Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro
Published: 21st, September 2025 GMT
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na ƙara bunƙasa tsaro da bayar da kyautar kayan aiki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Gwamna Inuwa ya ce: “Tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma. Ba za mu samu ci gaba, ba tare da zaman lafiya ba.
“Gwamnatina za ta ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da ƙungiyoyin sa-kai domin kawo ƙarshen barazanar ta’addanci.”
A nasa jawabin, Rabiu Baushe, ya gode wa gwamnan bisa wannan tallafi, inda ya bayyana cewa motocin da baburan za su ƙara musu ƙarfi wajen yin sintiri da shawo kan hare-hare a yankunan karkara.
Ya kuma yi alƙawarin cewa ƙungiyar PROHAN za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a dukkanin sassan Jihar Gombe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babura Gwamna Inuwa Kyauta Motoci mafarauta Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Ballon d’Or: ’Yan wasa 5 da ke iya lashe kyautar 2025
Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na bana.
A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya.
Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa.
Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin.
An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin tsaro a Kwara Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a KatsinaGa jerin manyan ’yan wasa biyar da aka fi ganin suna da damar lashe ta bana:
Ousmane Dembélé – (PSG, Faransa)Ousmane Dembélé ne ke kan gaba a jerin masu fafatawa.
Dembele ya ta rawa gani wajen kai PSG ga nasarar lashe kofuna uku – gasar Ligue 1, Coupe de France da kuma kofin Zakarun Turai na farko a tarihin kulob ɗin.
Ya zura kwallaye 21 tare da taimaka wajen cin wasu shida, musamman a muhimman wasanni.
Wannan ne yasa ake kallonsa a matsayin babban ɗan fafatawa.
2. Lamine Yamal – (Barcelona, Sifaniya)Matashin ɗan shekara 17 zuwa 18 ya yi abin mamaki a wannan kakar.
Yamal ya yi fice a gasar La Liga da kuma Copa del Rey inda ya zura kwallaye 18 tare da taimakawa wajen cin kwallaye da bayar da dama aka ci wasu 21.
Kwarewarsa da kwazo suka sa ake kallon shi tamkar fitacciyar tauraruwa ta gaba.
Sai dai kuma duk da haka, rashin nasara a Gasar Zakaraun Turai na iya rage masa ƙuri’u.
3. Raphinha – (Barcelona, Brazil)Shi ma Raphinha yana daga cikin manyan ’yan wasan da suka yi fice a bana.
Ya zura kwallaye 34 tare da bayar da damaa ka zura wasu 22 a muhimman wasanni.
Barcelona ta yi nasara a gida, kuma gudummawarsa ta zama abin yabo.
Amma duk da haka, ya na iya fuskantar kalubale wajen daga irin bambanci tsakaninsa da sauran taurarin Barcelona.
4. Vitinha – (PSG, Portugal)Vitinha na daga cikin ɗan tsaka-tsaki da aka yaba da rawar da ya taka a PSG.
Shi ke tsare tsakiya, yana rarraba kwallo da samar da daidaito tsakanin tsaro da hari.
Duk da cewa ba shi da yawan kwallaye ko taimako irin na ’yan wasan gaba, gudummawarsana da matuƙar muhimmanci.
Sai dai irin wannan rawar kan kananan wurare na iya zama mai ƙarancin tasiri ga masu kada ƙuri’a.
5. Mohamed Salah – (Liverpool, Masar)Salah ya ci gaba da zama ginshiƙi a Liverpool inda ya taimaka musu su lashe Gasar Firimiyar Ingila da kwallaye da dama da kuma taimakon cin wasu. A matsayinsa na ɗan wasa da ya dade yana taka rawar gani, yana da daraja a idanun masu jefa kuri’a.
Amma rashin kai Liverpool mataki mai nisa a Champions League na iya rage darajarsa a wannan karon.
Abubuwan da ke iya tabbatar da nasara?Masu shirya gasar sun ce abubuwan da ake la’akari da su wajen zabar Gwarzon Dan Wasan su ne: Hazikancinsa shi kadai, dabi’unsa da iya yanke hukunci da kuma gudummawa ga abokan wasansa dai saurnasu kamar haka:
A halin yanzu, ana kallon Ousmane Dembélé a matsayin babban wanda ke iya lashe wannan babbar kyauta, yayin da Lamine Yamal ke biye masa.
Raphinha, Vitinha da Mohamed Salah kuwa suna nan a sahun gaba suna jiran rarrabuwar ƙuri’u wanda hakan ke iya sa su kai bantensu.
Duk da haka, Ballon d’Or ya saba zuwa abubuwan ban mamaki; duk wani ɗan wasa mai tasiri — mai tsaron raga, mai tsaron gida, ko wani fitacce —na iya mamaye sahun gaba idan ya nuna bajinta a ƙarshen kakar.
Kazalika kokarin dan wasa na karshe-karshe musamman a Champions League ko wasannin kasashe na iya sauya kuri’un.