Fitattun dalibai akalla 12 ne  daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare  a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF).

A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa.

Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu.

A cewarsa, an zabo daliban 12 ne  sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar.

Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya kunshi dukkan kuɗin da ake buƙata a karatun sakandaren daliban.

“Muna kira da jama’a su ba da gudummawa da kuma ɗaukar nauyin ɗalibai. Kada a bar wannan aiki ga gwamnati da iyaye kadai. Ilimantar da ‘ya’yanmu hakki ne da ya rataya a kanmu gaba ɗaya,” in ji Gwamna.

Ya yaba da tsarin zaɓen kuma ya taya waɗanda suka yi nasara murna.

A nata jawabin, Babbar Shugabar Kwara ETF, Oluwadamilola Amolegbe, ta ce daliban 12 sun fito ne daga cikin jerin ɗalibai 640 da aka fara tantancewa bisa cancanta.

Ta bayyana cewa tsarin zaɓen ya fara ne da rubuta jarabawa ga dukkan daliban firamare na aji shida da suka amfana da shirin KwaraLEARN na koyon fasahar zamani, har zuwa lokacin da aka kammala tantancewa.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kwara ETF

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai

Gwamnatin Jihar Yobe ta ƙaddamar da shirin fara amfani da ma’adinan ƙarƙashin ƙasa da Allah SWT ya hore ma ta da nufin haɓaka tattalin arzikinta tare da samarwa al’umma aikin yi.

A yayin ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na Jihar da aka yi a babban ɗakin taron gidan gwamnatin Jihar da ke Damaturu, Gwamnan Jihar Mai Mala Buni ya ce kamfanin haɓaka ma’adanai ta Yobe Limited ita ce kawai hukumar da aka bai wa izini don gudanar da duk ayyukan bincike da haƙar ma’adinai a faɗin jihar.

Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA

Yana mai cewa, kamfanin haƙar ma’adinai na Yobe a halin yanzu shi ne, ƙashin bayan da zai samarwa Jihar hanyoyin dogaro.

“Jihar Yobe tana da wadataccen albarkatun ma’adinai kamar: Limestone, gypsum, kaolin, granite, Quartz, silica da sauran su duk da haka, tsawon shekaru da yawa, waɗannan ma’adinai sun kasance ba a amfani da su sosai kuma a yanzu lokaci ya yi da za a mayar da waɗannan ma’adinai da aka ɓoye zuwa kadarorin da za su samar da ayyukan yi, samar da wadata da kuma ciyar da ci gaban zamantakewa da tattalin arziki na mutanenmu gaba ɗaya.”

“Manufarmu ita ce tsara wani tsari don ci gaban fannin haƙar ma’adinai a Jihar Yobe ta hanyar da ta dace da manufofin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da haɗa kan al’umma, jawo hankalin masu zuba jari masu aminci da kuma tabbatar da alhakin gyara muhalli.

“kuma mun yi imanin cewa haƙar ma’adinai idan aka sarrafa shi yadda ya kamata, zai iya zama babban abin da ke haifar da juriyar tattalin arzikin jiharmu, samar da aikin yi ga matasa da kuma samar da kuɗaɗen shiga.”

“Muna hasashen samar da fannin haƙar ma’adinai wanda zai iya aiki a cikin tsarin dokoki, wanda ke tabbatar da ɗorewar muhalli da fa’idar al’umma; wanda ke haɗaka da haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu waɗanda aka amince da riƙon amana; wanda ke jawo hankalin masu zuba jari na ƙasashen waje.” Cewar Gwamna Buni.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara 
  • Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
  • Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai