Ina jinjina wa ‘yan Najeriya bisa juriyar ƙuncin rayuwa da suke fuskanta — Atiku
Published: 30th, September 2025 GMT
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinjina wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira “juriya, haƙuri da ƙarfin halin da suke nunawa duk da matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro” da ƙasar ke fuskanta.
A cikin saƙonsa na taya ’yan Nijeriya murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai da ƙasar ta yi shekaru 65 da suka gabata, madugun adawar ya yi zargin cewa, gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da halin ƙaƙanikayi da ’yan ƙasar suka tsinci kansu a halin yanzu.
Wazirin Adamawan ya bayyana damuwa kan yadda ’yan Najeriya ke rayuwa cikin ƙangin talauci, da yunwa, da rashin tsaro, da kuma rashin aikin yi, yana mai cewa abubuwa sun yi tsanani ne duk saboda rashin tausayi na gwamnatin da ke mulki a ƙasar.
“Abin takaici ne a ce ƙasa mai yalwar albarkatu da mutane masu basira ta koma wani wuri da ’yan ƙasar ke rayuwa kamar ‘yan gudun hijira da bara a ƙasarsu.
“Duk wata gwamnati mai sanin ya kamata tana ɗaukar walwala da tsaron jama’arta da muhimmanci. Amma abin da muke gani a yau shi ne gwamnati ta yi watsi da jama’arta,” in ji Atiku.
“Yunwa na kashe mutane a yayin da ’yan bindiga ke ci gaba kashe al’umma, amma Shugaba Bola Tinubu da muƙarrabansa sun zama ’yan kallo tamkar babu abin da yake faruwa.”
A yayin da yake roƙo tare da ƙara jan hankalin al’ummar Nijeriya a kan kada su yi ƙasa a gwiwa, Atiku ya bayyana cewa zaben 2027 wata muhimmiyar dama ce ta tsamo kawunansu daga ƙangin mulkin kama karya ta hanyar amfani da ƙarfin ƙuri’a.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa duk da cewa Nijeriya ta yi shekaru 65 da samun ‘yancin kai, amma har yanzu ƙasar tana tafiyar hawainiya, lamarin da ya danganta shi da rashin shugabanci nagari wanda almundahana da cin hanci suka yi wa kakagida.
Kazalika, Atiku ya ƙarfafi gwiwar al’ummar da cewa muddin akwai shugabanci na gari, Najeriya na da damar samun sauyi a duk wani fanni da ta gaza domin zama wata babbar ƙasa da za a yi alfahari da ita a duniya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Atiku Abubakar
এছাড়াও পড়ুন:
Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%
An samu wannan raguwar ne sakamakon sauye-sauyen da aka samu a shekarar da muke ciki.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA