Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe
Published: 3rd, October 2025 GMT
Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku.
Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Juma’a, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, reshen jihar, Bashir Mu’azu, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne.
“Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar gas ɗin girki. Binciken farko ya nuna cewa daliba ce ta bar girki ba tare da kulawa ba,” in ji Muazu.
Sai dai ya bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa, sai dai an kai dalibai uku asibiti.
“Wasu an kwantar da su a asibiti saboda firgici, wasu kuma saboda shakar hayakin gobarar,” in ji shi.
Wakilinmu ya kuma gano cewa a kwanan nan ne jami’ar ta ɗage dokar hana amfani da tukunyar gas a cikin ɗakunan kwana daliban.
A baya dai da risho mai amfani da kananzir kawai hukumar ta amince dalibai su yin amfani da shi saboda fargabar hatsari.
Wasu daga cikin daliban da suka yi magana da wakilinmu da suka bukaci a boye sunayensu sun nuna rashin jin daɗi kan yadda aka tafiyar da lamarin, suna zargin rashin kayan aikin kashe gobara a cikin jami’ar.
“Da hukumar kashe gobara ta jami’a tana aiki yadda ya kamata, da gobarar ba ta yi muni haka ba,” in ji ɗaya daga cikin daliban.
Ƙoƙarin jin ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Jami’ar Gombe, Hadu Naphtali, ya ci tura, domin bai amsa kira ko saƙon kar-ta-kwanan da wakilnmu ya aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A halin yanzu, Kwamandan Hukumar Kashe Gobara a jihar, DCF S.M. Sulaiman, ya shawarci shugabannin jami’ar da su gaggauta dawo da dokar hana amfani da tukunyar gas a ɗakunan kwana don kauce wa afkuwar irin wannan iftila’in a nan gaba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara tukunyar gas
এছাড়াও পড়ুন:
An Yi Kira A Bai Wa ‘Yan Hijira Saboda Sauyin Muhalli
Kungiyar kasa da kasa mai kula da ‘yan hijira ( IOM) tana yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su bayar da kariya da kare hakkokin wadanda suke rayuwa a yankunan da suke fama da matsalar sauyin yanayi.
A taron da ake yi a yanzu haka a garin Belem na kasar Brazil kungiyoyi masu zama kansu dake fafutuka da rajin kare muhalli suna gabatar da shawarwari akan yadda za fuskacin matsalolin da duniya take fuskanta.
Kiran kungiyar ya ambato mutanen da sauyin yanayi ya tilasta musu yin hijira, ‘yan asalin kasa a cikin karkara da ‘yan gargajiya.
Ibtila’oin dabi’a irin su ambaliyar ruwa, zafi mai tsanani, fari da mahaukaciyar guguwa, suna tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu a kowace shekara. Da akwai da dama da ba su iya tsallake iyakokin kasashensu, suna ci gaba da zama a wasu yankuna nesa da gidajensu.
Kungiyar tana son ganin an taimakawa wadannan bangarorin na mutane a karkashin kare muhalli.
Masana suna bayyana cewa a nan gaba, za a sami wasu kasashen da za su nitse a karkashin tekuna da suke kara cikowa,ko kuma su zama wuraren da ba za za iya rayuwa a cikinsu ba.
Mataimakin Babbar darakta na kungiyar ( IOM), Ughoci Daniels ya bayyana cewa, samar da tsarin yin gargadin gaggawa, da ayyukan hidima a cikin yankunan da aka fi fuskantar hatsari, yana da matukar muhimmanci domin karfafa mutane su ci gaba da rayuwa a inda suke.
Daniels ya kuma ce; Da dama daga cikin wadanda su ka fice daga cikin muhallinsu saboda sauyin yanayi, suna fadin cewa sun fiifta komawa zuwa gidajensu. Sai dai kuma garuruwan nasu sun tashi daga yadda su ka san su a baya saboda sauyin yanaki. A dalilin haka, abinda ake da bukatuwa da shi, shi ne samar da abubuwan da za su karfafa su.”
A dalilin haka, Daniel ya yi fatan ganin taron da ake yi na kasar Brazil akan muhalli ya zama wanda zai daura dan Ba, a fagen samar da sauyi da kuma biyan asarar da aka samu saboda sauyin yanayin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Amince Da Sauye-sauye A Tsarin Mulkin Kasar Benin November 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon November 16, 2025 Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci