’Yan bindiga sun kashe wani mutum sun sace hakimi a Kwara
Published: 6th, October 2025 GMT
Ana tsaka da Sallah ’yan bindiga suka karbe wani mutum har lahira sa’annan suka yi garkuwa da basarake a ƙauyen Rani Ramat da ke Ƙaramar Hukumar Patigi a Jihar Kwara.
Al’ummar yankin sun ce maharan sun kai farmaki ne a kan babura a yayin da ake Sallar Magariba ranar Lahadi inda suka rika harbi babu ƙaƙƙautawa.
A yayin da jama’a ke guje-gujen neman tsira ne ’yan bindigar suka harbe wani mutum. Daga nan suka yi awon gaba da basaraken ƙauyen mai suna Alhaji Ndako, zuwa inda ba a sani ba.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka kafin su koma cikin daji.
Kwamitin gwamnati ya ba da shawarar ƙirƙirar sababbin masarautu 13 a Bauchi NAJERIYA A YAU: ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’Shugaban Ƙaramar Hukumar Patigi, Ahmed Rufai, ya tabbatar da harin, tare da cewa mafarauta da ’yan banga sun bi sawun maharan domin ceto basaraken.
Ya bayyana cewa ƙaramar hukumar da hadin gwiwar gwamnatin jihar da jami’an tsaro na aiki tare da ’yan banga a ƙoƙarinsu na magance matsalar rashin tsaro a yankin.
Ya jaddada buƙatar fatattakar ɓata-garin daga dazukan yankin yana mai bayyana kyakkyawan fata cewa shirin gwamnatin jihar na ɗaukar jami’an tsaron dazuka da samar musu kayan aiki zai taimaka wajen shawo kan matsalar.
Wannan na zuwa ne a yayin da gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRahman, ya yi zama da masu ruwa da tsaki na ƙananan hukumomin Patigi da Edu, da nufin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga basarake Kwara matsalar tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata (AGILE) a yankin.
Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo.
Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na bukatar gyara.
Shirin AGILE, wani shiri ne na Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Jigawa, wanda aka ƙirƙira domin bai wa matasa mata ƙwarewar da za su dogara da kansu, inda ake sa ran mutum 50 za su amfana a horon da ke tafe.
A lokacin ƙaddamar da aikin, Mai kula da shirin AGILE a Birnin Kudu, Hajiya Maryam Hassan Jibrin, ta yaba da jajircewar Dr. Builder Uba ga ci gaban al’umma, tana jinjinawa kokarinsa tare da yi masa addu’ar ci gaba da jagoranci mai tasiri.
Da yake tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen ci gaban matasa, Muhammad Uba ya yi alƙawarin bayar da gagarumin tallafi ga mahalarta bayan kammala shirin cikin nasara.