Najeriya Ta Shirya Karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila A 2030– Tinubu
Published: 19th, September 2025 GMT
Najeriya ta tabbatar da shirinta na karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila na 2030, inda za ta zama ƙasar Afirka ta farko da za ta kafa wannan tarihi tun 1930.
Shugaba Bola Tinubu, ta bakin Shugaban Ma’aikatansa Femi Gbajabiamila, ya ce gwamnati ta ba da cikakken goyon baya, ta kuma shirya samar da dukkan abubuwan more rayuwa, tsaro da masauki kafin lokaci.
A jawabansu daban daban, Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa Shehu Dikko da Shugaban Kungiyar Wasannin Renon Ingila Habu Gumel, sun bayyana cewa Najeriya ce damar Afirka mafi cancanta, yayin da kwamitin neman karɓar gasar ya gabatar da shirin gudanar da wasanni 15, ciki har da kwallon ƙafa.
Najeriya da Indiya ne ke neman karɓar gasar, inda za a bayyana kasar da za a yi wasannin a watan Nuwamba 2025.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya
Shugaba Trump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya, yana mai zargin gwamnatin kasar da kyalewa ana kashe kiristoci.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkabe abin da ya kira ƴanta’adda masu kishin Islama da ke aikata ta’asa.
Ya kuma yi barazanar dakatar da duk wani taimakon da Amurka ke bawa Najeriya.
Tuni Najeriya ta yi watsi da ikirarin cewa ana kashe kiristoci ba gaira ba dalili a yankin arewacin inda galibi musulmi suka fi yawa.
A bayanin da Trump ya wallafa a kafar sadar zumuntarsa ta Truth a ranar Asabar ya ce ya ba wa ma’aikatar tsaron Amurka damar ta fara shirin daukar mataki kan Najeriya – “Idan har gwamnatin Najeriya ta bari ana ci gaba da kashe Kirista,” in ji shi.
Shugaban wanda ke da’awar samun lambar yabo ta zaman lafiya a duniya ya kuma yi mummunan kalamai ga Najeriya inda ya ce “Amurka za ta shiga cikin kasar da a yanzu ta wulakanta.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci