Gwamnan Jihar Kwara Ya Hori Sabbin Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima Akan Kishin Kasa
Published: 4th, August 2025 GMT
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bukaci sabbin mambobin hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) da aka rantsar da su kasance masu kishin kasa da kuma ci gaba da zama ’yan kasa nagari.
Gwamna AbdulRazaq ya bayyana haka ne a yayin bikin rantsar da rukunin ‘B’, a sansanin NYSC dake Yikpata a karamar hukumar Edu.
Ya kuma shawarce su da su yi taka tsantsan wajen gudanar da ayyuka daban-daban na kwas din.
Gwamna AbdulRazaq ya tabbatar wa ‘yan yiwa kasa hidimar cewa gwamnatin jihar za ta samar da yanayin da zai taimaka musu su ci gaba.
A nasa jawabin, kodinetan NYSC na jihar, Mista Onifade Joshua, ya yabawa gwamna AbdulRazaq bisa goyon bayan da yake baiwa NYSC a jihar Kwara.
An rantsar da jimillar mambobin 1,600 da suka kunshi maza 700 da mata 900 a sansanin Yikpata.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.