2025-11-09@14:18:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1263

«yarjejeniyar makamashin nukiliya»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da tsare tsare da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a hukumance, kamar yadda ofishin Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a yau Juma’a. Wannan dai na zuwa ne bayan ci gaba da tsaikon da aka samu  na tsawon kwana daya biyo bayan amincewar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu a ranar Alhamis. Duk da cewa an amince da matakin farko na yarjejeniyar, amma dai Isra’ila ba ta dakatar da hare-harenta a kan al’ummar yankin zirin Gaza, inda a cikin kasa da sa’oi 24 ta kashe Falastinawa akalla 70 da kuma jikkata wasu da dama a yankuna daban-daban na zirin Gaza. Tun da farko hukumar yada labaran Isra’ila ta bayar da...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan  damar. Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta ka’idojin yarjejeniyar, da kuma rungumar damar da tke cikinta.” Duk da cewa dai a  cikin kalaman nasa yafi nuna damuwa a kan fursunonin Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, duk da irin mummunan kisan kiyashi da Isra’ila take yi a Gaza, amma mya ce Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tsaf domin ba da cikakken goyon bayanta ga aiwatar da yarjejeniyar. A halin da...
    Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Nijeriya (NAEC) na 2025 a Legas ranar Alhamis. Ya koka da cewa, rashin gaskiya da rikon amana ne ya dabaibaye masana’antar mai da iskar gas, yana mai cewa akwai bukatar yin gaskiya da aiwatar da sabon tunani na fasaha wajen tafiyar da harkar mai da iskar gas a kasar. Orji ya lura cewa, kudaden da aka yi...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko October 8, 2025 Daga Birnin Sin Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan October 8, 2025 Daga Birnin Sin Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana October 8, 2025
    Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa, sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita Najeriya. Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Yusif Bashir da motar asibiti ƙirar Toyota Land Cruiser mai lambar ONG-0777, bayan ya shigo da ita ta iyakar Babura da Jamhuriyar Nijar. Tahir, ya ce tuni hukumar ta fara shirye-shiryen miƙa sh ga rundunar ’yan sandan jihar, domin ci...
    Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed.   Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta iya rayuwa a ware ba tare da yin hulda mai ma’ana da sauran kasashen duniya ba.   Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan raya kasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, wanda a cewarsa hakan zai karawa Bauchi damar karbar bakuncin taron kasa da kasa da kuma jawo hankalin masu zuba jari.   Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan...
    Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Sun ce za su gudanar da tattaki a cikin jami’o’i, tare da ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, sannan za su yi wa manema labarai jawabi domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu. Sun zargi gwamnati da rashin adalci wajen rabon Naira biliyan 50 na alawus-alawus, ƙin...
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama. Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa. “Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC A jawabinsa, Obasanjo ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed, bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, waɗanda ke inganta rayuwar jama’a. “Na yi farin ciki da abin da na gani da kuma abin da na ji. Ban zata cewa zan dawo Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci don buɗe irin wannan katafaren waje...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu. Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20. Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rabon gidaje 72 ga malamai da ma’aikatan lafiya a ƙaramar hukumar Mafa. Zulum ya ce Marbel ta shafe fiye da shekaru 24 tana aiki a cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke Mafa, kuma ba ta taɓa barin wurin ba ko...
    Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa. Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu...
    Haka kuma ya buƙaci a aiwatar da gyare-gyare don farfaɗo da tattalin arziƙi, inganta ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da damammaki ga matasa.Ya ƙara da cewa majalisar za ta sake duba Kundin Tsarin Mulki na 1999 domin bunƙasa dimokuraɗiyya da inganta mulki a Nijeriya.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025Manyan LabaraiTinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026 October 7, 2025
    Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa.   Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph na National Accord da kuri’u 9 a matsayin shugaban kungiyar.   Ya kuma bayyana cewa Mista Chris Nyamtu na gidan rediyon Najeriya ne ya yi nasara da kuri’u 21 yayin da Augustine Kuza na jaridar Pilot na Najeriya ya samu kuri’u 9 a matsayin Sakatare.   Mista Abel Daniel na jaridar Guardian a matsayin mataimakin shugaba Awayi Kuje na NAN a matsayin Mataimakin Sakatare, Michael...
    Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi ya ce, “Za a samu zaman lafiya na gaskiya a yankin Gabas ta Tsakiya ne kawai idan an kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa ka’idojin kasa da kasa da kuma hanyar da za ta maido da hakkokin masu hakki.” A jawabin da ya yi na bikin cika shekaru 52 na nasarorin da larabawa suka samu a yakin watan Oktoban 1973, Sisi ya yi nuni da cewa, yin amfani da karfin tuwo  domin aiwatar manufa ne ke haifar da tashin hankali, yayin da zaman lafiya da aka gina bisa adalci yana samar da daidaito na gaskiya da kuma dorewar zaman tare a tsakanin al’ummomi.” Ya yi nuni da cewa, tsagaita bude wuta, musayar...
    Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tana aiki don ƙirƙirar yanayi mai sauƙin zuba jari, da zaman lafiya don masana’antu, da haɓaka tattalin arziki mai dorewa. A ƙarshe, ya kira masu ruwa da tsaki da su fifita tattaunawa a wajen neman mafita maimakon rikici, yana cewa, “Nijeriya ƙasa ce mai girma da ke neman mafita a abubuwa da yawa, ya zama dole ne mu haɗa kai wajen kare abin da ke amfanar ƙasa baki ɗaya.” Tags: Aliko DangoteShettima ShareTweetSendShare Abubakar Sulaiman Related Manyan Labarai Talaucin Da Ya Ninku Fiye Da Sau Biyu A Gwamnatin Tinubu, An Ƙuduri Aniyar Kawar Da Shi Nan Da Shekaru 5 4 hours ago Manyan Labarai Uba Sani Ya Amince...
    A cewar Bankin Duniya, talauci a tsakanin mazauna karkarar Nijeriya ya kai kashi 75.5 cikin dari, wanda ke nuna ƙaruwar rashin daidaito da kuma tsananin matsin tattalin arziki a fadin kasar.   Ministan ya ce, gwamnati ta kuma kuduri aniyar inganta hasashen tattalin arziki da inganta sauye-sauyen da zai sanya Nijeriya ta samu ci gaba mai ɗorewa.   Bagudu ya jaddada cewa, gwamnatin da shugaban kasa Bola Tinubu ke jagoranta tana ba da fifiko wajen samar da ayyukan yi ta fuskar fasahar zamani, noma, tattalin arziki da ƙirƙire-ƙirƙire. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
      Sanarwar ta ce, hare-haren kakkaɓe maɓoyar ‘yan bindigar na zuwa ne a karkashin shirin ‘Operation Lafiya Nakowa’, da nufin fatattakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar Taraba.   Ya kara da cewa, harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan a kusa da Tarhembe, Tornyi, TY Farm, da ɗaukacin yankin Kando da ke yankin Tati, karamar hukumar Takum, da kuma rahotannin lalata gonaki a karamar hukumar Ussa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A karon farko a tarihin kwallon raga ta mata ta Iran ta zami lashe kofin zakarun Asiya, bayan samun galaba akan kawarta ta kasar Uzbakestan. An fara wasan fidda gwani a tsakanin kungiyoyin kwallon raga na mata na Asiya a ranar 2 ga watan nan na Oktoba, a birnin Tashqand wanda ya zo karshe a yau Lahadi da samun galabar Iran. Tun da fari kungiyar kwallon ragar ta Iran ta sami nasarori har sau uku a jere, da a karshe ta kai ga samun nasara akan mai masaukin baki kasar Uzbakestan. Mai bayar da horo ga ‘yan wasan Li Du Hi, ta bayyana jin dadinsa da nasarar da su ka samu, musamman saboda wannan ne karon farko aka sami wannan...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Allah Ya yi wa fitaccen ɗan jarida a Jihar Kano Aliyu Abubakar Getso, rasuwa da safiyar yau Lahadi bayan fama da rashin lafiya. Abubakar Getso ya yi aiki a kafafen yaɗa labarai da dama da suka haɗar da na gwamnati da kuma masu zaman kansu. Ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya da jikoki da dama. Iyalai sun ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 9:30 na safiyar yau Lahadi a gidansa da ke Second Gate a Unguwar Janbulo, Kabuga.
    BICTOR IKPEBA – 1997 Dan wasan Nijeriya Bictor Ikpeba, ne da ake yi wa lakabi da suna “Prince of Monaco,” Ikpeba ya samu shiga ne bayan ya taimaka wa kungiyar Monaco ta samu nasarar lashe kofin Ligue 1 ta Faransa. Danwasan ya samu kuri’a 2, inda ya kare a mataki na 32 a cikin jerin wadanda suka samu karramawa a shekarar ta 1997. ADEMOLA LOOKMAN – 2024 A kakar bara, wanda ya lashe gwarzon dan kwallon kafa na Afirka, Ademola Lukman, wanda a lokacin yake buga wasa a kungiyar Atalanta ne ya zo na 14 a bikin karramawar. Lookman ya lashe gasar Europa da Atalanta, inda ya zura kwallo uku rigis a raga, sannan ya taka rawar gani sosai a...
    Hukumar sararin samaniya ta kasar Iran ta bada sanarwan shirin cilla tauraron dan’adam a cibiyar cilla taurarin dan’adam na Chabahar tare da amfani da sandarerren makamashi. Kamfanin ndillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban hukumar Hassan Salarieh yana fadar haka a yau Asabar ya kuma kara da cewa, an kammala bangare na farko na cibiyar cilla taurarin yan’adam na Chabahar kuma hukumar ta fara shirin amfani da sandarerren makamashi don cillan taurarin yan’adam da suke gabanta, wadanda a shirye suke a cillasu. Salarieh y ace a halin yanzu akwai tauraron dan Adam mai suna Pars-2 da ke jiran  cillawa, sannan hukumar zata ci gaba da aiki a bangare na 2 na cibiyar don kammala aikin cibiyar cilla tararin...
    Da farko za ki wanke tsamiya sai ki dafa ta ki tace sannan ki wanke danyar citta sai ki nika ta, sannan ki samu roba mai kyau sai ki tace tsamiya tare da cittar kisa suga da filebo sai ki juya sosai ki sa a firij ko ki sa masa kankara. Asha dadi lafiya. Hadadden Lemon Shayi: Abubuwan da uwargida za ki tanada: Kankana, kokumba, sitoru beri na ruwa, lemo, tea bag, danyar citta, abarba, Lemon juice, na’a na’a. Yadda zaki hada: Da farko za ki wanke kankana da danyar citta sai ki nika su, sannan ki tace ki zuba a cikin tukunya, sai ki dora akan wuta ki wanke abarba da kokumba, ki yanka ki zuba a cikin tukunya...
    Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya yayi tsokaci kan martanin kungiyar Hamas kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana jin dadinsa da martanin da kungiyar Hamas ta mayar dangane  shirin shugaban Amurka Donald Trump kan Gaza, yana mai bayyana hakan a matsayin abin karfafa gwiwa. Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a cikin wata sanarwa a yau Asabar cewa: Guterres ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su yi amfani da wannan damar wajen kawo karshen yakin Gaza da kuma kawo karshen bala’in jin kai da fararen hula ke fuskanta. Ya kara da cewa, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya tabbatar da shirin Majalisar Dinkin Duniya na goyon bayan duk...
    Mista Fall ya jagoranci tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta kunshi wakilai daga UNICEF, UNESCO, UNDP, UNFPA, da mata na Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron. Ya jaddada cewa canjin al’umma ya ta’allaka ne akan jarin dan’Adam musamman ta hanyar ilmantar da ‘ya’ya mata da karfafa wa mata.   Ya kara da cewa, “tare da gwamnati da abokan huldarmu, mun himmatu wajen kawar da duk wani cikas da ke hana yara, musamman ma masu rauni damar samun ilimi”.   Fall ya gano muhimman abubuwan da ke kawo cikas ga ilimi a Nijeriya, da suka hada da rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, sauyin yanayi, da kuma ka’idojin zamantakewa da al’adu. Ya yi kira da a kara himma wajen inganta daidaiton jinsi...
    Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da yanayin ruwa da kasar da ke cikinsu ya kai kashi 73 cikin dari. Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, a yayin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, an kiyaye kyautata yanayin zaizayewar kasa a kasar Sin, kuma an cimma burin rage fadin gonakin da suka gamu da matsalar, da kuma rage illar da ruwa da iska suka haddasa wa gonaki....
    Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance. “Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00 a matsayin alawus-alawus na daliban. Idan aka tattara kudaden baki-daya, jimillarsu ta kama Naira 99,553,077,293.00,” a cewar rahoton. Duk da nasarar da aka samu a fadin kasar, shirin ya fuskanci kalubale wajen ganin an yi adalci a rabon a dukkanin shiyoyin fadin kasar guda shida da ake da su. Alkaluman da LEADERSHIP ta tattara a watan Mayun 2025, sun nuna dimbin gibin da ke tsakanin...
    Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Juma’a, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, reshen jihar, Bashir Mu’azu, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne. “Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar gas ɗin girki. Binciken farko ya nuna cewa daliba ce ta bar girki ba tare da kulawa ba,” in ji Muazu. Sai dai ya bayyana cewa babu...
    Ita dai wannan yarjeniyar wadda wanda mamallakin karamin Jirgin Sama, zai bayar da hayar Jirginsa na Sama, ba tare da ma’aikata da kula da Jirgin da kuma yin inshore ba. Akasarin wannan yarjeniyar ana yinta da takardar shedar mamallakan Jiragen Samn wato AOC. “Hakan ya nuna cewa, mun fara shiga cikin matakin fafada harkar kasuwanci mai zaman kansa ne kuma za mu yi hakan a bangaren Kamafnin Jirgin Sama na Air Peace ba ne, sai dai kawai, a bangaren sauran Jiragen Sama,” A cewar Manajin Darakantan. A shekarar 2024 ne dai, aka cire Nijeriya daga cikin jeren kasasshen da suka yi kaurin suna wajen saba yarjeniyar, ta bayar da hayar Jirgin Sama. Kazalika, hakan ya biyo bayan kiyaye daukacin ka’idojin...
    Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke Zariya.   Da yake jawabi, shugaban gidauniyar Malala, Mista Ziouddin Yousafzai ya yaba da kyakkyawar tarba da aka yi masa tare da tawagarsa, inda ya bayyana Masarautar Zazzau a matsayin babbar abokiyar tarayya wajen ciyar da manufofin Gidauniyar gaba.   Ya yi alkawarin karfafa hadin gwiwa da cibiyoyin gargajiya domin bunkasa samun ilimi da karfafawa ‘ya’ya mata samun damar da suke da ita.   A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yabawa gidauniyar Malala bisa ci gaba da tallafawa wajen inganta ilimin yara mata, musamman a Arewacin Najeriya.   Sarkin ya yi...
    Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda daya daga cikin shuwagabannin ‘yan bindigar ya yi bazaranar shedawa gwamnati da sauran jami’an gwamnatin da suka halarci wajen kulla sulhun cewa, idan har gwamnati ta kuskura ta kashe ‘yan bindiga dubu goma, suma za su hallaka adadin mutane kamar hakan. Wasu ‘yan Nijeriya dai, sun yi ittifakin cewa, kasar nan, ta koma tamkar, a hanun tafin ‘yan bindigar. Kulla wannan yarjeniyra dai, ta nuna...
      Mazauna unguwar Sabon Gero, dake bayan Millennium City a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta kammala aikin gyaran titin unguwar, wanda suka ce an bar shi a cikin mawuyacin hali duk da cewa an bai wa wani kamfani aikin kusan shekara guda da ta gabata.   Mazauna yankin sun bayyana cewa halin da hanyar take ciki ya jefa su cikin matsanancin rayuwa, musamman mata masu juna biyu da ke tilasta musu hawa babura domin neman kulawa a wajen unguwar, kasancewar babu asibiti a yankin.   Ɗaya daga cikin mazauna, Rashida Shehu, wadda ke da juna biyu, ta ce ta ji rauni a lokacin da take kokarin bin hanyar zuwa gari domin kula...
    Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman.   A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kogi da Kwara, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su.   “Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita zirga-zirgar ababen da suka dace kawai, wato don gudun kada a kama su ba tare da saninsu ba, yayin da masu garkuwa da mutane ke tserewa maboyarsu, ba...
    Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya jaddada ƙudirinsa na yin aiki tare da Gidauniyar Malala a ƙoƙarinta na ci gaba da bunƙasa ilimi da magance ƙalubalen da ke hana miliyoyin yara, musamman ’yan mata rashin zuwa makaranta. Da yake yi wa Malala Yousafzai  maraba a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya, Babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai a ofishin Mohammed Malick Fall, ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya zata yi aiki tare da gidauniyar Malala, wacce ta samu kyautar lambar yabo ta Nobel. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi mat An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja “Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake jaddada goyon bayanta ga asusun Malala wajen ganin ‘ya’ya mata da yawa suna samun...
    Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas (PENGASSAN), ta dakatar da yajin aikin kwanaki uku da ta fara biyo bayan rikici tsakaninta da matatar Dangote. Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba. Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 26 a Kogi Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Ƙungiyar ta kuma gargaɗi matatar Dangote da kada ta kaeya yarjejeniyar da aka cimma a ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro. Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, wanda ya sanar da janye yajin aikin, ya ce idan matatar ta karya yarjejeniyar, ƙungiyar ba za ta yi shiru ba. Rikicin ya samo asali ne bayan...
    Ɓangarorin biyu sun tashi baran-baran a wata tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan ƙwadago na Nijeriya, Mohammed Dingyadi a ranar Litinin.   Wannan yajin aiki na PENGASSAN ya shafi rufe ɓangarori da dama na harkar mai a Nijeriya, ciki kuwa har da babban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, tare da dakatar da ba matatar Ɗangote ɗanyen mai.   Kungiyar ta PENGASSAN ta ja daga, inda ta bayyana cewa, “Muna kan bakar mu har yanzu, saboda mutanen mu da aka kora daga aiki, muna so dole a mayar da su.”   Wannan na zuwa ne a yayin da wata kotun Abuja ta bayar da umarnin hana yajin aikin ƙungiyar ta PENGASSAN da ɗaukar matakin hana kai wa matatar Ɗangote ɗanyen...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinjina wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira “juriya, haƙuri da ƙarfin halin da suke nunawa duk da matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro” da ƙasar ke fuskanta.  A cikin saƙonsa na taya ’yan Nijeriya murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai da ƙasar ta yi shekaru 65 da suka gabata, madugun adawar ya yi zargin cewa, gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da halin ƙaƙanikayi da ’yan ƙasar suka tsinci kansu a halin yanzu. A gaggauta binciko makasan ’yar jaridar Arise TV —Tinubu ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe Wazirin Adamawan ya bayyana damuwa kan yadda ’yan Najeriya ke rayuwa cikin ƙangin talauci, da yunwa, da rashin...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa  Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai bayyana cewa a matsayin babban rashi a ƙasar da kuma fagen aikin jarida. ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa, marigayiyar ta rasu ne bayan wani farmaki da ’yan fashi suka kai gidanta da ke Katampe a Abuja, a ranar Litinin da ta gabata. Tinubu...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Iran zata iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran a yau, kamar irin abubuwan da ta faru a baya, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali, da kuma cike da zaman lafiya, da abota, da zaman tare, da tattaunawa, kuma za ta iya sanya tausayi ya mamaye harshen bai daya ta hanyar yin amfani da arzikin al’adu. A cikin sakon da ya gabatar a wurin taron karrama mawakan Iran Shams Tabrizi da Mawlana Jalaluddin Mohammad Balkhi, shugaba Pezeshkian ya ce a ranar Talata: An ambaci ranakun 29 da 30 ga watan...
    Tsohon Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Neja (SUBEB), Alhaji Alhassan Bawa Niworo, ya shiga hannun ’yan bindiga. An yi garkuwa da shi tare da wasu fasinjoji da dama a yammacin Litinin, 29 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 4 na yamma, tsakanin ƙauyukan Felegi da Ibi a kan hanyar Mokwa zuwa New Bussa a Ƙaramar Hukumar Borgu. Wata majiya ta ce Niworo tare da wasu ciki har da wani lauya, Barista Ahmad, na kan hanyarsu zuwa Minna ne lokacin da ’yan bindigar suka tare hanyar, suka kuma yi awon gaba da su cikin daji. Wasu daga cikin waɗanda aka sace ’yan kasuwa ne da suka fito daga kasuwar mako ta New Bussa. Abin da ya faru a zaman...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
    Shugabannin ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da wakilan Matatar Dangote na halartar wani taron gaggawa tare da wakilan Gwamnatin Tarayya. Shugaban ƙungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (TUC), Nuhu Toro, ne ke jagorantar ɓangaren ƙungiyoyin ƙwadago, yayin da Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Maigari Dingyadi da wasu jami’ai ke wakiltar Gwamnatin Tarayya. Ya zama tilas ɗalibai su gabatar da ‘Project’ kafin rajistar NYSC — Tinubu Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta gayyaci shugabannin PENGASSAN da na ɓangaren Matatar Dangote zuwa wannan taro sakamakon rikicin da ke tsakanin ɓangarorin biyu. Sai dai, duk da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana’antar raya al’adu ta kasar Sin, ta samu ci gaba bisa daidaito yayin shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, wanda aka gudanar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025. A cewar mataimakin ministan ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Lu Yingchuan, a shekarar 2024, darajar jimillar kadarorin sashen ta kai yuan tiriliyan 34.4, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.84. Lu wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin taron manema labarai, ya ce tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, Sin ta kuma cimma manyan nasarori a fannin bunkasa tasirin al’adunta. Ya ce a shekarar ta 2024, jimillar adadin cinikayya a fannin al’adu na Sin ya kai yuan tiriliyan 1.4, inda karin abubuwan sayayya a fannin da...
      Idan dai ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar, Abel Enitan, domin duba buƙatar ƙungiyar ASUU, a wani yunƙuri na tabbatar da ci gaban jami’o’in.   Sai dai har yanzu kwamitin bai fitar da wata sanarwa ko sakamakonsa ga jama’a ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano. Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin. ’Yan sanda sun kama kwayoyin N165.4m da makamai a Kano ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya Da yake ƙaddamar da shirin a Basawa, Zariya, shugaban FERMA na jihar Kaduna, Injiniya Kabir Iliyasu Danmarke, ya bayyana cewa aikin umurni ne daga shugaban hukumar na ƙasa, Dr. Chuku Emeka Obasi, bisa kudurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na rage haɗurra a hanyoyi. “Mun ɗauki...
    Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya, wato PENGASSAN, ta fara yajin aiki a faɗin Nijeriya daga daren Litinin, 29 ga Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan umarnin da shugabancin ƙungiyar ya bayar tun ranar Lahadi, inda aka umurci mambobi da su tsaida aiki a dukkan kamfanoni da cibiyoyi da hukumomin da suke aiki a su. A sakamakon haka, an kulle ƙofar shiga shalƙwatar hukumar NUPRC da ke Abuja, inda ɗaruruwan ma’aikata suka taru a waje ba tare da an bari sun shiga ba. Wannan mataki ya haddasa tsaiko a gudanar da ayyuka, musamman a sashen kula da harkokin mai da iskar gas na ƙasar. Rikicin Dangote Da PENGASSAN Ba Zai Kawo Wahalar Fetur Ba Majalisa Ta...
    Shekara guda matafiya da direbobi a ƙauyukan Malori-Guskuri da Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi na ci gaba da fama da wahala bayan da ruwan sama ya karya babban titin Kano–Maiduguri. A ranar 7 ga Agusta, 2024 ne ruwa ya cinye babbar hanyar a Malori-Guskuri, ya kuma yanke babban ɓangare na hanya. Mako guda bayan nan kuma wani ɓangaren ya rushe a Sabon Gari. Shekara guda da wata ɗaya bayan faruwar lamarin, wanda ya mayar wuraren da suka rushe sun koma tarkon mutuwa da ke haddasa haɗurra da suka kashe mutane da raunata wasu da dama. Wakilinmu da ya kai ziyara ya samu wani kamfanin gine-gine ya dawo Malori da kayan aikinsa. Mazauna sun tabbatar da...
    Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce adadin zirga-zirgar fasinjoji yayin hutun bikin tsakiyar kaka na Sin dake tafe nan da ‘yan kwanaki, zai kai kimanin biliyan 2.36. Da yake karin haske kan hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Lahadin nan, mataimakin ministan ma’aikatar Li Yang, ya ce yayin kwanaki takwas na hutun da za a fara tun daga ranar Laraba, za a samu karuwar tafiye-tafiye na yawon bude ido ko na ziyartar ‘yan uwa. Li, ya kara da cewa, an yi kiyasin ganin tafiye-tafiye kimanin miliyan 295 a duk rana cikin kwanakin hutun masu zuwa, karuwar da ta kai kaso 3.2 bisa dari kan na shekarar 2024 da ta shude. An kuma yi hasashen kaso...
    Sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga jihar Kano ta samu nasararta ta farko a gasar Firimiyar ta Nijeriya (NPFL) bayan doke Kun Khalifa daga jihar Imo a wasan mako na 5 da aka buga a birnin Aba. Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta samu nasara tun bayan haurowarta gasar. A minti na 14 da fara wasan ne Kun Khalifa suka fara zura ƙwallo a ragar Barau FC. Sai dai minti biyu kacal bayan haka, Yahaya Ibrahim ya farke wa Barau FC kwallo, wanda ya buɗe musu ƙofar dawowa cikin wasan. Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Ba za a yarda da ƙoƙarin maido da kudurori da suka ƙare ba kan Iran Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Yunkurin da kungiyar Tarayyar Turai Troika da Amurka ke yi na maido da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran, ba abu ne da za a amince da su ba. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da sanarwar mayar da martani ga ikirarin da kasashen Turai uku da Amurka suka yi na maido da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran. Ma’aikatar ta yi la’akari da yin amfani da hanyar warware takaddama da aka tanada a cikin yarjejeniyar hadin gwiwa game da...
    Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas ta Najeriya (PENGASSAN), ta fara yajin aiki saboda korar wasu ma’aikata a Matatar Mai ta Dangote da ke Jihar Legas. Sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya ce sun fara yajin aikin ne daga ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa ‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuros Riba Da misalin ƙarfe 6 na safe, mambobin ƙungiyar da ke aiki a ɗakunan kula da na’urori suka daina aiki. Umarnin ya shafi mambobin da ke ofisoshi, kamfanoni, da hukumomin gwamnati a faɗin Najeriya, waɗanda za su daina aiki da misalin ƙarfe 12:01 na daren ranar Litinin, 29 ga watan Satumba. Okugbawa,...
    Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki.   Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun ƙwararrun ma’aikata a bangarorin gine-gine, makamashi, fasahar zamani (ICT), kula da baƙi, da harkokin ƙirƙira. Muna da yakinin cewa waɗanda suka kammala karatu a wannan Cibiyar ba kawai za su samu ayyukan yi ba ne, har ma za su zama masu dogaro da kai kuma su samar da dama ga wasu.”   Shima Shugaban Cibiyar, Malam Husaini Haruna Muhammad, ya jaddada muhimmancin da horon ke...
    Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a Gombe HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Ya ce duk da cewa gwamnati ta amince da tsarin CONHESS na ma’aikatan lafiya, amma har yanzu ta kasa aiwatar da tsarin CONMESS na likitoci. A baya, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, amma ta dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi...
    Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a Gombe HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Ya ce duk da cewa gwamnati ta amince da tsarin CONHESS na ma’aikatan lafiya, amma har yanzu ta kasa aiwatar da tsarin CONMESS na likitoci. A baya, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, amma ta dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Rafael Grossi babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA a wata hira da yayi da gidan talbijin din Russia 24 ya bayyana cewa shirin nukiliya iran na zaman lafiya ne baki daya. Wannan maganar ta yi karo da kalaman prime minister isra’ila Benjamin Natanyaho  inda ya nuna cewa shirin nukiliyar Iran babban barazana ne,  don haka kalaman na shugaban IAEA sun tabbatar da ikirarin da iran ta dade tana yi na cewa shirin na zaman lafiya ne. Grossi ya fadi cewa ya amince hare-haren soji sa israila ta kai sun auna cibiyoyin nukiliyarta ta Fordo Natanza da kuma Isfahan inda ake ci gaba da inganta sinadarin yunariyum. Ya tabbatar da cewa iran ta tace yuraniyom kashi 60% ...
    Tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka bisa jagorancin Adam Smith ta kammala ziyara a kasar Sin a jiya Alhamis 25 ga wannan wata, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun maida hankali sosai kan batun. Kafin ziyarar tawagar, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun zanta ta wayar tarho, da yin musayar ra’ayoyi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da batutuwan da suke sa lura tare, kana sun tsara taswira kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kama a mataki na gaba. Bisa wannan yanayi, ziyarar tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka ta shaida muhimmiyar rawar manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara, da ci gaba da karfafa mu’amalar dake tsakanin...
    Jami’an ’yan sanda a Jihar Ondo sun kuɓutar da wata yarinya ’yar shekara huɗu da ta ɓace tare da gano wasu masu fataucin yara da ke gudanar da ayyukan su a yankunan Jihohin Ondo, Delta da Anambra. An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Sunday Kingsley da ke yankin Alagbaka Extension a garin Akure, ya ruwaito cewa ’yarsa Jesinta, ta ɓace ne a lokacin da take tare da mahaifiyarta Sunday Happiness. Gwamnatin Kebbi ta sake jaddada goyon bayanta ga hukumomin tsaro Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Olusola Ayanlade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka sanarwa manema labarai a Akure ranar...
    Kasashen Iran da Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar dala biliyan 25 don gina tashoshin makamashin nukiliya guda hudu a wani bangare na yarjejeniyar hadin gwiwa ta dogon lokaci da nufin karfafa alaka tsakanin Tehran da Moscow a fannoni daban-daban. An rattaba hannu kan yarjejeniyar zartarwa a birnin Moscow yau Juma’a tsakanin Kamfanin Hormoz na Iran da kamfanin Rosatom Project na kasar Rasha don ginawa da kuma kafa cibiyoyin samar da makamashin nukiliya na zamani hudu a garin Sirik da ke gabar teku a lardin Hormozgan na kudancin kasar. Babban aikin da za a gudanar a gundumar Kuhestak na yankin Sirik na lardin Hormozgan, zai iya samar da megawatts 5,020 daga makamashin nukiliya. An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne...
    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci birnin Ibadan, a yau Juma’a domin halartar bikin miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan, Oba Rashid Adewolu Ladoja na 44 da ake kan gudanarwa yanzu haka. Shugaba Tinubu da tawagarsa sun sauka a filin jiragen sama na Ladoke Akintola da ke Ibadan ne da misalin ƙarfe 1:30 PM na rana inda Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya yi masa maraba. Yadda ’yan haya za su samu ragin N500,000 a shekara  Babu wata jam’iyya dana ke shirin komawa — Kwankwaso Aminiya ta ruwaito cewa, tun kafin isowar Shugaba Tinubu aka fara gudanar da bukukuwan al’adun gargajiya da suka danganci miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan Oba Rashid Adewolu Ladoja. Juma’a a...
    Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya yi wani kakkausan gargadi game da halin da ake ciki na jin kai a Gaza, a daidai lokacin da Isra’ila ke yakin kisan kare dangi a can. A ranar Alhamis din nan, Lazzarini ya shaida wa manema labarai a wani taron manema labarai a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa, har yanzu yanayi a Gaza ba zai iya jurewa ba, yana mai bayyana halin da ake ciki a matsayin jahannama ta dukkan bangarorinta. “Ina ganin yana da mahimmanci ko da yaushe, kowace rana, mu tunatar da kanmu game da abin da ke faruwa a can, don kawai mu tabbatar da cewa ba mu fara...
    Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama, amma daga bisani aka sake shi bayan wasu dattawan unguwar sun sa baki. Matashi ya kashe kakanninsa saboda abinci a Kano An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Budurwar da abin ya faru da ita da ke koyon sana’a a wajen mutumin da ake zargi, ta ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 7 zuwa 8 na daren ranar Lahadi yayin da ake ruwan sama. A cewarta:...
    Daga nan sai ya jaddada aniyar Sin, ta ci gaba da goyon bayan matsayi da ikon MDD, tare da mara baya ga sassan kasa da kasa wajen cimma nasarar amfani da dandalin MDDr a matsayin fagen karfafa shawarwari da hadin gwiwa, da tsare-tsare da aiwatar da matakai yadda ya kamata.   Haka kuma, a yayin zantawarsa da shugabar taron MDD karo 80 Annalena Baerbock, a gefen babban taron muhawarar majalissar dake gudana a halin yanzu, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin na goyon bayan gina MDD mai karin inganci da hangen nesa, ta hanyar gudanar da sauye-sauyen kyautata karko da nagartar ayyukanta. Ya kuma bayyana kakkarfan goyon bayan Sin ga ikon MDD, da rawar da take takawa a...
    Bugu da kari, mahalarta bikin sun bayyana cewa, bikin ya nuna maimaituwar tarihin MDD na shekaru 80 da suka gabata, tare da yin kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, domin karfafa aniyar al’ummomin kasashen duniya ta kare zaman lafiya, da inganta fahimtar juna.   Haka kuma, Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG, ya shirya wani bikin kade-kaden fina-finai masu alaka da zaman lafiya, mai taken “Hadin kai a duniya, Muryar zaman lafiya”, a cibiyar fasaha ta Lincoln da ke birnin New York na kasar Amurka a daren ranar Talata.   Mataimakin sakantaren MDD mai kula da harkokin watsa labarai, Melissa Fleming, ta taya murnar bude bikin ta kafar bidiyo. Haka kuma, shugaban...
    An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11. Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku da suka tsere, na fuskantar tuhuma kan laifin aikata lalata, wanda ya saba wa sashi na 259 na kundin laifukan Jihar Kaduna na shekarar 2017. An ceto mutum 5 bayan gini ya rufta da su a Legas Gwamnatin Katsina ta kori ma’aikata da malaman makaranta na bogi 3,488 Ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Satumba wani mai suna Yahaya Aliyu, mazaunin Tudun Jukun...
    Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta sanya la’adar Dala 10,000, kwatankwacin Naira miliyan 15 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran. Ana dai neman Olumide ne a Amurka ruwa a jallo bisa zargin aikata laifukan zamba da dama. ’Yan bindiga sun harbi wani saboda rashin isassun kuɗi a asusunsa Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki A cewar sanarwa da aka wallafa a shafin FBI a ranar Laraba, ana tuhumar shi da laifukan zamba a banki, zamba da takardun shaida, laifukan da ake zargin ya aikata a jihar Illinois tun shekarar 2001. Adediran, mai shekaru 56, yana amfani da sunaye...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake fitar da Naira biliyan 5 domin biyan bashin ’yan fansho da haƙƙoƙin ma’aikatan da suka yi ritaya, lamarin da ya kawo adadin kuɗaɗen da gwamnatinsa ta biya zuwa yanzu ya kai Naira biliyan 27 tun bayan hawansa mulki. A wannan karon, kimanin tsofaffin ma’aikata 1,026 ne suka samu haƙƙoƙinsu waɗanda aka tsayar da biya tun a shekarar 2017. Komawar Natasha majalisa ya nuna haɗin kai zai iya yaƙar rashin adalci — Atiku Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa Aminiya ta ruwaito cewa, wannan wani yunƙuri na gwamnatin domin rage bashin Naira biliyan 48 na tsofaffin ma’aikata a matsayin haƙƙoƙin fansho da giratuti. Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da...
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya sanar da cewa: Masu binciken hukumarsa suna kan hanyarsu ta zuwa Iran Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran. Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran, amma shigarsu ta dogara ne da manufofin siyasar Iran. Ya ce: “Damar da suke da shi tana da kunci sosai, don haka tawagar hukumar IAEA tana da ‘yan sa’o’i kadan ko ‘yan kwanaki don sanin ko yarjejeniya da bangarorin biyu suka rattaba hannu a kai za...
      Gavi dai ba zai dawo ba sai a farkon shekarar 2026, shekarar da ake ganin kasar Sifaniya za ta kasance cikin kasashen da suka fi damar lashe gasar cin kofin duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da kuma Canada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
      Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.   Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin cikin gida (GDP), da karyewar hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ana samu a jere.   Tuni, dama masana suka yi hasashen cewa malejin tsadar rayuwa zai ƙara yin ƙasa sosai a sauran watannin ƙarshen 2025.   Haka kuma wani dalilin rage kuɗin ruwan shi ne domin a ci gaba da ƙarfafa tattalin arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...
    Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita. Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a...
    A jiya Lahadi ne dai jirgin ruwan agaji da aka bai wa sunan; ” Umar Mukhtar” ya bar ruwan kasar Libya  domin nufar Gaza da zummar karya killace yankin da aka yi na tsawon shekaru 18. Masu kula da jirgin ruwan na “Umar Mukhtar” sun bayyana cewa; Sun yi tanadin kayan aikin liktanci da aka bai wa sunan; Likitan Falasdinawa Husam Abu Saafiyyah. Har ila yau, hukumar agajin kasar Libya ta tanadi jirgin sama mai saukar angulu domin kai daukin gaggawa idan bukatar hakan ta taso. Da akwai mutane 20 a cikin wannan jirgin ruwan da su ka likitoci, masu fafutuka da kuma lauyoyi daga Libya da wasu kasashen turai. Jirgin ruwan na Agaji yana da cikakken goyon bayan al’ummar...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba suke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba, a yanzu suke zargin Iran da kin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliyar. A cikin wata hira da gidan talabijin na CCTV na kasar China, Pezeshkian ya ce, “Suna sa ran za a aiwatar da yarjejeniyar manyan tsare-tsare na shekaru 25 da aka tsara a baya tsakanin Iran da China.” Pezeshkian ya yi ishara da gazawar Amurka da kasashen Turai wajen cika alkawuran da suka dauka karkashin yarjejeniyar makamashin nukiliya, yana mai cewa, a yau kasashen da ba su...
    Ƙaramar Hukumar Sabuwa da ta Ɗandume a Jihar Katsina sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga, a wani yunƙuri na kawo ƙarshen hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen da suka daɗe suna addabar yankin. An gudanar da taron sulhun ne a ranar Asabar a ƙauyen Kabalawa Dungun Mua’zu, da ke iyaka da ƙananan hukumomin biyu, amma yana ƙarƙashin Sabuwa. Da wannan ci-gaban, adadin ƙananan hukumomi da suka ƙulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga a jihar ya kai tara. Sauran sun haɗa da Batsari da Kankara, Kurfi da Musawa da Ɗanmusa da Jibia da kuma Faskari. Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyu NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu Shugaban Ƙaramar...
    A daren ranar 19 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump sun tattauna ta wayar tarho, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, Sin da Amurka na iya cimma nasarar bai daya da wadata tare, ta yadda za su amfani kawunansu, da ma sauran sassan duniya baki daya. A nasa bangare kuwa, shugaba Trump cewa ya yi, alakar Amurka da Sin ita ce mafi muhimmancin dangantaka a duniya, yana mai cewa, aiki tare tsakanin kasashen biyu ka iya haifar da manyan abubuwa da za su ingiza zaman lafiya da daidaito a duniya. Ya yi fatan wanzar da babbar dangantaka mai armashi ta dogon lokaci tsakanin...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na ƙara bunƙasa tsaro da bayar da kyautar kayan aiki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a. ’Yan sanda sun kama mutane 5 kan zargin satar abincin yara a Borno Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Gwamna Inuwa ya ce: “Tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma. Ba za mu samu ci gaba, ba tare da zaman lafiya ba. “Gwamnatina za ta ci gaba da tallafa...
    A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa. Shugaban Kungiyar ta ACI Dakta Abdullahi Idris ya yi wannan Kira a wani taron manema labarai da Kungiyar ta Kira a Kaduna. Ya yi bayanin, Kungiyar ta lura da matakan da Gwamnati da Hukumomin tsaro suka dauka domin maido da zaman lafiya a wasu sassan Arewcin Kasar nan. Dakta Abdullahi Idris ya ce, matakan da aka dauka abin a yaba ne, Amma kuma sun yi kadan matuka...
    Rahotanni daga Islamabad sun nuna cewa gwamnatin kasar tana kwatanta yarjejeniyar tsaro da ta kulla da kasar Saudiya ,da irin wadda ke tsakanin dakarun tsaron kasashen turai da kuma kungiyar tsaro ta nato. Kasashen saudiya da Pakistan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakaninsu a wata ganawa da aka yi tsakanin prime minisata shehabaz sharif na Pakistan da takwaransa na kasar Saudiya Mohammad bn Salman a birnin Riyadh a ranar laraba da ta gabata inda suka kirata da yarjejeniya kan dabarun kasa, Musadik ya fadi cewa yarjejeniyar bata barazana ga kowa, kuma bata gayyaci wani ya kai wa kowa hari ba, amma kamar idan wata kasa dake cikin kungiyar kwance ta nato akai kai mata hari to kamar an kai...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50. Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa. “Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi. Sai dai har zuwa lokacin...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50. Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa. “Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi. Sai dai har zuwa lokacin...
    Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar. “Nijeriya za ta iya samun daloli masu yawa a kasuwar ta duniya”, a cewar Chuka Mordi Babban Jamie’s kamafanin Ellah Lakes kuma wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan ganin ana fitar da kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, domin yin hada- hadar kasuwancinsa. “Kashin dabbobin ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga, musamman wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani,...
    1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani da ita, zai iya kamuwa da cutar, ko kuma wani abu maikama da haka. 3- Ɓangaren saduwa a tsakanin ma’aurata- A wajen saduwa tsakanin mata da miji, ta hanyar haɗuwa maniyyi ko maziyyi da sauran makamantansu, wannan cuta za ta samu hanyar shigewa nan take da ɗaya daga cikinsu na ɗauke da ita. Don haka, waɗannan hanyoyi da aka ambata dukkanninsu na iya faruwa a...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce abin da ya faru shi ne wani jami’in tsaro da ke gadin wajen ne ya samu rauni a ƙafarsa ta hagu. A cewarsa, raunin ba shi da alaƙa da harbin bindiga, kamar yadda wasu shafukan Internet suka wallafa. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:45 na daren ranar...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari. Da zuwansa, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, tare da wasu suka tarbe shi. Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki Shugaba Tinubu ya gana da uwargidan marigayin, Aisha Buhari, da sauran ‘ya’yansa, inda ya sake yi musu ta’aziyya. Ya kuma tabbatar wa Aisha Buhari cewa zai ci gaba da kula da ayyukan alheri Buhari ya bari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona al’aurar ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
    Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona farjin ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
    Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro. Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi amfani da wuka da aka zafafata a wuta wajen ƙona jikinta. Ihun yarinyar ne ya jawo hankalin maƙwabta, inda suka yi gaggawar zuwa suka ceceta tare da sanar da ‘yansanda. Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Kabiru Mohammed Abdulkadir, ya...
    Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da sanyin safiyar Juma’a. Rahotanni sun ce yayin harin, maharan sun harbi wani jami’in ɗan sanda da ke gadin sakatariyar suka ji masa rauni ƙafa. An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza Lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda maharan suka buɗe wuta. Shugaban ƙungiyar NUJ reshen jihar, Rajab Ismail Mohammed, ya bayyana harin a matsayin abin tayar da hankali da kuma babbar barazana ga lafiyar ’yan jarida...
    Najeriya ta tabbatar da shirinta na karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila na 2030, inda za ta zama ƙasar Afirka ta farko da za ta kafa wannan tarihi tun 1930. Shugaba Bola Tinubu, ta bakin Shugaban Ma’aikatansa Femi Gbajabiamila, ya ce gwamnati ta ba da cikakken goyon baya, ta kuma shirya samar da dukkan abubuwan more rayuwa, tsaro da masauki kafin lokaci. A jawabansu daban daban, Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa Shehu Dikko da Shugaban Kungiyar Wasannin Renon Ingila Habu Gumel, sun bayyana cewa Najeriya ce damar Afirka mafi cancanta, yayin da kwamitin neman karɓar gasar ya gabatar da shirin gudanar da wasanni 15, ciki har da kwallon ƙafa. Najeriya da Indiya ne ke neman karɓar gasar, inda za a...
    Benfica ta sanar da naɗa José Mourinho a matsayin sabon kociyanta, domin maye gurbin Bruno Lage, wanda ƙungiyar ta karo bayan da Qarabag ta doke ta a gasar Zakarun Turai ranar Talata. Benfica ta kori Lage duk da cewa wasa ɗaya kawai ya yi rashin nasara a dukkanin gasa a bana. Wata sanarwa da Benfica ta fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa, Mourinho mai shekaru 62 zai jagoranci ƙungiyar har zuwa kakar wasanni ta 2026/2027, tare da zaɓin raba gari a ƙarshen kakar nan. An yanke wa Soja hukuncin kisa ta hanyar rataya Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar Tsohon kociyan Chelsea, Real Madrid da Manchester United, ya dawo Benfica ne bayan ya rasa aiki a...
    Wata babbar kotun sojin Najeriya da ke zamanta a sansanin sojoji ta Maxwell Khobe da ke garin Jos a Jihar Filato ta yanke wa wani soja mai suna Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya. An yanke wa Musa hukuncin kisa ne a ranar Alhamis bayan da aka same shi da laifuka biyu kan kisan gilla da aka yi wa wani direban babur mai ƙafa uku mai suna Abdulrahman Isa a garin Azare na Jihar Bauchi. Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu Daily Trust ta ruwaito cewa, an fara shari’ar Musa ne a farkon watan Agustan 2025 bayan kama shi biyo bayan binciken haɗin gwiwa da...
    A yau Alhamis ne ne aka kai wasu hare-hare biyu na suka da wuka akan mashigar ‘al-karamah’ dake kan iyakar Falasdinu da Jordan. Majiyar ‘yan sahayoniya wacce ta ambaci labarin ta kuma ce; A matakin farko an kai hari ne ta hanyar bude wuta da bindiga akan sojoji, sannan aka kai wani harin ta hanyar sara da wuka. Harin ya yi sanadiyyar kashe sojoji biyu da kuma jikkata wasu da dama. Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai,sojojin HKI su ka killace yankin baki daya domin yin bincike. A cikin watan Satumba an kai wani harin irin wannan wanda ya yi sanadiyyar halakar ‘yan sahayoniya 3 da kuma jikkata wasu da dama. Wannan harin na ‘yan gwagwarmaya ya zo...
    Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa lokacin da take kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga a ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Hakkin ya fito ne daga bakin Hakimin Bassa, Bagudu Amos, yayin wani taron tattaunawa da mata kan rikici da zaman lafiya mai taken: “Ƙarfafa Matakan Kare Fyade da Cin Zarafin Mata a Jihar Neja”. Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara Taron dai wata kungiya mai zaman kanta mai suna Tunani Initiative ce ta shira shi, tare da hadin gwiwar gidauniyar Dorothy Njemanze Foundation da kuma gidauniyar Foundation, domin ƙarfafa gwiwar mata wajen magance cin zarafin jinsi...
    Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun yi dafifi a Gidan Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbar shi da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bayan dawowarsu ofis. Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara na tsawon watanni shida a lokacin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a jihar. Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m Sai dai a ranar Laraba, Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci tare da umartar gwamnan, mataimakiyarsa da ’yan majalisar dokokin jihar da su koma bakin aiki daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba. A halin yanzu, tsohon shugaban riƙon ƙwarya na jihar, Rear Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya miƙa mulki...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido Wada ya jagoranta a Dutse babban birnin jihar.   Ya bayyana cewa, Rundunar za ta hada gwiwa da wadanda abin ya shafa domin fuskanatar kalubalen zirga-zirga don daukar matakin da ya dace.   A cewarsa, rundunar ta ci gaba da  shirye-shiryen ‘yan sanda da al’umma ke tafiyar da su ta hanyar samar da hadin gwiwa mai karfi da masu ruwa da tsaki da suka himmatu...