Aminiya:
2025-09-19@16:19:37 GMT

Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi

Published: 19th, September 2025 GMT

Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona al’aurar ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita.

Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta.

Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe

Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida.

Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda.

An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) domin kula da ita.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce an kama matar da wasu, ciki har da wata mai maganin gargajiya mai suna Fatima Abdullahi, wadda ta karɓi kuɗin matar sannan ta tabbatar mata cewa yarinyar mayya ce.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne ranar 11 ga watan Satumba, 2025.

Tuni Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike, tare da tabbatar da adalci.

’Yan sanda sun kuma ja hankalin iyaye da su daina kai yara wajen bokaye, domin hakan na iya jawo ɓarna maimakon samun waraka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Mayya zargi

এছাড়াও পড়ুন:

An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta ce jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da DSS sun kashe ’yan ta’addan ƙungiyar IPOB da yawa.

Kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ya ce tawagar ta lalata sansanonin IPOB a yankin Ezioha da ke Ƙaramar Hukumar Mbaitoli, da kuma a Umuele, Ubuakpu, da Amakor a Ƙaramar Hukumar Njaba.

’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?

Ya ce da yawa daga cikin mambobin ƙungiyar sun mutu yayin samamen, wasu kuma an kama su, yayin da wasu suka tsere da raunuka.

Okoye, ya ƙara da cewa an gano bindigogi da harsasai da dama a sansanonin, haka kuma ƙwararru sun lalata abubuwan fashewa da aka samu wuraren.

Rundunar ta jadadda ƙudirinta na wanzar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa tare da roƙon jama’a su yi aiki tare da jami’an tsaro.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wata mata ta ƙona farjin ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi
  • Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi
  • Mutum 1,666 ne suka kashe kansu a Legas cikin shekaru biyar – ’Yan sanda
  • Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza
  • ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu
  • An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda
  • ‘Yansan Jigawa Sun Tabbatarwa Mafarauta Da ‘Yan Bulala Samun Horo
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono