Matatar Ɗangote Ta Zargi Ƙungiyar PENGASSAN Da Yi Wa Al’ummar Nijeriya Zagon Ƙasa
Published: 1st, October 2025 GMT
Ɓangarorin biyu sun tashi baran-baran a wata tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan ƙwadago na Nijeriya, Mohammed Dingyadi a ranar Litinin.
Wannan yajin aiki na PENGASSAN ya shafi rufe ɓangarori da dama na harkar mai a Nijeriya, ciki kuwa har da babban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, tare da dakatar da ba matatar Ɗangote ɗanyen mai.
Kungiyar ta PENGASSAN ta ja daga, inda ta bayyana cewa, “Muna kan bakar mu har yanzu, saboda mutanen mu da aka kora daga aiki, muna so dole a mayar da su.”
Wannan na zuwa ne a yayin da wata kotun Abuja ta bayar da umarnin hana yajin aikin ƙungiyar ta PENGASSAN da ɗaukar matakin hana kai wa matatar Ɗangote ɗanyen mai da iskar gas.
Matatar Ɗangote ce ta shigar da ƙarar a gaban kotun ma’aikata a Abuja, kuma Alƙalin kotun ya ce Matatar Ɗangote kamfani ne mai zaman kansa da ke da lasisin samarwa da raba man fetur domin buƙatun ‘yan Nijeriya.
Sai ga shi kuma duk da umarnin kotun, ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Nijeriya ta yi barazanar shiga yajin aikin domin nuna goyon baya ga PENGASSAN.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Ta Kai Wa Sojojin MDD Hari A Kasar Lebanon
Tankar yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta bude wuta akan dakarun zaman lafiya na MDD dake kudancin Lebanon
Dakarun zaman lafiyar na MDD dake kudancin Lebanon (UNIFiL) sun sanar da cewa tankar yakin “Isra’ila” ta buder wuta akansu, da hakan ya tilasta musu guduwa zuwa inda za su buya.
Rundunar ta “UNIFIL” ta kuma bayyana abinda ya faru da cewa keta kudurin MDD ne mail amba 1701, tare da yin kira ga “Isra’ila’ da ta dakatar da abinda take yi.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da dakarun zaman lafiyar na MDD suke keta kudurin MDD ta hanyar kai hare-hare da kuma yin kutse a cikin yankunan dake kan iyaka.
A ranar 27 ga watan Oktoba ma dai rundunar ta MDD ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin sama maras matuki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila da ya rika shawagi akan sojojinta masu sintiri da zummar kai musu hari. Haka nan kuma a waccan ranar wani jirgin saman maras matuki na “Isra’ila” ya jefa bom a kusa da dakarun a garin Kafar-kalla.
A baya a ranar 12 ga watan Oktoba wani jirgin na “Isra’ila” da ya jefa bom, ya jikkata daya daga cikin dakarun zaman lafiyar na MDD.
An kafa rundunar UNFEL ne dai a 1978 bayan da sojojin Haramtacicyar Kasar Isra’ila su ka kutsa cikin kudancin Lebanon, an kuma karfafa ayyukan rundunar a 2006 da fitar da kuduri 1701. Da akwai sojoji 10,000 akarkashin wannan rundunar domin sa ido akan dakatar da yaki daga Isra’ila da kuma karfafa sojojin Lebanon a kudancin tafkin “Litani”.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Makiya Sun Kulla Makirci kan Kasar Labanon Irin Wanda Suka Kulla Kan Siriya November 16, 2025 Kasar Afghanistan Na Kokarin Karkata Akalar Kasuwancinta Zuwa Iran November 16, 2025 Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila. November 16, 2025 Zarfi: HKI Ce Kawai Take Ayyana Nukiliya Ba Bisa Kaida Ba A Yammacin Asiya. November 16, 2025 Shugaban kasar venuzuwela Yayi Tir Da Atisayan Soji Da Trinidad and Tobago Ke yi. November 16, 2025 IRGC ta kama wani jirgin ruwan dakon mai a gabar tekun kudancin Makran November 16, 2025 Iran : sojojin Amurka a yankin Caribbean barazana ne ga zaman lafiya November 16, 2025 Lebanon za ta kai karar Isra’ila a MDD kan gina Katanga a iyakarta November 16, 2025 AU ta sake watsi da ikirarin Trump cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya November 16, 2025 Falasdinu ta yi wasan sada zumunci a Spain November 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci