Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Asibitin Dabbobi A Jihar Kwara
Published: 15th, August 2025 GMT
Ministan Ma’aikatar Kula da Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabon asibitin dabbobi, da cibiyar ajiye dabbobi, tare da samar da allurar rigakafi a Jihar Kwara.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon nazarin taswirar fadin jihar(Geospatial Mapping) da aka gudanar a Ilori babban birnin Jihar Kwara.
Da yake wakiltar Ministan, Richard Mbaram ya bayyana wannan shiri a matsayin babbar nasara a tarihi wajen samo mafita ta dindindin ga rikicin manoma da makiyaya a ƙasar nan.
Ya ce aikin na daga cikin tsare-tsaren Shirin Sauya Hanyar Kiwo na Kasa (National Livestock Transformation Plan) na tsawon shekaru goma (2019-2028) wanda ya mayar da hankali kan gyara harkar kiwo a Najeriya.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ƙasa na L-Press, Dr. Sanusi Abubakar, ya yaba wa Jihar Kwara bisa zuba jari a bangaren ci gaban kiwo.
Ya yi alkawarin ci gaba da bai wa gwamnatin jihar goyon baya domin cimma sabon tsari a harkar kiwo.
Shi ma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda Mai ba shi Shawara na Musamman Alhaji Sa’adu Salahudeen, ya wakilta, ya yaba wa cibiyar cike ta Jami’ar Bayero Kano bisa jajircewa da ƙwarewar da suka nuna a duk tsawon aikin.
Ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta aiwatar da sakamakon binciken ba tare da kaucewa daga abin da aka gano ba.
Gwamna AbdulRazaq ya yi kira ga sarakuna, abokan hulda, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su hada hannu da gwamnati wajen aiwatar da shawarwarin da binciken ya bayar.
Tun da farko a jawabinsa, Darakta a Cibiyar Harkar Noma ta Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Sanusi Muhammed, ya bayyana cewa binciken ya samar da wani dandali mai inganci don tsara ayyuka, kai agaji, da ƙirƙirar manufofi a bangaren kiwo.
Farfesa Muhammed ya yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da bayanan taswirar wajen gyaran ruwan sha na dabbobi da ƙirƙirar tsarin samar da ruwa mai jure canjin yanayi.
ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara Jihar Kwara
এছাড়াও পড়ুন: