Guterres ya jaddada wajabcin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza
Published: 10th, October 2025 GMT
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan damar.
Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta ka’idojin yarjejeniyar, da kuma rungumar damar da tke cikinta.
Duk da cewa dai a cikin kalaman nasa yafi nuna damuwa a kan fursunonin Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, duk da irin mummunan kisan kiyashi da Isra’ila take yi a Gaza, amma mya ce Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tsaf domin ba da cikakken goyon bayanta ga aiwatar da yarjejeniyar.
A halin da ake ciki kuma, ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a wanan Alhamis ta ba da rahoton cewa, ‘yan sa’o’i bayan tattaunawar tsagaita bude wuta tsakanin kungiyar Hamas da “Isra’ila”, Isra’ula ta kaddamar da wasu hare-haren a Gaza inda ta kashe mutane goma sha daya.
Yayin da mazauna yankin ke jiran aiwatar da yarjejeniyar tare da dakatar da kai hare-haren bama-bamai, ofishin ya bukaci ‘yan kasar da su guji yin zirga-zirga a kan titunan al-Rashid da Salah al-Din ko kuma a yankunansu har sai an fito fili a fili.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana a dandalin telegram cewa, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, asibitoci a zirin Gaza na ci gaba da karbar wadanda suka yi shahada, inda aka kashe mutane goma sha daya, daya daga cikinsu ya mutu a karkashin baraguzai da wasu arba’in da tara suka jikkata. Ma’aikatar ta kara da cewa an kuma kashe mutane biyu a cibiyoyin raba kayan agaji.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar: An Yi Kiran Gudanar Da Yi Wa Shugaban Kasa Zanga-zanga October 9, 2025 Jagora: A Yi Amfani Da Hanyoyin Sadarwa Na Zamani Domin Koyar Da Muhimmancin Salla October 9, 2025 An Fara Aiki Da Zango Farko Na Tsagaita Wutar Yaki A Gaza October 9, 2025 Shugaban Kasar DRC Ya Kira Yi Takwaransa Na Rwanda Da Ya Daina Taimakon M23 October 9, 2025 Jagora: Dole Ne Ga Hukumomin Da’awa Da Malamai Su Kula Da Batun Tsayar Da Sallah A Tsakanin Al’umma October 9, 2025 Babban Kwamandan IRGC Ya Jaddada Batun Wurga Makiya Cikin Mummunar Nadama October 9, 2025 Hamas: An Cimma Yarjejeniyar Karshen Kan Dakatar Da Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Gaza October 9, 2025 Kungiyar Jihadul-Islami Ta JInjinawa Al’ummar Falasdinu Kan Juriyarsu A Lokacin Yaki October 9, 2025 Shugaban Kasar Ecuador Ya Tsallake Rijiya Da Baya Daga Kisan Gilla October 9, 2025 Venuzuwela Ta Kaddamar Da Atisayan Soji Don Mayar Da Martani Ga Barazanar Amuka October 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza a Masar ranar Litinin
Masar za ta shirya wani taron kasa da kasa kan zaman lafiya a birnin Sharm el-Sheikh da ke bakin Tekun Maliya a ranar Litinin, wanda Shugaba Abdel Fattah el-Sisi da takwaransa na Amurka, Donald Trump, za su jagoranta.
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta bayyana cewa taron zai tattaro shugabanni daga kasashe fiye da 20.
Manufar taron ita ce “kawo karshen yakin Gaza, da karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya, da kuma fara wani sabon mataki na tsaro da kwanciyar hankali a yankin,” in ji sanarwar.
A ranar Laraba Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Hamas sun amince da mataki na farko na wani shiri mai matakai 20 da ya gabatar a ranar 29 ga Satumba don cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da sakin dukkan fursunonin Isra’ila da ke hannun Hamas a musayar fursunoni Falasdinawa kusan 2,000, da kuma janye sojojin Isra’ila daga dukkan yankin Gaza.
Mataki na biyu na shirin ya tanadi kafa sabon tsarin mulki a Gaza, samar da wata rundunar tsaro da za ta kunshi Falasdinawa da sojoji daga kasashen Larabawa da Musulmi, da kuma kwace makamai daga hannun Hamas.
Tun daga watan Oktoba na 2023, hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa fiye da 67,600 a Gaza, yawancinsu mata da yara, tare da mayar da yankin kufai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100% October 12, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter A Kasar Habasha October 12, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci