Kungiyar Miyetti Allah Ta Musanta Zargin Boye Makamai A Cikin Garken Shanu
Published: 7th, October 2025 GMT
Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen jihar Kwara ta yi watsi da zargin cewa mambobinta na boye makamai a cikin shanunsu domin gujewa jami’an tsaro.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Shehu Garba ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a Ilorin.
Ya ce Hausa Fulani da Bororo a jihar su ne masu bin doka da oda kuma ba su da wani laifi a kan haka.
Shugaban na MACBAN ya yi zargin cewa mayar da tsohon Sarkin Fulanin Igangan da ke Oyo, Alhaji Saliu Abdulkadir zuwa jihar Kwara a shekarar 2021, da kuma sauran makiyayan da suka yi tashe-tashen hankula ne suka haddasa matsalar tsaro a jihar.
Alhaji Garba ya bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su sanya ido kan ayyukan tsohon Sarkin Fulanin Igangan da sauran masu ci-rani don hana kwatankwacin abin da ya faru a Oyo a Kwara.
Shugaban kungiyar ta MACBAN ya tabbatar wa gwamnatin jihar kan kudirinsu na bayar da gudunmuwar domin rage matsalolin tsaro a jihar zuwa mafi karanci.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Miyetti Allah Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
Daga Isma’il Adamu
Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar.
Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa da kasafin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da shi yadda ya dace.
Ya bayyana cewa kashi 82 cikin ɗari na kasafin an ware shi ne ga manyon ayyuka(capital expenditure), yayin da kashi 18 cikin ɗari aka ware ga ayyukan yau da kullum(recurrent expenditure), rabo wanda ya ce ya fi abin da doka ta baya ta tanada, wadda ke bukatar kada kudaden gudanarwa su haura kashi 30 cikin ɗari.
Gwamna Radda, wanda ya bayyana kasafin a matsayin “kasafin jama’a,” ya ce an tsara shi ne daga shawarwarin da aka tattara a tarukan jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a fadin kananan hukumomi 34 na jihar.
Yayin da yake jinjinawa ‘yan majalisar dokokin jihar bisa kyakkyawar alakar aiki da suke da ita da bangaren zartarwa, gwamnan ya bukaci kwamitocin majalisar su gudanar da aikinsu na sa ido don tabbatar da cewa an aiwatar da kasafin yadda ya kamata.
Tun da farko, yayin mika kudirin kasafin domin rattaba hannu, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Nasir Yahaya, ya ce ‘yan majalisar sun duba tare da amince da kasafin cikin makonni uku, lamarin da ya sanya Katsina ta zama jihar farko da ta samu dokar kasafin kudin shekara ta 2026.