An yanke wa Soja hukuncin kisa ta hanyar rataya
Published: 18th, September 2025 GMT
Wata babbar kotun sojin Najeriya da ke zamanta a sansanin sojoji ta Maxwell Khobe da ke garin Jos a Jihar Filato ta yanke wa wani soja mai suna Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
An yanke wa Musa hukuncin kisa ne a ranar Alhamis bayan da aka same shi da laifuka biyu kan kisan gilla da aka yi wa wani direban babur mai ƙafa uku mai suna Abdulrahman Isa a garin Azare na Jihar Bauchi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, an fara shari’ar Musa ne a farkon watan Agustan 2025 bayan kama shi biyo bayan binciken haɗin gwiwa da jami’an sojoji sashin harkokin da hukumomin yankin suka gudanar.
Al’amarin ya ja hankalin jama’a sosai saboda tsananin mugun halin da aka aikata da kuma yunkurin tauye amanar jama’a da sojan ya yi.
Shugaban Kotun Sojojin Najeriya ta 3, Birgediya-Janar, Liafis Bello ya ce an samu sojan da laifin kisan kai da kuma mallakar harsasai ba bisa ƙa’ida ba.
Kotun ta tabbatar da cewa, shaidun da aka gabatar a lokacin shari’ar sun nuna cewa, Musa ya haɗa baki da wani mai suna Mista Oba, domin su kai Isa gidansa da zargin taimaka masa wajen kwashe kayansa.
Ya ƙara da cewa Musa ya bugi Isa a kai da wani abu na katako, inda ya sume, kafin ya shaƙe shi ya mutu.
A ƙoƙarinsu na ɓoye laifin, Musa da abokinsa sun cusa gawar wanda aka kashe a cikin buhu tare da jefa ta a tsakanin ƙauyukan Shira da Yala a Jihar Bauchi.
“An sayar da babur mai ƙafa uku na Isa daga baya, wanda ya ƙara fallasa yadda aka tsara yadda lamarin ya faru,” in ji masu gabatar da ƙara na soji yayin shari’ar.
Hakazalika sun bayyana cewa a binciken da ake yi, an samu Musa da harsashi na musamman har guda 34 na nau’in 7.62mm ba tare da wata izinin doka ba.
Da yake yanke hukuncin, Birgediya Janar Bello ya bayyana abin da Musa ya yi a matsayin “abin kunya, rashin tausayi da kuma cin zarafi da rahin a ɗa’a da kimar sojoji.”
“Ka nuna rashin tausayi daga mai kare ’yan ƙasa zuwa mai kisan gilla, matakin da kuka ɗauka abin kunya ne kuma abin kunya ga Sojojin Najeriya,” in ji kotun.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukuncin rataya
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansan Jigawa Sun Tabbatarwa Mafarauta Da ‘Yan Bulala Samun Horo
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido Wada ya jagoranta a Dutse babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, Rundunar za ta hada gwiwa da wadanda abin ya shafa domin fuskanatar kalubalen zirga-zirga don daukar matakin da ya dace.
A cewarsa, rundunar ta ci gaba da shirye-shiryen ‘yan sanda da al’umma ke tafiyar da su ta hanyar samar da hadin gwiwa mai karfi da masu ruwa da tsaki da suka himmatu wajen samar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
Dahiru Muhammad ya bayyana jin dadinsa da irin dimbin karfin da suke da shi, da tsari, da tsarin jagoranci.
A yayin ziyarar, maziyartan sun yi alkawarin ci gaba da jajircewarsu wajen kiyaye dazuzzuka da kuma tabbatar da tsaro a fadin jihar.
Sannan sun gabatar da muhimman bukatu ga kwamishinan ‘yan sanda, wadanda suka hada da samar da hanyoyin sadarwa da ayyukansu ga babbar hukuma, jami’an tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki ta hanyar CP a matsayin hanyar tuntubar juna.
Shirya horar da ƙwararrun mambobi don haɓaka ƙarfin aikinsu da tabbatar da suna aiki daidai da buƙatun doka.
Sauran buƙatun sun haɗa da samar da tallafin abin hawa, kamar babura, don sauƙaƙe ayyukan su.
Taron ya hada wakilai uku da suka hada da shugaba, Kwamanda, da Sakatare daga kowace karamar hukuma 27 dake fadin jihar.
Tawagar ta kuma samu rakiyar Salisu Garba Kubayo, babban mataimaki na musamman kan hukumar manoma da makiyaya ga Gwamna Umar Namadi.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, kungiyar ‘yan kabilar Igbo reshen jihar karkashin jagorancin Cif Christopher Agbo ta kai ziyarar ban girma ga kwamishinan ‘yan sanda.
Kungiyar ta bayyana kudirinta na tallafawa ‘yan sanda wajen wanzar da zaman lafiya, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, da kuma samar da yanayi mai kyau na kasuwanci da zamantakewa a fadin jihar.
KARSHE/USMAN MZ