Kwara ta bukaci a sanya ido sosai, yayin da jami’an tsaro ke kara kai hare-hare a maboyar masu garkuwa da mutane
Published: 2nd, October 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kogi da Kwara, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su.
“Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita zirga-zirgar ababen da suka dace kawai, wato don gudun kada a kama su ba tare da saninsu ba, yayin da masu garkuwa da mutane ke tserewa maboyarsu, ba ma son abin ya shafa masu bin doka da oda.
A cewarta gwamnatin ta yi nadamar matsalolin wucin gadi da takaita zirga-zirgar ka iya haifarwa a yankunan da ke kusa.
Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa sabon kokarin da suke na fatattakar ‘yan ta’addan, tare da gurfanar da su a gaban kuliya har sai an kawar da su gaba daya, kuma a fitar da su daga dazuzzuka.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana
Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana.
A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana.
Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a BornoHakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe a FIFA Club World Cup da Chelsea ta lashe a Amurka.
Shi kuwa Mohammed Salah ya taka rawar gani a Liverpool a kakar da ta wuce da lashe Premier League, kuma shi ne kan gaba a zazzaga kwallaye mai 29 da bayar da 18 aka zura a raga, hakan ya sa ya karbi kyautar takalmin zinare, wato Golden Boot.
Mohammed Salah dan ƙasar Masar mai shekara 33 na fatan karbar kyautar gwarzon Afirka karo na uku bayan 2017 da kuma 2018.
Shi kuwa dan ƙwallon tawagar Super Eagles ta Najeriya, Victor Osimhen ya jagoranci Galatasaray ta dauki babban kofin tamaula na Turkiya da cin ƙwallo 26.
Osimhen ya taba zama gwarzon Afirka 2023 a lokacin da shi kuma Hakimi ya yi na biyu
To sai dai mai riƙe da kyautar a yanzu, wato Ademola Lookman na Nijeriya, bai kai bante ba a kakar nan sakamakon gaza taka rawar gani yadda ake buƙata.
Za a gudanar da bikin karrama gwarzon dan ƙwallon ƙafa na Afirka na bana ranar Laraba a birnin Rabat na Morocco.