‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗansanda Da Wata Mata, Sun Yi Darkuwa Da Mutum 6 A Kwara
Published: 25th, September 2025 GMT
Ta kuma tabbatar da yin garkuwa da mutane shida a yankunan biyu, inda ta kara da cewa wasu shida sun samu raunuka a harbin bindiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar.
Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani.
Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin GamuwarsuA cewar sanarwar NPFL, an ci tarar Katsina United Naira miliyan ɗaya bisa laifuka uku: jefa abubuwa cikin fili, rashin tsawatarwa magoya baya, da haddasa hargitsi a wasa. Haka kuma, ƙungiyar za ta biya Naira miliyan biyu saboda gazawa wajen samar da isasshen tsaro, tare da ɗaukar nauyin gyaran motocin Barau FC da aka lalata.
Jimillar tarar da Katsina United za ta biya ta kai Naira miliyan tara (₦9m), tare da umarni daga NPFL cewa duk sauran wasanninta na gida a kakar bana za ta buga su a garin Jos, jihar Filato. Hukumar ta kuma bai wa ƙungiyar awa 48 ta ɗaukaka ƙara idan bata gamsu da hukuncin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA