Aminiya:
2025-09-25@03:02:40 GMT

An sake raba Naira biliyan 5 haƙƙoƙin ’yan fansho a Kano

Published: 24th, September 2025 GMT

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake fitar da Naira biliyan 5 domin biyan bashin ’yan fansho da haƙƙoƙin ma’aikatan da suka yi ritaya, lamarin da ya kawo adadin kuɗaɗen da gwamnatinsa ta biya zuwa yanzu ya kai Naira biliyan 27 tun bayan hawansa mulki.

A wannan karon, kimanin tsofaffin ma’aikata 1,026 ne suka samu haƙƙoƙinsu waɗanda aka tsayar da biya tun a shekarar 2017.

Komawar Natasha majalisa ya nuna haɗin kai zai iya yaƙar rashin adalci — Atiku Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan wani yunƙuri na gwamnatin domin rage bashin Naira biliyan 48 na tsofaffin ma’aikata a matsayin haƙƙoƙin fansho da giratuti.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da biyan haƙƙokin kashi na biyar a ranar Laraba, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ta ƙulla aniyyar kawo ƙarshen wannan ƙalubale da tsofaffin ma’aikatan ke fuskanta kafin ƙarewar wa’adin mulkinsa na farko.

“Wannan wani yunƙuri ne na cika alƙawarin da muka yi na kawo ƙarshen wahalhalun da tsofaffin ma’aikata da iyalansu ke fuskanta tsawon shekaru,” in ji shi.

“Da Yardar Allah, kafin ƙarshen wannan wa’adi, za mu biya dukkan haƙƙoƙin gratuity har da na waɗanda suka rasu,” a cewar gwamnan.

Haka kuma, gwamnan ya sanar da shirin ƙaddamar da wata babbar manhajar tallafa wa matasa 4,000 a fadin jihar, inda kowannensu zai samu Naira 150,000 a matsayin jarin dogaro da kai.

Kungiyar ma’aikatan da suka yi ritaya ta ƙasa (NUP), ta bayyana farin cikinta bisa wannan mataki, inda shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Godwin Abumisi, ya bayyana Abba Yusuf a matsayin “gwamna nagari” tare da jaddada goyon baya domin ganin ya samu wa’adi na biyu a 2027.

“Gwamna Yusuf na cikin jerin gwamnonin da suka cancanci yabo. Saboda wannan karamci nasa, tsofaffin ma’aikata za su mara masa baya a 2027, saboda duk wani kyakkyawan wa’adi na buƙatar a maimaita shi,” in ji Abumisi.

Shi ma tsohon shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Kwamared Ayuba Wabba, ya jinjina wa gwamnatin jihar, inda ya ce biyan tsofaffin ma’aikatan haƙƙoƙinsu zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin jihar da kawo zaman lafiya a cikin al’umma.

Binciken Aminiya ya nuna cewa, gwamnatin jihar ta raba kudaden a matakai guda biyar daban-daban da suka hada da: Naira biliyan 6 a karon farko, sai Naira biliyan 5 a karo na biyu, da Naira biliyan 5 a karo na uku, da Naira biliyan 6 a karo na hudu, sai kuma wannan karon cikon na biyar da aka raba Naira biliyan biyar.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Naira biliyan 5

এছাড়াও পড়ুন:

UNGA: Shettima Ya Tallata Damar Zuba Jari Na Dala Biliyan 200 A Fannin Makamashi A Nijeriya

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki manyan matakai na gyara tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa farashin musayar kuɗi, da kuma sabunta tsarin haraji da kwastam.

 

Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun fara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, inda ya nuna cewa manyan kamfanonin tantance darajar kuɗi irin su Fitch da Moody’s sun ɗaga matsayin Najeriya saboda ingantattun manufofi da ƙaruwar ajiyar kuɗi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Syria ya yi jawabi a taron MDD karon farko cikin kusan shekaru 60
  • Ma’aikatan Gwamnati 5,000 Sun Fara Rubuta Jarabawar Tabbacin Gurbin Aiki A Kaduna
  • Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa
  • An Kama Tsohon Ɗan Wasan Super Eagles, Victor Ezeji, Kan Zargin Aikata Zambar ₦39.8m
  • Mun ci ribar Naira biliyan 601 a watanni shidan farkon 2025 – Bankin GT
  • UNGA: Shettima Ya Tallata Damar Zuba Jari Na Dala Biliyan 200 A Fannin Makamashi A Nijeriya
  • Babban Bankin Nijeriya Ya Rage Kuɗin Ruwan Da Bankuna Ke Caja
  • Katsina Za Ta Ɗauki Nauyin Karatun Mahaddata Alƙur’ani – Gwamna Radda
  • Talata ce ɗaya ga watan Rabi’ul Thani — Sarkin Musulmi