Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu.

Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20.

Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rabon gidaje 72 ga malamai da ma’aikatan lafiya a ƙaramar hukumar Mafa.

Zulum ya ce Marbel ta shafe fiye da shekaru 24 tana aiki a cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke Mafa, kuma ba ta taɓa barin wurin ba ko da a lokacin rikicin Boko Haram.

“Ko da rikici ya yi tsanani, ba ta taɓa barin Mafa ba, duk da cewa ba ’yar asalin jihar ba ce. Ta kula da ’yan uwana da dama, har da mahaifiyata. Wannan ya sa ta cancanci a girmama ta,” in ji Zulum.

Gwamnan ya bayar da umarnin a bai wa ma’akaciyar gidan da sunanta, tare da sanar da cewa ɗanta, Anthony Duaka, wanda ya kammala karatun banki, an bas hi aiki kai tsaye a Jami’ar Kashim Ibrahim da ke Maiduguri.

A cikin martaninta, Marbel ta bayyana farin cikinta da godiya ga gwamnan bisa karramawar da ya yi mata.

“Yau ce rana mafi farin ciki a rayuwata. Gwamna ya karrama ni fiye da tsammanina. Ya ɗauki nauyin karatuna na digiri a fannin lafiya, ya ba ɗana aiki, yanzu kuma gida. Na gode ƙwarai,” in ji ta.

Wannan mataki ya biyo bayan irin na shekarar 2022, lokacin da Gwamna Zulum ya bai wa wata malamar makaranta ’yar ƙabilar Igbo, Misi Obiageli Mazi, kyautar gida saboda jajircewarta da bin lokaci wajen zuwa aiki a jihar.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe

A yayin da ake yawan samun ɓarnar dorinar ruwa a garuruwan Daɗin Kowa da Kupto da Malleri da Wade a yankunan Ƙananan hukumomin Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe ta kai ga samun asarar amfanin gona da rayuka.

Hakan ne ya sa Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Yamaltu/ Deba a Jihar Gombe Inuwa Garba ya gabatar da ƙudiri a gaban zauren Majalisar Wakilai ta tarayya domin neman ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarnar dorinar ruwa.

’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya

Inda ya ce dorinar na yi wa manoma ɓarna sosai da ke janyo asarar rayuka, dukiyoyi da lalacewar amfanin gona a yankunan da abin ya shafa.

Inuwa Garba ya bayyana hakan ne, a shafinsa na Facebook cewa, dorinar ruwan ta zama babbar matsala ga manoma da al’ummomin waɗannan yankuna inda ake samun girgizar tattalin arziki sakamakon lalacewar gonaki, lalata hanyoyi da kuma rasa muhallin zama.

Ya ce, wannan ƙudiri na da nufin kawo mafita ta dindindin domin kare rayukan mutane, kiyaye dukiyoyin su da kuma tabbatar da ci gaban noman rani da damina, wanda shi ne tushen rayuwar yawancin mazauna yankin.

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Gombe, tare da hukumomin kula da ruwa da su kai ɗauki cikin hanzari ta hanyar bayar da tallafi, gyaran madatsun ruwa da kuma samar da hanyoyin rage haɗarin dorinar a nan gaba.

A ƙarshe, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwa na waɗanda suka rasa rayukansu a ibtila’in dorinar ruwa yana roƙon Allah Ya jikan mamatan da rahama, tare da ba iyalansu haƙuri, juriya na rashin da suka yi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Soja ya kashe matarsa, ya hallaka kansa a Jihar Neja
  • Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
  • Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa
  • Cuba Ta Bayyana Bada Kyautar Noble Ga Dan Kasar Veunzuelas machado A Matsayin Abin Kunya.
  • Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina
  • Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro
  • Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
  • Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida
  • Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe