Bayan biyan N50m ma’aurata da ’yarsu su da aka yi garkuwa da su a Katsina
Published: 20th, September 2025 GMT
Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina.
Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50.
Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa.
“Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wani bayani da ya fito daga bakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina game da lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Garkuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Fubara ya sauka a filin jirgin saman Fatakwal
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya dawo bayan shafe tsawon lokaci baya jihar biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci da Shugaba Tinubu ya yi.
A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci, wadda tsohon Hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-Ekwe Ibas (rtd), ya jagoranta.
’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aikiMagoya bayan gwamnan sun taru a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal domin tarbarsa bayan dakatar da shi na tsawon watanni shida, amma daga baya suka watse bayan shafe lokaci suna jira ba tare da ganinsa ba.
Da safiyar ranar Juma’a, magoya bayan suka koma Filin Jirgin Sama na Fatakwal.
Jirgin da ya ɗauko gwamnan ya sauka a filin da misalin ƙarfe 12 na rana.
Ya gaisa da magoya bayansa a filin jirgin kafin daga bisani ya shiga mota tare da ayarinsa suka tafi.
Babu tabbacin cewar ko gidan gwamnati ya nufa kai-tsaye domin ci gaba da gudanar da harkokin mulki.