
    Firai ministan kasar Beljium Bart De Wever ya fadawa sauran tokororinsa na kasashen turai kan cewa bai amince a yi amfani da kudaden Rasha da aka kwace a kasashen turai don yakar kasar a Ukraine ba, sai tare da wasu sharudda. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Wever ya na fadar haka,...
    Sojin Isra’ila sun kame dukkan jerin jiragen ruwa masu dauke da kayan agaji da ke ƙoƙarin shiga Zirin Gaza, inda suka kama daruruwan masu kai agajin tare da ɗaruruwan jiragen. Bidiyon da ken una tafiyar jiragen kai tsaye ya nuna yadda sojojin Isra’ila suka kutsa cikin jirgin ƙarshe da safiyar Juma’a. Fashewar tukunyar gas ya...
    Ita dai wannan yarjeniyar wadda wanda mamallakin karamin Jirgin Sama, zai bayar da hayar Jirginsa na Sama, ba tare da ma’aikata da kula da Jirgin da kuma yin inshore ba. Akasarin wannan yarjeniyar ana yinta da takardar shedar mamallakan Jiragen Samn wato AOC. “Hakan ya nuna cewa, mun fara shiga cikin matakin fafada harkar kasuwanci...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan.   A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu.   Ya kuma...
    Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar.   Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar.   Gwamnan...
    Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ofishin Kano, ta gudanar da wani taron kara wa masu yi wa kasa hidima na NYSC aiki a karkashin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (EMVs).   An zabo mahalarta taron ne daga kungiyoyin ci gaban al’umma (CDS) a kananan hukumomin Tarauni da Dawakin Kudu Kano.   An...
    “Muna tabbatar da inganta tsarin na PCS domin a kara tabbatar da karfafa gasa a fadin diniya a fannin na sufurin Jiragen Ruwa na NPA wanda hakan zai kuma kara samar da damar janyo masu zuba hannun jari daga waje na kai tsaye da kuma kara karfafa tattalin arzikin kasar, a nan gaba,”. A cewarsa,...
    Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya isa birnin bandar Abbas a jiya alhamis gari na 10 ke nan a ci gaba da ziyarar aiki yi a fadin jihohin kasar, da yake kaddamar da ayyukan ci gaba da aka kammala. Ziyarar ta shugaban kasa a jihohi tana taimakawa wajen samar da cundanya...
    Ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta fadi cewa akalla sama da falasdinawa 66225  ne suka rasa rayukansu, yayin da 168938 kuma suka jikkata a aci gaba da kiran kare dangi da HKI ke yi a yankin gaza tun daga watan oktoban shekarar bara da ta gabata. Akalla fararen hula 77 ne ake kaashewa 222 kuma...
    Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran tayi  Allah wadai da da irin bayanan da kungiyar G7 ta yi game da shirin nukiliyarta, kuma ta bayyana shi a matsayin munafunci da kuma canza gaskiya , Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il baghae ya fadi cewa kungiyar G7 ta amince da matakin da ya sabama doka da...
    Fira ministan kasar malesiya Anwar Ibrahim da na Pakistan shehbaz sharif suna tir da matakin da HKI ta dauka kan jiragen tawagar Sumud Flotilla  ajiya Alhamisi a shafukansu na X , bayan da jagororin tawagar suka sanar da cewa sojojin HKI sun kama jiragen ruwa guda 14 dake dauke da yan kasashen waje da kayayyakin...
    Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”.   Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a...
    A yau Alhamis, kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, layin dogo na kasar Sin ya gudanar da balaguron fasinjoji miliyan 23.13 a jiya Laraba, wato ranar farko ta hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na tsawon kwanaki 8. A cewar kamfanin sufurin jiragen kasan,...
    Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane a Nijeriya (NAPTIP) ta ce ta kama wani mahaifi yana yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Mai magana da yawun hukumar NAPTIP na ƙasa, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku...
    A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa.   Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano. Zanga-zangar...
    Gwamnatin Rasha ta jaddada cewa: Yarjejeniyar dabarun da kulla da Iran dole ne a aiwatar da ita Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar a yau Alhamis a cikin wata sanarwa cewa: Yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Rasha da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara aiki, tare da tabbatar da cewa kasashen biyu bisa tsarin yarjejeniyar...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun jaddada aniyarsu ta watsi da duk wata barazanar makiya tare da alwashin mayar da martani mai tsanani fiye da harin alkawarin gaskiya da ya gabata A cikin wani sako mai kakkausar murya, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da...
    Sojojin Yemen sun kai hari kan wani jirgin ruwa da yake hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar da cewa, da sanyin safiyar ranar Larabar nan, sun kai hari kan jirgin (MINERVAGRACHT) da makami mai linzami a mashigin tekun Aden. Sanarwar da Rundunar Sojin Yemen ta fitar ta...
    Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta sanar da cewa; A kowace rana Falasdinawa guda 100 ne suke yi shahada saboda zaluncin sojojin mamayar Isra’ila Babban kwamishinan hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya bayyana cewa: A kowace rana sojojin mamayar Isra’ila suna kashe kimanin Falasdinawa 100 a zirin Gaza....
    Masar ta jaddada goyon bayanta ga zaman lafiyar Sudan tare da yin watsi da matakan bangare guda kan kogin Nilu Kasar Masar ta jaddada cikakken goyon bayanta ga zaman lafiyar kasar Sudan da kuma yankinta a jiya Laraba, tare da tabbatar da hadin kan matsayar kasashen biyu da kuma kin amincewa da matakan bangare daya...
    Rundunar ta kuma bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 11:15 na safe, wata tawagar rundunar ta kama wasu mutane biyu a filin tirela na Dangauro. Sanarwar ta kara da cewa, “An samu wadanda ake zargin dauke da buhu bakwai da ake zargin kayan maye ne wanda aka fi sani...
    Ganau sun ƙara da cewa a lokacin da aka shaida wa matar cewa Yelwa ba ta nan, sai ta koma mashigar gidan ta kwarara wa kanta man fetur tare cinna ashana wanda hakan ya janyo wuta ta tashi.   Nan take lamarin ya janyo hankalin mutanen da suke kusa da wurin inda suka yi ƙoƙarin...
    Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da farmakin da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan jiragen ruwan ‘yan fafatuka dake dauke da kayan agaji ga al’ummar Gaza. Kungiyoyin Falasdinawa, kwararru na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin Turai sun bi sahu inda sukayi tir da harin baya bayan nan da aka...
    Kasar Colombia ta kori jami’an diflomasiyyar gwamnatin Isra’ila sakamakon harin da Tel Aviv ta kai kan wani jirgin ruwan agaji na kasa da kasa da ke daura da Gaza, yayin da ta bukaci daure shugaban Amurka a gidan yari saboda hadin kan gwamnatin kasar a aiwatar da kisan kare dangi na Isra’ila a zirin Gaza....
    Akalla Falasdinawa 44 ne sukayi shahada a yayin da wasu da dama suka jikkata a ranar Laraba a wasu jerin hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, a cewar shaidu da majiyoyin lafiya. Sojojin Isra’ila sun yi luguden wuta kan wasu gidaje a sansanin ‘yan gudun hijira na Shati da ke...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan bukatar hakan ta taso, zai iya janye burinsa na takarar shugaban kasa a 2027 don mara wa matashi baya. Atiku, wanda jigo ne a haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC, ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da BBC Hausa a ranar Laraba. NAPTIP ta kama mahaifin...
    Iran ta yi kira da a gaggauta kakaba wa gwamnatin Isra’ila takunkumi mai tsauri kan kisan kiyashin da take ci gaba da yi a zirin Gaza, sakamakon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan. Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya karo na 60...
    Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ce ta kama akalla mutane biyar da ake zargi da safarar mutane tare da ceto mutane 24 a Filin Jirgin Sama na Ƙasa Nnamdi Azikiwe, Abuja. Hukumar ta ce daga cikin wadanda aka cafke ɗin, har da wani uba da ya yi ƙoƙarin safarar diyarsa zuwa...
    Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce zai kori dukkanin jami’an diflomasiyar Isra’ila daga ƙasarsa a matsayin martani ga kama jiragen ruwa masu ɗauke da agaji zuwa Gaza. Ya kuma ya bayyana cewa an yi garkuwa da yan Colombia guda biyu. Petro babban mai caccakar yaƙin Isra’ila a Gaza, ya zargi Isra’ila da sake saɓa dokokin...
    Kungiyoyin Kare Muradun Arewa, wato Arewa Defence League, sun fitar da sanarwar da suka kira October Declaration, wadda ta tanadi matakai na gaggawa don magance matsalolin tsaro, koma bayan tattalin arziki da kalubalen rayuwa a Arewacin Najeriya. Shugaban kungiyar, Murtala Abubakar, ya bayyana hakan a taron dabarun da aka gudanar a Arewa House Kaduna, inda...