Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina
Published: 22nd, September 2025 GMT
Ƙaramar Hukumar Sabuwa da ta Ɗandume a Jihar Katsina sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga, a wani yunƙuri na kawo ƙarshen hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen da suka daɗe suna addabar yankin.
An gudanar da taron sulhun ne a ranar Asabar a ƙauyen Kabalawa Dungun Mua’zu, da ke iyaka da ƙananan hukumomin biyu, amma yana ƙarƙashin Sabuwa.
Da wannan ci-gaban, adadin ƙananan hukumomi da suka ƙulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga a jihar ya kai tara.
Sauran sun haɗa da Batsari da Kankara, Kurfi da Musawa da Ɗanmusa da Jibia da kuma Faskari.
Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyu NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen MalabuShugaban Ƙaramar Hukumar Sabuwa, Sagir Tanimi, da takwaroransa na Ɗandume, Bashir Gyazama, sun halarci taron, inda aka ce su ne suka taimaka wajen cimma yarjejeniyar.
Taron wanda ya ɗauki sa’o’i da dama ya haifar da wasu muhimman matsaya da ɓangarorin biyu suka cimma.
An amince da dakatar da kai hari, inda ’yan bindiga suka yi alƙawarin daina kai hare-hare a ƙauyuka.
Haka kuma an ba su damar shiga garuruwa da ƙauyuka domin harkokin kasuwanci ba tare da tsoron cutarwa daga jama’a ba.
Bugu da ƙari, ’yan bindigar sun yi alƙawarin sako mutanen da suka yi garkuwa da su, sai dai sun roƙi gwamnati ta yi ƙoƙarin ganin an saki ’ya’yansu da ke tsare.
Ɓangarorin biyu sun kuma sha alwashin yin aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
A yayin taron, ’yan bindiga da dama sun halarta ɗauke da manyan makamai, tare da shugabanninsu da suka haɗa da Idi Muwage da Alhaji Kabiru da Kachalla Rusku da Kachalla Murtala da Kachalla Mai Saje da Kachalla Dawa da Ardo Abdulsalam Fatika da kuma Alhaji Labi.
Shugaban kwamitin zaman lafiya, Dakta Salisu Ladan, ya bayyana cewa manufar yarjejeniyar ita ce dawo da zaman lafiya mai ɗorewa da kawo ƙarshen kashe-kashe da garkuwa da mutane da sauran munanan ayyuka.
Ya ƙara da cewa, “Shugabannin yankin sun tabbatar wa ’yan bindigar da tsaron rayukansu tare da maraba da su don su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwanci a kasuwannin yankin.”
Haka kuma an cimma matsaya cewa za a buɗe kasuwar shanu ta Ɗandume da aka rufe saboda matsalar tsaro, domin bai wa ’yan bindigar damar kawo dabbobinsu da yin ciniki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Ɗandume Sabuwa Zaman lafiya zaman lafiya yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Mahara sun kashe ɗan sanda, sun ɗauke bindigarsa a Taraba
An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba.
Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan bindigar suka yi wa shingen binciken ƙwanton ɓauna.
An ce maharan sun harbi ɗan sandan ne a kansa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take, lamarin da ya sa sauran abokan aikinsa da ke wurin suka tsere.
Bayan sun yi kisan, ’yan bindigar sun ɗauke bindigar marigayin sannan suka tsere daga wurin.
Kakakin rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai ɗaga wayar kiran da aka yi masa ba kuma bai amsa saƙon da aka tura masa dangane da lamarin ba.